BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Girgiza kai Ummy tayi ta kama Amna suka mik’e tana gyara doguwar rigarta, Husseina ce da mamaki ya isheta tace “Amna kuma? Ai ba Amna bace Hamna ce, Ammar meyasa baka tsaya kayi tunani ba kawai ka hau dukanta haka?”
Dafe k’ugu yayi da hannu d’aya hannu d’aya kuma ya nuna kanshi yace “Kenan yanzu na zama mahaukaci ne da ban iya gane yaran da har goyasu nayi a bayana? Yaran da suka tashi a gaban idona ne zan kasa fahimtar wacece wannan ko wacce waccen?”
Kallonta Ummy tayi dan ta gane wacece ma a ciki, sai dai duhun dake akwai wajen bai bari ta iya ganewa ba, hakan yasa tace “Da gaske ne? Amna ce?”
Gyad’a kai tayi alamar eh, sallalami Husseina ta fara ta rik’e baki tace “Oh ni Husseina, yanzu dama Amna ce nake wa kallon Hamna? Amma meyasa dana kira Hamna kika amsa? Ita tana ina?”
Amna da har yanzu take jin marin nan daya mata da takalmi kuka kawai ta sake fashewa dashi, shi kuma k’wafa yayi ya kalleta ya nunata yace “Daga yanzu duk inda zaki je saina baki izini indai har nine wanda zai aure ki.” wucewa yayi inda Ummy ta bishi da kallo ganin jikinshi biji-biji ga kayanshi sai k’yallin mai suke, kama Amna tayi suka shiga ciki bata yarda sun tsaya falon ba, sama suka haura d’akin su suka zaunar da ita, fad’a Ummy keyi sosai na haushi da takaici, har da cewa “To ubanki ne shi da har zaki tsaya ya miki wannan dukan? Ba dan kin zama sakarya ba ma akan me zakiyi tsaye yana d’irkarki haka? Amna aure fa ake shirin yi miki dashi, da hakane zaku zauna kinsa tsoronsa a ranki? Na tabbata da yer uwarki ce Hamna wallahi ko gudu ne tayi daga gurinshi, dan baya da maraba da mahaukaci idan ranshi ya b’ace.”
Amna dai shiru tayi sai sharar hawaye take, hakan yasa Ummy cewa “Kiji harda wani cewa wai in zaki fita saida izininshi, to mu duk aikin banza ne kenan a gidan? To zaki fita bada izinin nashi ba sai naga in kasheki zaiyi.”
D’agowa Amna tayi cikin kuka tace “A’a Ummy, tunda dai yace haka ni zan bi umarninshi, zan nemi izininshi kafin na fita, shikenan sai a zauna lafiya, ko Mama ma tana fad’a mana mu dinga jin maganarshi dan shi kad’ai ne ke tsawatar mana.”
Da mamaki Ummy tace “Ke yanzu sai ki biye masa kuma?”
Jinjina kai tayi alamar eh tare da cewa “Ummy hakan shine zaman lafiya na, nasan ni ba yer uwata Hamna bace, nice mafad’aciyar kuma mai zuciyar, amma akan yah Ammar bana da ko d’aya, bansan meyasa ba.”
Tab’e baki Ummy tayi tace “Lallai kina da aiki Amna.”
Ko da yayi wanka shiryawa yayi cikin riga da wando bak’ak’e, makullin mota ya d’auka ya sake fita, k’aramin gurin cin abinci ne *Kebab* ya zauna ya ci abinci, daga nan kuma hanya ya d’auka saida ya samu inda babu hayaniya ya paka nan, jingina kawai yayi yana sauraron wa’azindake tashi a motar, maganganun Ummy ne kawai ke dawo masa a k’wak’walwa, awa d’aya da rabi ya d’auka a wurin nan kamar mai bacci kafin wayarshi ta fara ruri, saida kiran ya tsinke aka sake maidowa kad’ai ya taso daga kwanciyar da yayi ya d’auki wayar, a zuciyarshi yace “Abdullahi kuma? Meyasa zai kirani a wannan lokacin?”
Tsaki yayi saboda wata zuciyar data fad’a masa watak’ila zai maka k’orafine saboda baka je d’aukar amarya ba, d’auka yayi ya d’ora a kunne yayi shiru, daga can b’angaren Abdullahi yace “Ammar yane? Kana cikin gari ko kana gida?”
Can k’asan mak’oshi yace “Lafiya?”
Abdullahi ne yace “Lafiya ba lafiya, dama a cikin yan matan amarya ne aka bar wasu basu samu komawa tare da sauran mutane ba, kuma gashi duk wanda na kira wallahi wasu ma sun fad’a min kai tsaye ba zasu iya dawowa d’aukar su, ni ma kuma mota ta tun safe tana hannun k’ane na, yanzu haka nafi awa d’aya ina jiran adaidaita sahu ko taxi na samar musu amma wallahi shiru, gashi dare na k’arayi shiyasa nace bara na kiraka dan Allah ka zo ko Hamna ka d’auka, tunda kaga gidanku ba bari fitar dare ake yi ba inba da dalili mai…”
Ammar ne ya dakatar dashi cikin sanyayyar murya yace “Ya isa haka dan Allah, magana ba tsayawa ba numfasawa, yanzu kenan nufinka naje na zama drebata na d’auko ta? Bayan kuma a gida babu wanda ma yasan da fitarta, to ba zan iya ba.”
Abdullahi ne yace “Dan Allah Ammar ka taimaka, bana so ne ta shiga matsala a dalilin halartar bikin nan nawa, dan Allah.”
Tsaki yayi ya kashe wayar, hakan kuma yasa Abdullahi yarda d’ari bisa d’ari cewa zai zo, dan haka ya ci gaba da tsayuwa a bakin titin, ai kuwa baifi minti ashirin ba saiga motar Ammar, dan dama yasan gidan da jimawa dan anjima ana ma gidan tsare tsare tsare da tanadi, k’arasawa sukayi k’ofar gidan Abdullahiya shiga ya samu su Hamna cirko cirko su biyar a farfajiyar gidan, Hamna ya kalla yace “Hamna ki taso ga Ammar nan zai tafi dake.”
“Wa!? Ta fad’a da k’arfi tana zaro ido ta d’ora da “Waya fad’a mishi ina nan? Meyasa sai yanzu ya zo bayan ban ganshi d’azu ba?”
Abdullahi ne yace “Yanzu dai ba lokacin magana bane ki taso ku tafi kafin ya mana tijara ni dake.”
Mik’ewa tayi tace “Ina zuwa.” Cikin d’akin ta shiga ta samu amaryar tare da babbar yayarta tana k’ara gyara mata d’aki, uwar d’aki suka shiga Hamna tace “Dan Allah k’awata taimako zaki min.”
“Taimakon me kuma k’awata?” Cikin fargaba tace “Yah Ammar ne ya zo d’auka ta, kuma jiya ma a wurin kamun ku saida ya min fad’a kan fita babu hijabi, shine nake so dan Allah ki ara min ko da babban mayafi ne, insha Allahu gobe idan na taso daga école zan biyo na kawo miki.”
Murmushi tayi ta nuna mata wurin kayan tace “Besty akan wannan ne har kike cewa wani taimako? Ki duba ga kayan nan sai ki zab’a.”
“Yawwa.” Ta fad’a tana bud’a wurin kayan, wani babban mayafi ta d’auka wanda ya dace da kayan nata, ita kanta data kalli madubi sai taga tafi kyau da kamala, sai ta ganta kamar wata amaryar ita ma, fitowa tayi zata fita sauran k’awayen suka ce ai ba zata barsu ba, tare suka fito inda ta zagaya zata shiga motar, da kallo ya bita har ta shigo, amma take jikinshi ya bashi wannan ba mayafinta bane, cikin lallami Abdullahi ya zuro kai yace “Abokina ka taimaka ka aje wad’annan ma mana, in kayi haka zaka samu lada fa.”
Kallonshi yayi fuskar nan a d’aure yace “Me zai hana ka basu makwanci a gidan naka? Ai sabgaka suka zo? Ni munyi da kai zan zo d’aukar maka mata ne?”
Murmushi Abdullahi yayi yace “Ba haka bane, amma dai ka taimaka.”
Mayar da kallonshi yayi kan titi yace “Kasan zasu rage maka jin dad’i kenan? Shine ni ma zaka takura min.”
Kallon yan matan yayi da suka saki baki suna kallonshi yace “Ku muje.”
Da sauri wuka bud’a suka shiga suka zauna, ko kallon Abdullahi baiyi ba ya ja suka wuce, saida sukayi tafiya mai nisa babu mai magana kafin ya daidaita madubin gabanshi yana k’arewa yan matan kallo, a ranshi yake k’yamar irin shigarsu kamar ba yaran musulmi ba, babu wacce babu k’arin gashi a kanta da muguwar kwalliya ta d’aukar hankali, girgiza kai yayi ya juya ya kalli Hamna, sai kace wata malama k’wafa yayi ya ci gaba da tuk’i, sunyi nisa muryar d’aya daga cikin yan matan tace “K’awa Hamna da kina da yaya kyakyawa haka shine bamu sani ba?”
Wani buhun haushi ne ya tasowa Hamna, tasan halin k’awarta dan haka ta d’aure fuska ta kalli Ammar da yake tunanin kalar iskancin da zai tatawa yarinyar, tab’e baki tayi a zuciyarta tace “Wai kyakyakwa, humm.”