BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Jim ta d’anyi saboda haushin Ammar data sake ji, har ga Allah tana b’oyewa ne dan kar Ummy taji ba dad’i, da k’yar ta kalleta tace “Kin fad’awa Abba ne?”

Girgiza kai tayi tace “Hamna ba zan sanar dashi yanzu ba, kema kin sani ina fad’a masa zai biyo jirgi ya taho, ni kuma ina so mu fara tafiya gida na d’an shirya ki da kuma ni saina kira na fad’a musu.”

Shiru tayi kawai dan bacci ke son d’aukarta, saida aka k’ara tabbatar da lafiyarta da bebyn sannan aka sallamesu bayan an bata magungunan da zasu taimaka mata, suna zuwa gidan da suke Ummy ta zama mai haihuwar tare da anfani da duk abinda zai kawo mata ruwan nono wanda dama ta tanede shi saboda ranar, sai lokacin ta kira gidan ta sanar dasu, lieutenant yayi murna sosai da kuma fad’an rashin dawowa har haihuwa ta risketa tana nesa dasu, ya fad’a mata zasu zo tare da Hajia dan ba zai yarda ta taho yanzu ba, saita nuna masa ba komai kawai idan sukayi ko sati biyu zata dawo, tunda Zeituna ma gaf take da haihuwa bai kamata ya taho ya barota ba, da haka ya gamsu ya zauna sai hotunan yaro da suka game gidan da familyn cikin d’an lokaci.

*Gaga’s house* da dare suna tafiya a hankali a cikin unguwar ya ga duk tayi sanyi sosai ba yanda ya saba ganinta, jawota yayi jikinshi yace “Lafiya? Me kike tunani?”

Saida ta d’ora hannunta kan k’irjinshi tana takawa a hankali tace “Hamna nake tunani, tunda na tashi yau nake tunaninta ina ji kamar wani abu na faruwa da ita, ta canza sosai amma kuma bata son yin doguwar magana da ni, bansan me yake damunta ba.”

Shafata yayi yace “Karki damu kinji, watak’ila bata jin dad’in zaman gidan nan ne shiyasa, amma idan kina so saina kaiki ki ganta amma fa bayan kin haihu.”

Murmushi tayi tace “Nagode.”

Wayarshi tayi k’ara yana dubawa ya ga kiran Amar, yana d’auka Amar tsabar farin ciki da kuma tsokana yace “Kai yaro kana ina? Ka zo gida fa Ummy ta haihu.”

Gabanshi kawai yaji ya fad’i ba tare da sanin dalili ba, amma saboda jaraba sai yace “Amar ni ne yaron? Ni ne dai yaro ko? To ka bari na dawo gidan zaka maimaita haka da bakinka.”

Amar ne yace “Naji dai, yanzu ka duba WhatsApp d’inka na tura maka hoton bebyn, anan dai gida kowa ya damemu da cewa wai yafi kama da kai, ni kuma a ganina ai dani da kai duk d’aya ne.”

Murmushi Ammar yayi yace “Hakane, amma ai na fika manyan ido, na fika dogon hanci, kai kawai gaskiya suka fad’a na fika kyau.”

Yana fad’a kuma ya kashe wayar ya shiga WhatsApp, dannawa yayi foton ya fara alamar bud’ewa, fad’uwar da gabansa ya sakeyi yasa shi d’auke idonshi daga kan yaron, a hankali ya sake kallonshi idonshi bud’e kamar ba yaron da aka haifa yau ba, sanye da kayan sanyi masu hula safar k’afa data hannu, hancinshi tubarkallah zungurere. A hankali yake jin abun na shigarshi kamar sihiri, ba zai iya tantancewa ba k’auna ce ko soyayya, amma dai k’anan nashi ya shiga ranshi daga kallo d’aya, murmushi yayi ya jawo Amna yace “Kinga Ummy ta haihu.”

Da sauri ta k’ura idonta tana fad’in “Na gani.” Tana ganin yaron cikin farin ciki tace “Wow mai kama da jarumi na.”

Kallon idonshi tayi tace “Kamar kayi kaki ka tofar wallahi.”

Kallonta yayi, haka kawai yaji ya tsargu sai kawai ya share yace “Haka zaki haifo naki kema sak ni.”

Ko da suka dawo gida sun samu anata wannan murna, lokacin Zeituna ma ita kawai tasan me take ji ana dai ganinta, saida dare yayi ta fara nak’uda sosai, likitar su Ammar aka kaita da gaggawa, ta jima tana nak’uda ta galabaita sosai, ana kiran sallah asuba ta haifo jaririyarta ita ma mai kama da ita gashi har saman goshinta luf luf, amma ana buk’atar k’ara mata jini dan ta rasa shi, lieutenant ne yace a duba nashi, har an duba za’a d’iba Ammar yace a d’ibi na shi, lieutenant yace “Ai akwai buk’atar a fara dubawa idan yayi daidai.”

Murmushi ya masa yace “Ni fa jininka ne, ina da masaniya akan jininka da nawa Abba, amma in baka yarda a dararawa matarka ba sai an duba ni to a duba.”

Dariya kawai lieutenant yayi, duk da haka da aka shiga ciki saida yasa aka gwada jinin sannan aka diba aka saka mata, tubarkallah masha Allah, a cikin kwana d’aya an samu k’aruwar yara biyu *Fatima Zahra* da kuma *Shureim*, fatan Allah ya raya.

*Bayan sati biyu*…

*Alhamdulillah*
14/10/2020 à 00:58 – Ummulkhairi: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*BADAK’ALA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_

*SADAUKARWA GA*

‍‍‍ _*AHALI NA*_‍‍‍

✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ ️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_47_

*Bayan sati biyu* yau Junaid ya tafi makaranta yana cikin koyarwa aka ce ana sallama da shi, yana fitowa yayi mamaki sosai ganin *Sani* tare da *Salma* a tare dashi, k’arasawa yayi suka gaisa ita ma ta gaishe shi, da mamaki yace “Tonton lafiya dai ko?”

Saida ya kalli Salma ya mata alamar ta basu wuri kafin ya gyara tsayuwa yace “Lafiya ba lafiya ba Junaid, wata alfarma na zo nema a wajenka.”

_*Anzo wajen, Sani dai d’an Innusa ne yayan Alhaji, wanda yace baya buk’atar taimako ko alfarmar Alhaji Suley, dalilinshi yasa Hajia dagewa ta ga yaranta sun zama masu muk’ami a gwamnatacce, meya faru yau da har aka zo neman alfarma a wajen ahalin Suley?*_

Junaid ne yace “Tonton wace irin alfarma kuma? Ai daka kirani a waya sai naje har gidan ma.”

Murmushin jin dad’i yayi yace “A’a ba sai ta kai ga haka ba, dama akan maganar makarantar yer uwarka Salma ne?”

Saida ya kalli inda take tsaye da uniforme d’inta yace “Wani abu ne ya faru?”

Cike da damuwa yace “Kasan dai yaran yanzu ka haifesu ne baka haifi hali ba, tana tare da k’awaye ne da basa jin magana wanda yasa sukayi rashin kunya wa malaminsu, hakan yasa aka koresu tare da tab’a musu conduite (bansan me zan kirashi da turanci ba), yanzu tsawon sati d’aya kenan muna ta bibiya da bayar da hak’uri dan a gyara ta koma, amma abun ya ci tura wallahi, shine sai jiya malamin yace idan akwai wani babba ko malamin da muka sani mu mishi magana, shiyasa na tuntub’e ka dan kasa baki dan Allah ta koma.”

Ajiyar zuciya ya sauke, zai so ya taimaka musu sai dai kuma yaji Hajia tace duk wanda d’aya daga cikin iyalin Innusa ya neme shi taimako ya fara fad’a mata kafin yayi, bai nuna masa komai ba sai cewa da yayi ba komai zaiji da matsalar, godiya ya masa suka koma suka tafi, shi ma aji ya koma da tunanin yanda zaiyi, shin ya fara fad’a mata ne ko kuma kawai yayi? Da wannan tunanin ya kammala ya dawo gida, da rana tsaka ya tarar da tashin hankalin da baiyi tsammani ba.

Yaran gidan na wasa tare da Huda wacce ita kanta bata cika sakewa ba idan tana cikin yaran, Hajia na fitowa ta gansu sai kawai ta musu tsawa tace “Kai, maza ku wuce ciki, karna sake ganinku da yarinyar nan dan matsatinku da nata ba d’aya bane, kuji ni ko.”

Kai suka d’aga mata alamar eh suka shiga ciki, wannan magana data fad’a a kunnen Maryama wacce ita ma ta fito kiran Huda dan bata so tana shiga cikinsu, tana jin haka ta matso tace “Da me suka fita Hajia? Kina babba kike fad’in maganar nan a gaban yara, ina ce dai nan daga jikokinki sai jikokin Hajiarsu Jibril, ko ita ma jikokinta basa da damar yin wasa a gidan nan ne?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected