BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da kallo kawai aka bita inda lieutenant ke tunanin larurar ciki ce kawai, Hajia kuma take ganin kishi ne ba komai ba, haka suka gama cin abincin sai dai babu wani nishad’i tunda Ammar ya tafi bare ayi raha, haka kowa ya tashi ya kama gabanshi sai kuma randa ta juyo aka sake irin wannan zaman, dan abune mai wuya ka gansu zaune hakanen wuri d’aya dukansu.

Ko da yaje ya samu Jano a can, insp. ya basu hak’uri yace su ba juna hak’uri kuma a kiyaye gaba, rumi-rumi suka fito daga ciki kowa ya shiga motarshi, saida Ammar ya kira wani matashin saurayi dan ya zo ya bi bayanshi da motarshi saiya kaiwa lieutenant tashi a can ofishin shi, Jano na daidaita motarshi zai fita ya fito daga tashi motar ya same shi, saida yasa ya sauke gilashin suka kalli juna yace “Jano karka manta, a dalilinka na tab’a shiga prison, dan haka kaima ka shirya shigarshi ko da na kwana d’aya ne, ka dai san nasan shige da ficenka da kuma sana’ar da tafi shigo maka da kud’i.”

Saida ya nuna mishi yatsa yana kalkad’a shi yace “Ka kula.”

Wucewa yayi ya barshi nan, tare da yaron da ya zo suka tafi shi a motar lieutenant har suka isa. Yayi mamaki sosai da aka ce wai Ammar na son ganinshi, Ammar dai daya sani? A gaskiya ba dan Ammar d’aya ya sani ba a duniya idan ka cire *sahabi Ammar bin Yaseer wanda suka fara shahada a musulunci* da sai yace shine amma ba nashi ba, dan nashi in ya zo kai tsaye yake shiga ko da yana tare da bak’i ne, izinin shigowa yasa aka masa, saida ya ganshi ya dai tabbatar shi d’in ne, cikin nutsuwa ya zauna kan kujerar dake fuskantarshi ya bashi makullan yace “Abba gashi, nagode.”

Shima cikin yanayin kulawa yace “Har ka dawo ne? To ya ake ciki?”

“Ba komai Abba.” Ya fad’a babu walwala tare dashi, saida ya gyara zama ya kalli lieutenant yace “Abba, akwai wata masaniya da nake son baku kan wani mutum, bansan ko kana so ba?”

Kallonshi yayi da murmushi, ko ma wanene tashi ta k’are cewar lieutenant, amma sai yace “Zamu so mana idan ya shafi aikinmu.”

Sai kuma kawai ya mik’e zai fita yace “Shikenan, zan nemo.” K’ofa ya tunkara lieutenant ya bishi da kallo, me yake nufi kuma? Ganin zai fita yasa yace “Ammar.”

Juyowa yayi da fad’in “Na’am.” Saida ya kalli agogo yace “Da k’arfe hud’u na yamma ka same ni gidan gona ta dake kusa da *Olga oil*.”

Da d’an murmusawa yace “To Abba.”

Fita yayi da wayarshi a hannu yana neman wata lamba, saida ya shiga mota ya zauna sannan ya aika kiran, bayan an d’auka sun gaisa ya fara mishi wasu tambayoyi, sun d’an jima suna magana kafin daga bisani yace “Ka tabbatar motar kayanshi ce ake d’orawa?”

Daga d’aya b’angaren aka ce “Na tabbata yallab’ai.”

“Ya yanayin lodin yake?” Ya tambaya, daga can tace mishi “Eh to, kwalayan (karton) indomie ne da lipton, sai atampopi daga sama da shadda, sai kuma buhunan shinkafa a sama.”

Wani murmushin da shi kad’ai yasan ma’anarshi yayi yace”Nagode, zan sake kiranka.”

Yana kashewa ya tayar da motar ya d’auki hanyar, wannan binciken k’wak’wafin shi ya wuni yana yi, daga nan zuwa can daga can zuwa nan, waya kuma har ya gaji da amsawa duk saboda son kawo k’arshenshi, sai misalin *12:30* ya d’auki hanyar komawa gida cike da gajiya, kai tsaye b’angarenshi ya nufa da makulli a hannu da waya, da wata zazzak’ar sallama ya shiga sai dai babu kowa bare bare a amsa mishi, falon yasha gyara sai k’amshin turaren wuta yake na jonawaa lantarki, ga kwanukan abinci da aka jera wurin ya k’ayatu, murmushi kawai yayi ya aje makullin da waya akan teburin tsakiyar falon ya shiga d’akinta. Tana tsaye gaban madubi tana d’aure k’ananan kitsonta, yana ganinta ya fad’ad’a murmushinshi da fad’in “Wow, duniyata.”

Da sauri ta juyo ta kalleshi, murmushi tayi ita ma tare da takowa cike da kunyar kayan data saka, tana zuwa ta narke a jikinshi tana sauke numfashi a hankali, ni’imtaccen k’amshinshi turarenshi ne ke ratsa hancinta, shafata yake tare da mamatsa bayanta yana cika hannu da tsokar bayanta ido rufe, har tsakiyar kanshi yake jin duk wasu albarkatun jikinta na sake samun matsuguni a na shi jikin, turaren na kwantar mishi da hankali sosai, a hankali ta d’ago kai ta kalleshi, kallon tattausan fuskarsa wacce ke canza launi duk sanda ta so yasa ta lumshe ido, saida ta d’aga k’afafunta ta kai bakinta daidai na shi ta sumbata, babu wata k’ara ko sauti, saidai tasirin sumbar yasa ya lumshe ido, lokaci d’aya suka bud’e ido a tare suka kalli juna, murmushi ta sakar masa tace “Ka gaji ko yah Ammar?”

Girgiza kai yayi cikin sanyin murya yace “A’a ba yah Ammar ba, ki saka min wani sunan na daban.”

Saida ta jujjuya matsakaitan idonta tace “Umm! Kamar wane kenan kake so?”

Murmushi ya mata yace “A ganinki wane sunan na cancanta? Ni dai kinga na baki sunan duniyata, saboda kin zama dunuyata, ni kuma fa me na zama naki?”

Saida ta k’ara rik’e k’ugunshi da kyau da hannayenta tana kallon k’asumbarshi sannan tace “Nima ka zama duniyata, sabuwar rayuwata kuma farin cikina.”

Raba jikinshi yayi da na ta ya d’an turata gefe ya k’ura mata ido, kallonta yake kamar zai had’iyeta, dogon wandon jeans bleue dark da riga bleue light mai hannaye iya damtse, dogayen takalmi bak’ak’e sai yar gajerar kwalliya da tayi, juyawa yayi yana zagayata dan ganinta da kyau, masha Allah duk da tana da gaba sosai, amma kuma sama suke can mak’ale da k’irji, bayan nan kam tubarkallah yau data saka wando ya zauna mata daram akansu sai abun ya bayar da citta. Kiran sallah a masallacin dake jikin gidan nan ne yasa yace “Bari na dawo daga masallaci, ina nan tare dake sai la’asar zan fita.”

Ban d’akinta ya fad’a yayi alwala ya fito, gabanta ya tsaya ya danna mata wata mahaukaciyar sumba a goshi sannan yace”Saina dawo.”

Tare suka fito daga d’akin shi ya fita ita kuma ta zauna zaman jiranshi.

Tunda Ummy ta shiga d’aki bata sake fitowa ba, har asibiti ake ta kiranta wasu k’ananan ma’aikatan na tambayarta kan wani abu idan ya shige musu duhu, har akayi sallah azahar aka gama bata fito ba, damuwa da halin da take ciki yasa Zeituna shiga d’akinta dan ta gani, da sallama ta shiga Ummy kuma naji bata amsa ba, dan haka bata shiga ba saita tsaya daga k’ofar tace “Ummy Ammar kina lafiya? Naga har anyi sallah kuma baki fito ba.”

Tasowa tayi daga inda take ta zo ta bud’e k’ofa, kallon kallo sukayi sai yanayin damuwa tare da ita, cike da kulawa tace “Ummyn Ammar lafiya ko? Ko ba kya jin dad’i ne?”

Saida ta rufe d’akin ta fito ta fuskanceta sai kawai ta d’auketa da wani wawan mari, dafe kumci tayi lokaci d’aya ta saki k’ara, Zeinabu da fitowarta kenan daga sallah taji saukar marin, da sauri ta matso tana kallonsu da mamaki, Nana ma dake kan ajiye abinci a tebur ita ma k’ura musu ido tayi, Inna ma saukar marin taji ta tsaya, ba tare data bari ta d’ago ba Ummy ta nunata da yatsa tace “Wannan shine abinda ke faruwa, bana son munarfici da iyayin tsiya.”

Tsaki tayi ta bita da harara ta fita harabar gidan, Zeituna data kasa had’a ido da ita saida taga fitarta ta tafi a guje d’akinta, Inna ce ta bi bayanta har d’akinta, tana zuwa ta sameta ta zauna kusanta tace “Amarya kiyi hak’uri, hakan zaman ya gada dama indai ance zo mu zauna to zo mu sab’a ne.”

Saida ta share hawaye sosai ta kalli Inna tace “Ba komai Inna, ni ai ba bak’uwar zafi bace, kawai ki kwantar da hankalinki.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected