BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Sama da k’asa ta harareshi tana kallo ta ga me zaiyi, tsaf ya haye gado har da jan zani ya rufe, murmushi ta saki mai ciwo kafin ya kalleta yace “Idan aka kira sallah la’asar ki tashe ni.”

Da kallo kawai ta bishi tana tsaye bata gusa ba, tun yana kallonta yana murmushi har ta ga idonshi rufe dai alamar yayi bacci, cikin takonta na hankali kwance ta shiga ban d’akin ta d’ebo a murfin butar dake ciki ta fito, saida ta tsaya kanshi ta juye masa ruwan a fuska.

*Aiki ya kwaso ki Hamna.*

Da k’arfi ya firgita ya tashi yana zazzare ido yana kallonta, cikin goge ruwan fuskar tashi yace “Ke lafiyarki k’alau? Me ke damunki?”

Saida ta rik’e k’ugu tace “Abinda ke damunka.”

“To miye haka?” Ya fad’a da k’arfi, tab’e baki tayi tace “Babu ta yanda za ayi kayi bacci wallahi bayan ni baka barni bacci ba, haka kawai.”

A nutse ya kalleta yace “Hamna zaman lafiya kike so ko tashin hankali? Duk wanda kika zab’a shi zan zage damtse na nuna miki, tunda ni har siyarwa nake kuma ina koyar dasu.”

Wata yar dariya tayi tace “…

*Alhamdulillah*
04/11/2020 à 14:39 – Ummulkhairi: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*BADAK’ALA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_

*SADAUKARWA GA*

‍‍‍ _*AHALI NA*_‍‍‍

✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ ️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_72_

“Duk wanda kake ji nima shi nake ji.”

Murmushi yayi yana sauka daga kan gadon yace “Hum!”

Fita yayi daga d’akin ya koma falo, nan ma ko da ya kwanta kan kujera tayi tsaye ai babu shi babu bacci, tashi yayi ya koma d’akin yasa key da sauri, babbugawa ta shiga yi tana kiran ya bud’e, dariya ya mata yace “Indai kina da zuciya ki rabu dani, na gane me kike buk’ata yarinya, tanadi nake miki har a jima da dare saina b’arar miki da ita.”

Hak’ura tayi ta kwanta a falon ita ma, ko da aka kawo mata abinci ta ci ta sake shan magani dan jaraba ce kawai amma tana jin jikin sosai. Bata jimawa da kwantawa ba kawai amai ya sake taho mata, da gudu ta shiga ban d’akin dake falon d’an nesa da madafa, jin kakarin abun yake daga sama ba sosai ba, tasowa yayi yana fitowa ya tabbatar da abinda yake zargi, tsaye yayi yana mata dariya har ta ida ta juyo zata fito, wurga masa harara tayi zata fita yace “Madame ki fad’i gaskiya mana, duk yanda akayi an sake samun k’aruwa ne.”

Wani kallo ta masa tace “K’aruwa fa, da kai? Shikenan dan na zama kaza daga tab’a ni sai d’aukar ciki? Allah ya sawak’e.”

Hannunta ya kama tana ta k’ok’arin k’wacewa amma ya rik’e gam, saida ya kaita har d’akinshi ya kwantar da ita kan gado, k’afarta taga ya d’aga yana shirin saka mata hannu, da sauri ta yunk’ura ta tashi tana fad’in “Malam lafiya?”

Kallonta yayi fuska a had’e yace “Kwanta.”

Cike da tsiwa tace “Na k’i na kwanta d’in, Ammar ka rabu dani mana.”

Sam babu alamar wasa ko walwala a fuskarshi ya sake kallonta, hannu yasa ya kwantar da ita da k’arfi ya taushe da hannu, hannu ya zura cikin rigarta ya janyo pant d’inta ya jefar, ihu ta fara tana fad’in “Allah ka k’yale ni banda lafiya, Ammar kashe ni fa zakayi, wai kai baka da iman…?”

Da sauri taja bakinta tayi gum tare da rintse ido sosai, ta d’auka ita ya kaiwa wannan naushin, ashe gado ya daga dan shi kanshi ya so d’auketa da mari, amma ya kasa baisan me yasa ba? Idonshi jawur ya kalleta ya juyo da fuskarta zuwa kallonshi da k’arfi yace “Kalle ni nan.”

A hankali ta bud’a idonta ta sauke akan shi, rarraba ido ta shiga yi tsoron yanayinshi ya shiga zuciyarta sosai, a hassale sosai yace “Akan me zan bani umarni gaba da gaba ki fad’a min ba zakiyi ba? Wacece ke Hamna? Me kike ji dashi da zaki dinga min abinda kika ga dama?”

Rikicewa tayi ta rasa tunaninta baki d’aya, cikin had’iyar yawu masu d’aci tace “Bo…sss, kayi hak’uri dan…”

Cikin daka tsawa yace “Waye Boss d’in?”

Da k’yar ta d’aga labb’anta tace “Abb…” Sai kuma tayi shiru ta kasa k’arasawa ta fashe da kuka, kallon fuskarta yayi sosai yanda take kukan da gaskiyarta, a take yaji gwiwarshi tayi sanyi zuciyarshi ta raunata sosai, sai kuma yaji haushin kanshi na kukan da take yi dalilinshi, a hankali ya d’an d’agata ya koma gefenta ya kwanta yasa hannu yana share mata hawaye, ture shi ta fara yi amma me Ammar zaiyi saiya shiga manne mata yana rik’eta a jikinshi gam.

Ita ba tayi shiru ba kuma bata tsaya ba, kallonta yayi a raunane ya sassauta muryarshi yace “Kiyi hak’uri kinji, ba zan sake ba to na miki alk’awari.”

Da wani fitinanne mamaki ta kalleshi, Ammar ne ke bata hak’uri har da alk’awari? Lallai duniya juyin waina ce, ganin yanda take kallonshi yasa ya k’ara rusunawa yace “Eh kiyi hak’uri, ba zan sake saka ki kuka ba, *Hamna ki fahimci rauni na akan ki mana*, wallahi kina da mahimmanci a zuciya ta, amma ba zaki gane ba yanzu saboda nasan kin tsane ni.”

Sake mannata yayi a k’irjinshi yana ci gaba da shafa kanta, jin tayi shiru sai ajiyar zuciya take saukewa, wallahi ji take kamar ta k’urma ihu dan dad’i, *Ammar ne ke mata kalamai haka da sanyi sosai, kuma sanyin ma ba mai cutarwa ba? Lallai ta yarda ita d’in wata ce a zuciyarshi, to ko wannan dalilin ne yasa bai cika saurin kaiwa jikinta ba kamar yanda yake da saurin kaiwa a jikin yer uwarta? Amna har dukanta ya tab’a yi amma ita iyakarta dashi mari a fuska, wuuu!*.

Bacci na neman d’auketa kan k’irjinshi taji yace “Ya kike jin jikinki yanzu? Da sauki ko na kaiki asibiti?”

Saida ta turo baki gaba ta rufe idonta kamar tayi bacci, jin bata bashi amsa ba yasa shi lek’a fuskarta, k’ura mata ido yayi ganin tayi wani fauuu da ita, a hankali ya d’ora bakinshi kan nata ya sumbata, sake kallonta yayi yace “Bakin kamar chocolat, *ina sonki* amma baki da hankalin da zan fara bani kisan al’amarin nan a yanzu.”

Sake tura kanta yayi ya ci gaba da shafata, sai tayi kamar ta farka kuma ta daure tayi shiru, Ammar? Yana so na? K’wafa tayi a ranta tace “Lallai ma mutumin nan, ba zai fad’a min ba saboda banda hankali, ai kuwa ka shiga ukunka wallahi.”

Haka ta wuni a galabaice babu lafiya, da dare ko da ya shigo a gajiye shima yayi zaune kan kujera yana kallonta, rigar kanti ce ta saka marar nauyi wacce ta dace da ita, ita dai bata ce dashi komai dan haka yace “Kankana me kika dafa ki kawo min na ci? Yunwa nake ji sosai.”

A wani yamutse ta kalleshi tace “Me na dafa? Ai kai zan ma wannan tambayar me ka shigo min dashi? Ina fama da kaina ne zan tafi maka d’ori?”

Kallonta yayi na yan dak’ik’u, lallai da aka ce kar Allah ya kawo ranar yabo, a take ya tuna da Amna sanda take amarya, da kanshi yace kar tayi girki amma saida tayi, murmushi yayi a ranshi ya mata addu’a kafin yace “To me kile so na siyo miki?”

Saida ta kalli tsakiyar idonshi tace “Kaza.”

Wani kallo ya mata yace “Kaza kuma? Bayan wacce kika ci jiya?”

Saida ta d’an d’ago daga kan kujerar tace “Eh na ci cin dole ba, kuma aikin da kayi ai yafi na kazar da na ci, dan haka siyo min yanzu na ci na darje.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected