BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Amma ba damuwa zaiyi maganin saurayin kafin ita, shi daya zauna yana kallo yana jin dad’i tana zagar masa yaro amma bai hanata ba, dan baisan darajar ‘ya’ya ba saboda bai da su shi, da azama ya k’araso wajen ta bayansu ba tare da sun san da zuwanshi ba, saida ya tsaya da kyau ya toge sosai yasa k’afarsa ta dama a gaban k’afafun saurayin nan da ko sunanshi Hamna bata sani ba bare ta fad’a mana ya kwashi k’afafunsa.

Sai ji tayi kawai abu ya fad’i k’asa pamm, da sauri ta saki Shureim ta juya ta kalli ikon Rabb, bawan Allah bai san me ya faru ba, baisan wane shaid’anin bane a cikin shaid’anun, abinda ya sani kawai shine a cikin aljannun ma wannan gagararre ne, duk yanda akayi ko dai a gidansa ne suke tsaye ko kuma sun taka masa yara basu sani ba, amma wannan kwasa da aka masa ko jirgin sama yana shaida maka zai tashi ya d’aga ka daga kan k’afafunka bare kuma bil’adama.

Yana shirin bud’e idonshi daga k’asar da fuskarshi ta daduma yaji an tokara masa gwiwar k’afa a baya an hana shi tashi, bai yarda yayi gamo ba saida yaji an figi hannunshi ta baya anyi ciri dashi, yana jin sautin k’arar gotawar k’ashin shi sanda aka karya hannunshi, azaba ce tasa shi sakin k’arfinshi ya daka uwar ihu.

Yana jin k’ararshi ya sake cije leb’e yana fad’in “Au! Zaka iya ihu ashe.”

Tsakiyar kanshi ya dafe ya rik’e hab’arshi da d’aya hannu da niyyar kawai ya juyar masa da wuya, an jima uban kowa bai mutu ba, Hamna data shiga firgici na abinda zai aikata bata san sanda ta rumgume shi ta baya ba ta rik’e hannayenshi gam ta fashe da kuka tana fad’in “Dan Allah Ammar sake shi baiyi komai ba, dan Allah karka kashe shi ka rufa mana asiri.”

K’arfin tartsatsin da yaji kamar k’arfin dake cikin wutar lantarki ne, ba wai tsayawa ba daga masifa, hatta numfashin shi ma ta kusa sawa ya bar jikinsa, har jikinshi ma ya shida ita ta musamman ce, sannan dokinshi ma ya tabbatar da yana kewar mace, dan a take sak’on yaje ya kuma haifar da sakamako mai kyau. Sakinshi yayi tare da mik’ewa tsaye yana kallon mutumin, shi fa ko fuskarshi ba bai gani ba, tsabar fitina ce kawai da neman wanda za’a mutu tare, sai lokacin ta sake shi tana k’ok’arin su kalli juna sai kawai ya taka da sauri yaja hannun Imam da Shureim wanda dukansu sukayi shiru da kukansu suna kallon babbar harka, cikin gida ya shige dasu.

Cikin jin kunya ta kalleshi ya tashi zaune yana karkad’e k’asa a fuskarshi yana furzar data bakinshi, a hankali cikin taushin murya tace “Dan Allah kayi hak’uri kaji, kayi hak’uri da abinda ya maka, yayana ne.”

Shi dai da har yanzu bai gama gane komai ba ga hannunshi dake zugin bala’i na karaya ko kallonta baiyi ba, ko da taga haka ta mik’e ta shige gida da gudu da niyyar yau saita kawo k’arshen wannan bura’ubar da yake mata a gidan nan. Shima yana ganin shigewarta ya fashe da kuka na gasken gaske yana birkid’awa yana rik’e hannunshi da yake jin kamar zai cire ya barshi, gashi ba zai iya tuk’a motar ba bare ya kai kanshi wajen magani, baida nutsuwar da zai iya kiran wani ya zo ya d’aukeshi, mai gadin gidan ne yaji kukan babban mutum a waje ya fito da gudu, da taimakonshi ko da ya duba hannun yace karaya ce, tsaf ya mishi magani yasa mishi magani yanata addua’r Allah ya sawak’e, saida aka gama yace mi shi “Amma ba kaine bak’on da ka zo wajen Hajia Hanne (Inji shi)?”

“A’a.” Ya fad’a yana tashi tsaye, shima tsaye ya mik’e yace “Amma garin yaya ka karya hannu haka? Gashi kuma banga alamar hatsari ba.”

Huyowa yayi ya kalleshi, hatsari? Hatsari ma yake cewa baiga alama ba, bayan abinda ya faru yafi karon babbar mota muni, juyawa yayi ya ci gaba da tafiya a hankali yana d’an sosa bayanshi inda ya daka mishi gwiwa, motar ya bud’a ya shiga ya tayar ya fara janta a hankali yana tuk’i da hannu d’aya, sai dai ya ci alhwashin ko ma uban waye wannan yayan nata wallahi saiya tara masa yaran nan na unguwarsu yan zaman kashe wando sun ciro masa jijiyar dake sadar da ji da ganinshi.

*Allah yaba mai rabo sa’a.*

*Ko da* ta shiga da masifa a falon ta same shi yana wa Shureim bala’i yana fad’in “Akan banzar waya zaka zauna ana zagin ubanka a gaban k’aton banza, me yasa baka buga wayar a k’asa ba ta b’are? Duk duniya idan ka cire ni ubanka da uwarka da kuma yan uwanka ban yarda ka d’auki raini a hannun kowa ba, kaji na fad’a maka.”

Girgiza kai Shureim ya shiga yi yana sako da hawaye, tana bayanshi a hassale tace “Wannan har d’ab’ia ce kake jin kana koya masa to?”

Juyowa yayi ya kalleta, kallon jin haushi da zan iya miki komai, ganin bai tanka mata ba yasa tace “…

*Alhamdulillah*
04/11/2020 à 14:38 – Ummulkhairi: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*BADAK’ALA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_

*SADAUKARWA GA*

‍‍‍ _*AHALI NA*_‍‍‍

✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ ️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_67_

Ammar me ye matsalarka da samari na? Akan wane dalili ne kullum ka ganni da saurayi saika wulak’anta ni a gabanshi ko kuma ka muzantashi? Me yasa? Ka fad’a min idan ba haka ba yau ni da kai a gidan nan wallahi sai dai duk mu babbake.”

Da fari da kallonta yake yana tunanin hannun da idan ya bigeta dashi zata fi jin zafi, amma data ce wai duk su babbake sai ta bashi dariya, dariya ya shiga yi hankali kwance wanda hakan ya sake hassalata cikin d’aga murya ta kalli Hajia dake zaune tana kallonsu kamar tv tace “Hajia ki mana tsakani da bawan Allahn nan ya daina shiga tsakani na da samari na, tunda dai ba zamansa nake ba kuma ba aurenshi ne akai na da zai addabe ni ba.”

A hankali Hajia ta d’an dafe kanta dan ciwon kai taji suna neman sanya mata, lallai da taso a had’a aurensu, amma yanzu tunaninta shine yanda wannan yara zasu zauna in aka aurar dasu, lallai gaskiyar Junaid ne gidan nan zai iya kamawa da wuta, ganin Hajia ma ta k’yalesu saita k’ara jin haushi tace “To Allah idan na sake tsayawa da saurayi ka min iskanci Ammar saina soke ka da wuk’a.”

Hajia ta kalla tace “A matsayinki na kakarshi Hajia ki fara nema masa magani, dan wallahi ya gama kwancewa.”

Sama da k’asa ta bishi da harara ta giftashi zata wuce d’akinta, cikin salon da ka rantse bashi yayi maganar ba yace “Nan gaba ma wuyansu zan fara takawa, kin k’waci kanki da rumgumar da kika min, amma kika sake gigin zagar min yaro sai jini ya fita a bakinki, dan abu d’aya dana lura dashi shine baki k’aunarshi, to ni ina son kayana ehee.”

Tab’e baki tayi tace “Akan me zan k’aunace? Wannan d’in?”

Ta fad’a tana nuna Shureim, gyara tsayuwarsa yayi yace “Me yasa baka son shi? Shi ba d’a bane?”

Kawai dan ta b’ata masa rai tace “Saboda bai min ba.”

Gabanta fad’uwa yake saboda kallon da yake mata, murya k’asa k’asa yace “Me yasa bai miki ba?”

Da sauri Hajia dan ta tsayar da maganar tace “Hamna wuce d’akinki bana son tashin hankali.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected