BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Zeituna kasa bacci tayi da suka ce wannan kayanta ne, ta nemi tasan dalilinsu na canzawa amma kawu Mamu yace ai d’iyarshi ce ita ma, zai iya yi mata komai kamar yanda zai wa su Jumare, wanda a wannan lokacin Jumare dake kamar k’anwa ga Zeituna dan ta bata shekara uku haushi kamar zai kasheta, har d’aki ta samu Jumma tana kuka wai an yiwa Zeituna siyayya ita ba’a mata ba, nan ta bata hak’uri tace ita ma gobe zata amshi kud’i wurin babanta a siyo mata, da haka kad’ai tayi shiru ta koma d’akin su, haka tayita hattarar Zeituna tana zaginta tana harara tana mata cilli da kayan da aka siyo, saida kawu Mamu ya mata magana daga cikin bukkarshi yace zai ci uwata kad’ai ta shafa mata lafiya.

➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️

Ko da Junaid ya zo gida shiryawa yayi ya sake fita, bai zame ko ina ba sai gidansu Maryama, yana zuwa kuma sun fita ba jimawa, amma yayi nasarar ganin Huda a k’ofar gida da madara tana sha, hannunta ya kama yace “Huda ko?”

Kai kawai ta d’aga mishi, murmushi yayi yace “Ina mamanki?”

Saida ta kalli hanyar dasu Maryama sukayi tace “Yanzu suka fita ita da tanti Iklima.”

Nuna hanyar yayi yace “Kenan ta nan suka bi?”

“Eh.” Ta fad’a tana sake d’aga mishi kai, mik’ewa yayi yasa hannu aljihu ya ciro jaka goma guda ya damk’a mata a hannu yace “Wannan kisha madara kinji ko.”

Da sauri ta fizge hannunta ta sakar masa kud’in tace “A’a bana so, Mamata ta hanani karb’ar kud’in maza.”

Da mamaki yace “To me yasa?”

Tana kallon idonshi tace “Tace wai ita zatayi aiki dan ta samo min komai da nake so.”

Murmushi ya sakeyi ya k’ara mik’o mata kud’in yace “To ki karb’i wannan, ni bana cikin wanda ta hanaki karb’an kud’in su saboda ni mahaifinki ne.”

Zaro ido tayi tace “Kaiii, ni fa bana da Baba, mutane ma ce min suke shegiya, kuma suna cewa mamata yar iska ce.”

Jim yayi saboda rashin jin dad’in abinda ya fito daga bakin yarinyar, murmushin yak’e ya mata yace “To yanzu dai karb’i wannan, insha Allahu lokaci yayi da zaki ga mahaifinki kema.”

Mak’ale kafad’a tayi tace “Um um, idan na amsa Mama zata toye min hannu na da wuta.”

Lura da yayi ba zata karb’a ba yasa yace “To shikenan, yanzu fad’a min me kike so na siyo miki idan zan dawo.”

Rufe baki tayi tsoro ya bayyana a tare da ita tace “Dan Allah karka fad’awa Mama na nayi hira da kai, ta hanani tsayawa da maza a waje.”

Tana gama fad’a ta ruga a guje tayi cikin gidan, da kallo ya bita shi kuma yana mamakin yanda Maryama ke tsaye kan tarbiyyar ‘yarta, amma kuma ita tana zubarwa da yarinyar mutumci, motarshi ta shiga ya nufi inda yasan zai ganta, bai kuwa sha wahala ba ya samu Iklima zaune bakin wani dakali a pacific tare da wani, fitowa yayi suka gaisa ya tambayeta ina Maryama? D’akin dake bayansu ta nuna mishi tace “Tana ciki, amma tana fitowa yanzu.”

Kallon d’akin yayi yaji zuciyarshi na neman bugawa, ji yayi kamar ya tura k’ofar ya shiga, amma kuma tsoron abinda zai gani yasa ya kasa hakan, tsayuwarshi kuma ya jirata shi ma dai wani k’arin tension d’in ne, juyawa yayi ya bud’a mota zai shiga sai yaji an fito daga d’akin, juyowa yayi sai kuwa suka had’a ido, sam bata cikin yanayin farin ciki dan fuskarta a had’e take, bayanta wani matashin yaro ne ya fito da ba zai wuce shekara ashirin da d’aya zuwa da biyu ba, Maryama kuma a k’alla ba a k’asara ba tana da shekara ashirin da shida zuwa da bakwai, zai iya kiranta warin k’anwar shi Umaima, wani buhun haushi ne ya rufe shi ya tsaya yana kallonta harta k’araso kusa da Iklima, wannan matashin kam sai wasar baki yake ya bawa d’aya abokin na shi hannu yace “Saura kai, amma ba zan jira ka ba gaskiya.”

Mik’ewa shi ma yayi ya shiga d’akin sai Iklima data juyo ta kalli Junaid tace “Yallab’ai Junaid sai anjima.”

D’akin ta shiga yana kallo suka rufe, zaune Maryama tayi bakin dakalin ita ma dan jiran Iklima, shi kuma waccen matashin ya wuce Junaid ya bishi da kallo kamar ya shak’e shi, amma ya zaiyi duk abinda ya samu shamuwa watan bakwai ne ya ja mata, kallonta yake kamar zai had’e ta ita kuma ta had’e fuska tana danna wayarta, rufe murfin motar yayi ya tako ya zo gabanta, cikin wani yanayi yace “Yanzu dan Allah Maryama baki ji kunya ba?”

A hankali ta d’ago kai ta kalleshi tace “Kunya kuma? Ta me fa?”

Girgiza kai yayi yace “Maryama me waccen yaron zai miki? Idan dan kud’i kike siyar da mutumcinki na baki kud’i Maryama dan ki tsira daga rainin irin wannan yaran, idan kuma dan jin dad’i kike bud’a farjinki ga kowane d’a namiji, domin Allah me waccen zai iya yi miki? Me zai hana ki nemi cikakken namiji wanda zaki san ya shige ki har ma ya sakaki kukan dad’i ko na wahala, amma waccen da ko kaciyarshi bata gama warkewa ba tsiyar me zai tsinana miki? Ni fa da aure nake sonki, Maryama dan Allah ki taimaka ki aure ni ko na kwana d’aya ne, ni kuma zanyi k’ok’ari na ga na gamsar dake ta kowane fanni har ki yarda ki zauna dani, amma wannan abun kunya dame yayi kama, yaron da na tabbatar kud’in daya biyaki shi kanshi k’uru ce yayi ya baki su saboda shed’an na k’awata mishi yin zinar, mtssss.”

Duk da ba cikin hargagi yake maganar ba amma ta tabbatar ranshi ne ya b’ace, mik’ewa tayi ita ma cikin b’acin rai da fitar da hawaye a idonta tasa hannunta ta fito da kud’i a rigar nononta ta warware su, jaka biyu ce nuna mishi tayi tana fad’in “Kaga abinda ya bani, wannan kuma zan ci abinci da su na tsawon kwana uku ni da ‘yata, malam ka fita a harka ta mana, soyayya ce nace banayi ka shafa min lafiya mana, ko ana so dole ne?”

Sai kuma ta fashe da kuka ta koma ta zauna kamar an turata, cikin kuka ba tare data kalleshi ba take fad’in “Taya kake tunanin zan ji dad’in rayuwata? Taya kake tunanin ina farin ciki da abinda ke faruwa da ni? Waccen yaron fa bai fi sa’an k’ane na ba na biyu, amma yau ni ce na kwanta yaron can ya nemi yanda yake so, meye anfanin rayuwa ta Junaid? Me yasa iyayena zasuyi min haka? Me yasa wannan mutumin da ko sunanshi ban sani ba ya tafi ya bar ni da ‘yarsa? Me ya kamata nayi yanzu? Junaid ka fahimci wani abu, duniya yanzu ba’a taimako dan Allah sai dan abinda zaka bayar ko za’a samu daga gareka, da irin hakane aka lalata min rayuwata, kuma da hakanne ma yanzu ake ci gaba da gurb’ata min rayuwar.”

A hankali ya zauna akan dakalin cikin sanyin jiki ya kalleta yace “Maryama rayuwarki na da anfani, kuma tabbas yanzun rayuwarki a gurb’ace take, amma idan har kin so canzawa kuma kika bani dama wallahi zaki dawo sabuwar mace kamar babu abinda ya tab’a faruwa dake, dan Allah Maryama ki amince da soyayya da nake miki, wallahi babu nufin cutarwa ko sharri a zuciyata, ni zan zama miji na gari a gareki, sannan zan zama uba da za ayi alfahari da shi ga ‘yarki Huda, ki amince ki bani linzamin ragamar rayuwarki, zan d’aukeki na kaiki cikin ahalina kuma farin cikina, kema zaki zama d’aya daga cikin dangina.”

Shiru tayi sai yar shashek’ar kuka da take tana tunanin abinyi, tabbas tun zuwanta garin nan a cikin manya manyan mutanen da take jin labarinsu a gari akwai ahalin Gaga, wanda suke ji da iko, matsayi, da kuma naira, ahali ne daya tara yan boko sosai kuma bokon ta musu rana, matsalarta d’aya shine tana jin tsoron shiga cikin babban dangin irin wannan saboda abinda ka iya zuwa ya dawo, tana cikin wannan tunanin Iklima suka fito suma, saurayin wucewa yayi inda Iklima ta kallesu tace “Mari kina nan dama? Ai na d’auka kin tafi da naga mutumin na ki ya zo.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected