BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tun kafin ta k’araso inda yake zaune kan kujera ta basar ta had’e fuska irin ba wasan nan, tana zuwa ko zaune ba tayi ba ta tara masa hannu, (Allah gamu gare ka) d’aga kai yayi ya kalleta da mamaki, mayar da kanshi yayi k’asa bai tanka mata ba, cikin jujjuya baki tace “Kai nake jira.”

D’aga kai ya sake yi ya kalleta, ba alamar wasa shi ma yace “Baki iya sallama bane?”

Saida ta turo baki tace “Ina wuni.”

“Ba wannan na tambayeki ba ai.”

Kallonshi tayi sai kuma ta juya baya ta rik’e k’ugu ta sake mik’a hannunta tace “Ka bani na juya na koma ina da abun yi a ciki.”

Kallon nutsuwa ya mata yace “Me zan baki wai? Kin bani ajiya ne?”

Juyowa tayi da mamaki tace “Ban gane me zaka bani ba? Takarda ta mana.”

Da sauri ya kalli idonta yace “Kinga Sa’ada ba wasa na zo muyi ba, ki d’auko kayanki ki wuce mu tafi, komai dare ina so mu bar garin nan.”

Wani yamutsa fuska tayi tana kallonshi tace “Ai ba haka mukayi da kai ba, ko ka manta?”

Kallonta yayi sai kawai ta ma bashi dariya ganin har wani girgiza take wai ita rashin mutumci take so ayi, mik’ewa yayi ya tsaya gabanta yana k’are mata kallo yace “Jaraba kike so muyi Sa’ada?”

Saida ta rage girman idonta tace “Eh, ai gidanmu ne nan ina da masu tsaya min.”

Ba alamar annuri yace “To ni kuma kinga a gidan naku zan kakkarya ki kuma a gode min akan haka, amma bana so a k’ara miki wani dukan bayan wanda zan miki, dan haka in bala’in kike ji muje gida sai ayi.”

Matsawa tayi baya tana fad’in “A’a me zai kaini gidanku, ni na zo gidanmu kenan ai da kake gani na nan, da kaga na fita to…”

Shiru tayi tana k’yabta ido dan bakinta yake kallo kamar jiran yaji me zata fad’a yake, saida ya kawar da kanshi yace “Ki d’auko jakarki mu tafi, in kuma ba zaki tafi ba ki gaya min.”

Saida ta juya d’an k’aramin bakinta mai d’an tsayi kafin tace “Eh.”

Da kyau ya kalleta yace “Eh me?”

Saida taja baya sosai ta saita k’afafunta k’ofar shiga cikin d’akin Ardayi sannan tace “Ba zan tafi ba.”

Da sauri ta k’arasa shigewa ciki tana ma kanta dariya, da kallo ya bita yace “Eh lallai yarinta ce kamar yanda Hajia suka fad’a.”

Fita yayi ya samu dreba suka k’arasa wani masauki mai kyau a garin suka yada zango anan, dan ya lura wannan bikon mai tsada ne na gaske, watak’ila saiya salwantar da wasu zinariya kafin ta yarda su koma, tunda dai ba zai yarda yayi tafiyar banza ba, uwa uba kuma umarnin gwamnatinshi ce dole a cika ko ba’a so.

Saida akayi sallah magrib yayi wanka yana kwance ya d’auki wayarshi ya tura mata gajeran sak’o kamar haka “Uwar Ammar ce quoi t’on problème? Qu’est ce que tu veux?”

Sanda ta samu sak’on murmushi ta saki ta mayar masa da harufa hud’u tace “Rien.”

Shi ma maido mata yayi da “In dai hakane to ki yarda mu koma gobe.”

Maido masa tayi da “Indai hakane saika yarda zaka hau rak’umi a garinmu.”

Zaro ido yayi yana k’ara nanata karantawa, maida mata yayi da “Amma ai na hau lokacin aurenmu, me zaisa yanzu na hau da girma na haka kawai.”

Cikin basarwa tace “Shikenan sai ka koma inda ka fito kai kad’ai.”

Ba alamar wasa a amon muryarshi yace “Kinsan Allah, wallahi tare dake zan koma, bari ganin fa ina lallab’a ki sa’a ce kika ci.”

Wata dariya tayi kafin ta maido da ” *Sa’ada, Sa’adatu sa’ar mata, ko bakiyi kyau ba kinyi sa’a*, ka daina fad’in sa’a a gabana sunanta gare ni.”

Iko sai Rabba, da mamakin wannan sabon canjin dan shi dai bai santa da shi ba yace “Nima fa har yanzu ban huce kan abinda kikayi ba, dan kin samu na zo shine sai kin waina ni.”

Kafin ta maido ya kirata a wayar dan ya tabbatar mata ta shirya gobe zasu koma, ko da ta d’auka tace “An zo wurin, ai dama an fad’a min ba da son ranka ka zo ba saboda ba so na kake ba dama, shiyasa nake so kawai ka bani takardata tunda banda mahimmanci a wurinka.”

Cike da mamaki yace “Sa’ada ni? Ni ne kike fad’awa haka?”

“To ai gaskiya ce.” Ta fad’a tana juya baki kamar a gabansa, cike da kokonto yace “Anya kuwa Sa’a baki yi waya da babban d’anki ba? Dan naga irin fitinarsa ke kike min yau d’in nan.”

Kai tsaye tace “D’ana ba fitananne bane gaskiya kawai yake fad’a.”

“Shikenan.” Ya fad’a yana d’orawa da “Yanzu fad’a min abu d’aya, zaki shirya ko kuma ba zaki shirya ba, dan ba zan zauna ina lallab’aki ba sai kace wasu yara masu shirin aure.”

Cikin muryar shagwab’a da kuka tace “Eh mana kace haka, idan kana tare dani sai ka nuna min mun girma mun tsufa muna da yara da jikoki, amma idan ka shiga d’aya d’akin saika d’anyance ka zama yaro kana kinibibi…”

Duk da ta kai k’arshen kalmar amma saida ta rufe baki, rarraba ido ta shiga yi tana saurarenshi yana fad’in “Ade nine kinibabben? Ba damuwa karki je d’in ki ci gaba da zama anan.”

Kashe wayar yayi ya aje gefe, shi kad’ai kamar wanda aka tab’a saiya fashe da dariya kuma, wai kinibibi? Shi ne yau ake ma rigima, ko Zeituna dake yarinya ai yanzu ta daina tunda ta haifi nata yaran, in kaga rigimarta yanzu ita ma tana son wani abu shi kuma yaga yanzu ya wuce wannan ajin, to fa haka zasu kwana tana botsare masa yana tarota tana baud’ewa.

A gida kuma rabon ayi zamu ce Amar na kan hanyarshi ta dawowa gida saida ya shigo cikin kwanar gidan wasu samari biyu suka sha gabansa, tsayawa yayi ya bud’e mota ya fito, tunda dai suka ga fuskar wanda suka gani a waya aka kuma biyasu kan su jigata shi sai kawai suka mame shi da duka, su bakwai ne dan haka babu yanda ya iya dasu, dan bak’in ciki kuwa shi ma saida suka masa tsinanniyar karaya a hannu, abunka ga unguwar masu hali babu hayaniya mota ko moto ma sai jefi jefi suke wucewa, saida suka ga ya daina motsi suka barshi nan ba tare da sun raba shi da komai na sa ba sai su da suka d’ora masa takarda a kan jikinshi.

A k’alla mota uku ta wuce amma babu wanda ya kula dashi, Junaid ne kad’ai da yaga motarshi ce anan ya tsaya da niyyar tuntub’arshi yaji lafiya, ya shiga tashin hankali sosai ganinshi a kwance kamar ba ma kama bace babu rai kam, gigicewa yayi ya rasa ta ina zai fara, sai yayi bakin titi da gudu kuma ya dawo yayi hanyar gidan kamar ya k’arasa, yayi haka har sau hud’u kafin daga bisani ya fara kiciniyar janshi zuwa mota, a lokacin kad’ai takardar data fad’i ma ya kula da ita, da sauri ya d’auka tunaninshi abune mai mahimmanci, saida ya bud’a ya karanta rubutu kamar haka ” _Duk wanda ya min kankara sai nayi masa na itace, baka dake ni ka karya min hannu akan banzar k’anwarka ba, to ka dafata ka cinye kai kafin nan muyi jinya tare, banza dak’ik’i mai k’walwar kifi.”_

Da sauri ya zura takardarshi ya ci gaba da janshi har ya sa shi motarshi ya fizga ya bar erea, da suka tafi ganin yan uwa ne da yallab’ansu suka karb’eshi da gaggawa, dan su duk da sun san Amar amma tashin farko ma sun d’auka Ammar d’in ne, cikin ikon Allah suka samo shi dan dama k’ananun raunika ne sai karyar hannu da suman da yayi, saida aka bawa Junaid kyakyawan labari kad’ai ya samu nutsuwar kiran d’an biyun Amar d’in.

Wallahi yana gida kwance yana kallo ana lallasa d’an uwanshi sakamakon masifarshi, da Junaid ya fad’a masa cikin tsananin damuwa da d’an uwanshi yace yana zuwa, bai d’auki lokaci mai tsayi ba ya isa ya same su, har ga Allah Junaid bai nuna masa takardar nan ba dalilinshi kuwa shine, in dai ya gani to baisan ina rigimar zata tsaya ba, a sanin daya ma Amar ba mutum ne mai rigima ba, shi fa da Ammar d’in ne to ko shakka ba zaiyi ba, amma Amar har yanzu abun na bashi mamaki, duk tambayar daya masa sai dai yace ba komai ko ban sani ba ko uhum, haka ya d’auki Amar yace ai sai dai su koma gida, ya zaiyi inba zuba ido ba, yana kallo ya labta Amar a bayanshi ya fito dashi har waje kuma yana k’orafi wai zai karya masa baya k’aton wofi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected