BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Juyowa yayi hakan yasa ta arta a guje tayi falon, girgiza kai yayi a ranshi yace “Ai zamu had’u ne, zan miki horon da har ki mutu ba zaki manta dani ba.”
Tana shiga falon ta tsaya das saboda Hajia data samu zaune kan kujerarta fuskarta a had’e sai kuma Ummy da Zeinabu gefenta da alama fad’a ta musu ke take musu, ko kuma dai tuhumarsu take, cikin tsananin fad’uwar gaba da sanyin jikin ta tako zuwa tsakiyar falon, murya k’asa k’asa tace “Assalama alaikum.”
Kallonta kawai sukayi amma babu wanda ya amsa, nufa hanyar da zata sada su da d’akin su tayi, a hankali Hajia tace “Zo nan.”
Kamar wacce k’waiya fashe ma a ciki haka ta taho ta durk’usa gabanta kanta k’asa, tsaye Hajia ta mik’e hakan kuma baisa Hamna yunk’urin kare kanta ba dan bata san Hajia da saurin hannu ba inba abu ya kai mak’ura ba, bata ankara ba taji saukar yatsu biyar, tana dafe kunci ta d’ago ta kalleta yayin da Hajia kuma tace “Ke har ni zaki mayar wata mahaukaciya a gidan nan, ina cikin gidan nan amma kike nema kiyi rayuwar da kika ga dama, me kike so ki zama Hamna? Yar iska? So kike ki zama kamar uwarki kenan? To baki isa ba wallahi, yanzu fad’a min a cikinsu wacece tasan da fitarki a gidan nan?”
Ta fad’a tana nuna su Ummy, Hamna kuma babu abinda ya mata zafi kamar cewa wai tana so ta zama yar iska kamar uwarta, kenan mahaifiyar tasu ce yar iska? Lallai ni na jawa mahaifiyarmu wannan wulak’ancin, tsawa Hajia ta mata tace “Dake nake magana kina jina.”
Kallonsu Ummy tayi ta girgiza kai tace “Basu san fita ta ba.”
Cikin masifa tace “To gidan ubanwa kika je? Me kika je yi da baki dawo ba sai yanzu? Hamna kina ‘ya mace ace ba kya cikin gidanku kina waje, to me kikeyi? Kuma ba a motonku kika fita ba, kenan wani ne ya zo ya d’auke ki kuma ya dawo dake.”
Kallonta Hamna tayi tace “Wallahi Hajia adaidaita na shiga, kuma wurin kan amarya ne muka tafi, nasan idan na tambaya ba za’a barni ba shiyasa, kuma ki tambayi yah Ammar kiji tare ma muka dawo yanzun.”
Kallonsu Ummy tayi tace “Ku b’ace min da gani ku Allah ya taimake ku.” Tashi sukayi inda ita kuma ta koma ta zauna tana kallonta tace “Tare da Ammar?”
Kai ta gyad’a alamar eh, amma me Hajia za tace sai cewa tayi “To na sani ko tare dashi kuke yawon iskancin na ku, dan ni ban yarda dake ba, shi kuma dama idonshi tsakar kai suke ba kunya ne dashi ba, yanzu idan na kira shi zai iya fad’a min abinda ya faru tsakanin ke da shi.”
Mamaki ne yasa Hamna kallon Hajia kawai ta kasa cewa komai, hakan yasa Hajia cewa “Je kirawo min shi, dan wallahi ko iskanci kuke yau saina kawo k’arshen shi a gidan nan, watak’ila dama wannan dalilin ne yasa kika k’i amince da auren nan.”
Mik’ewa tayi ta fita jiki a sanyaye da tunanin halin kakarsu, tana zuwa k’ofar d’akin ta tsaya dan tana jin hayaniyarsu, sallama tayi Amar ya amsa, ba tare data shiga ba tace “Yah Amar Hajia ke son ganin yah Ammar yanzu.”
Amar ne ya amsa da “Yana d’aki bari na fad’a masa.” Juyawa tayi ta fita shi kuma ya shiga ya fad’awa Ammar, fitowa yayi babu ko riga zai fita Junaid yace “Haka kuma za’a tafi wurin Hajiar?”
Ko kallonshi baiyi ba yace “To ko nine Hassan meye a ciki? Ba haihuwarmu tayi ba? Tunda ita ko dare da Allah yasa mana mu samu nutsuwa a cikinshi bata bari mu nutsun ai sai mu fara zuwa mata tsirara inta neme mu.”
Jibril dai da abun duniya ya isheshi da kallo kawai ya bishi, ai kuwa yana shiga Hajia ta kalleshi da wani mamaki, zaune yayi kujerar dake kallonta ya d’ora k’afa d’aya kan d’aya wanda hakan yasa suke iya ganin kwantaccen gashin k’afar shi mai silb’i, ido cikin ido ya kalli Hajiar yace “Mutan makka gani, ance kina kira na yanzu a daren nan, shine nace bara na zo da gaggawa kar azo ko zuciyar ce ta fara bugawa ba daidai ba.”
A murtuke ta kalleshi tace “Duk maitarka wallahi zuciyata tafi k’arfin ka nuna k’warewarka a kanta, shege kenan burinka kenan a kai na.”
Murmushi ya mata na shegantaka yace “To in kuwa hakane baki shawara mana? Ki rage b’acin rai da sakawa mutane idanu, ki dinga samun isashen bacci hakan zaisa ki dinga samun nutsuwa, sannan ki rage yawon surutu da hayaniya, inba haka ba Allah in kika bari zuciyarki ta kamu da ciwo da hannu na zan parkaki na fito da zuciyar na ‘yar da ita.”
Murmushi Hamna tayi harda rufe baki inda Hajia ta gama cika, cikin fad’a tace “To yanzu wace rashin d’a’ar ceta saka shigo min falo babu riga?”
Murmushi ya mata yasa hannu ya shafi k’irjin shi har zuwa kan nonon shi yace “To dan kin kalli wannan meye? Ko jariri dai ba zai iya tsotsar wannan ba, kuma ma Hajajju me kike tsammani dama ga marar mata wanda yayi shirin kwanciya.”
Tsaki tayi yayin da Hamna ta sunkuyar da kai kamar tace k’asa bud’e na shiga, tana mamakin wannan rashin kunya tashi ita kam, a nutse ta kalleshi tace “Wannan take fad’a min wai tare kuka shigo yanzu daga wajen kan amarya, shine nake so naji daga bakinka?”
Kallon Hamna yayi wacce ita ma ta kalleshi, murmushi yayi mata wanda ta tabbatar na mugunta ne, sai yanzu ta tuna Allah ya isar data masa, take tace “Na shiga uku.”
Kallon Hajia yayi yana murmushi yace “…
*Addu’arku*
23/06/2020 à 13:57 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BADAK’ALA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
_*AHALI NA*_
*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`
_Bismillahir rahamanir rahim_
_22_
Murmushi yayi yace “Ni kuma? A ina muka had’u? Ni ina zuwa wannan shirmen banzan ne da har zamu had’u dake? Hajajju ki matseta ta fad’a miki inda ta tafi, amma ni karki tambaye ni, saida safenku.”
Mik’ewa yayi kam ya nufi k’ofa zai fita, juyowa yayi ya kalli Hamna wacce ta juyo ita ma tana kallonshi kamar ta d’ura mishi ashar, wata ‘yar iskar shoki ya kwaso daga k’asa yayi sama da hannu ya rufe rabin fuskarshi yana dariya, haushi ne ya k’ara kashe Hamna wato irin yanda take yi masa ne yayi, kashe mata ido d’aya yayi ya fice daga falon, Hajia kuma kallon Hamna tayi tace “Wallahi idan kika sake fita daga gidan nan ba da izini na ba wallahi dake za’a d’aura auren nan, tashi ki bani wuri.”
Mik’ewa tayi jiki a sanyaye ta nufi d’akin su ita ma Hajia nata d’akin ta shiga, tana shiga ta samu Amna kwance kan gado da rabin fuskarta harya kumbura ga jini daya kwanta a idonta d’aya, kaya ta fara cirewa inda Amna ta mik’e tace “Yawwa kin dawo, Hamna gaskiya daga yau ba zan sake taimakonki ba idan kina son fita a gidan nan, ki nemi izini idan an barki ki fita amma ni ba zan sake amsa sunanki ba idan ba kya nan.”
Juyowa tayi da niyyar sauke mata kwadon bala’i sai kuma taga fuskarta a kumbure, da sauri ta matso ta zauna kusanta tace “Amna meya sameki a fuska haka? Ba dai dukanki sukayi ba?”
Cikin b’acin rai tace “Eh mana duka na yayi, ki duba kiga yanda ya rugurguza min fuska kamar wata jaka.”
Da mamaki tace “Waya dake ki haka?”