BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
*Allah ka shirya mana zuri’a*
Sallamar wani daga cikin masu neman Marfu’a ne wanda yake kira ta k’i d’agawa ta katse musu hanzari, tsaye yayi yana muzurai ya kalli wanda ke karta yace “Marfu’a ta zo ne?”
Wani d’an daudu ne ya kalleshi ya yatsina fuska cikin harshenshi na mata yace “Kaga wani sabon salo kuma shafa kwalli da tab’arya, to yanzu duk nan cikin mu wa ka aje ya maka gdinta da zaka mana tsaye haka saman ka kana tambayarmu ita.”
Wani jan kallo ya masa zaiyi magana wata mace tace “Ka wuce mana tana ciki, mu ka tsaremu ka tambayemu ita kamar ajiyarta ka bamu.”
Su Marfu’a dake d’aki suna jin ance ya wuce ta zabura ta mik’e dan ita tasan masifar *Labo*, da sauri ta kalli Ma’aruf tace “Labo ne fa, yi sauri shiga nan.” Ta nuna mishi bayan wasu tarin kaya, ba musu kuwa ya tattara rigarshi da wando ya kutsa ciki yayi shiru, saida ya kalli takalmin dake k’ofar d’akin na Ma’aruf kafin ya wuce ciki ko sallama babu, shigarshi kuma yayi daidai da Ma’arufa dake kwance kan gado tana gyara d’aurin k’irjin ta, wani kallon tuhuma ya dinga bin d’akin dashi harda ma ita kanta, da k’yar ya tsaya gabanta ya yaye zanin jikinta, ganin babu komai jikinta yasa yace ” Me hakan ke nufi? Ke da wani d’an iskan ne a d’akin?”
Kamar zatayi kuka tace “Wai me yasa kake hakane Labo, ni da wa ka gani a d’akin nan? Zuwa na fa kenan daga k’auye wanka kad’ai nayi.”
“To amma takalmin uban waye na gani a k’ofar d’akin, tunda dai ba naki bane.”
Kamar wacce ta tashi daga bacci tace “Uhum! Ina jin takalmin Big (Ma’aruf suke kira da haka a gidan)ne, ina jin ma harya fita ai.”
Jin ta fad’i haka yasa ya kalleta ya sunkuyo tare da kwantawa gefenta, hararan gefen ido ta masa tana yak’e, shi kuma nan ya fara shafarta yana fad’in yayi kewarta, na d’aya idan ta hanashi samun abinda yake so bala’i zai fara yanzu watak’ila ya had’a da dukanta ma , na biyu kuma tana buk’atar kud’i shi kuma tasan a wannan fannin indararo ne baisan ciwon kud’i ba, dan haka tana ji tana gani ya sake mata wawiyar caccaka.
Ma’aruf na cikin kaya yana jin duk tsiyar dake faruwa yayi luf abin shi, sun jima kafin ya saka kayanshi ya fito da kud’i ya jefo mata ya fice, d’aukar kud’in tayi ta kalli k’ofar daya fita tace “K’aramin d’an iska kawai, kaji da bak’in halinka.”
Juyawa tayi inda Ma’aruf ke k’umshe ta bushe da dariya tace ” Big sai a fito ko tunda dodon ya tafi.”
Fitowa kam yayi daga cikin kayan yayi sharkaf da zufa yana kallonta yace “Yarinyar nan ba ki da mutumci wallahi, ina cikin d’akin kuma shine zaki yarda ki biyewa waccen bunsurun.”
Tsaki yayi ya juya zai fita tace “To kuma aikin daka fara fa?”
Juyowa yayi ya kalleta yace “Allah ya kiyaye na jefa gugata bayan Labo ya cire tashi gugar, sai kuma wani lokacin yarinya.”
Juyawa yayi yaji tayi tsaki ta kuma cewa “D’an iska kawai, kawai ka ce ba zaka iya ba.”
Saida yasa takalminshi ya kalleta yace “Ke wai jakar ina ce d ba kya gajiya? Yanzu duk abinda ya faru kice baki gaji ba.”
Mik’ewa tayi tsaye ta rarumo zani ta d’aura a k’irji tace “Haihuwar Salma ce fa, ko ka manta ne, gadon juriya nayi.”
Wucewa yayi zai shiga d’akin da yake kwantawa mutan gidan suka saka shewa da habaici wai suna nuna ba komai amma kuma da wani abu a k’asa, d’an daudun nan kad’ai ya kalla ya malmala mishi wata ashar ya wuce ya barshi.
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
Bayan tafiyar Abbas Sameera ta samu Ammie lokacin Abba shima ya fita, nan ta fad’a mata abinda ke faruwa yar aikin data d’auka, Ammie ce ta kalleta da mamaki tace “Takwarata, kuma ke yanzu kin yarda ki taimaka mata? A gaskiya ni dai hankali na bai kwanta ba.”
Cikin rarrashi tace “Ammie, wallahi babu abinda zai faru da yardar Allah, kuma ma Ammie ai ba su suka aikata laifin ba, kinga ba zamu hukuntasu da laifin da iyayensu ne suka aikata ba.”
Ajiyar zuciya ta sauke ta kalleta tace “Shi ya amince ne?”
Da fara’a tace “Ammie munyi magana da shi kuma ya amince, kawai yace dai bai yarda taje ko kusa da d’akin shi bane bare kuma ciki.”
“To shikenan, Allah ya taimaka mana.” Saida ta kwanta kan k’afafun ta tace “Ameen Ammie na.”
Shafa bayanta ta fara yi tana fad’in “Ya kamata fa kisan girma kikeyi takwarata, shiyasa kullum mijinki ke k’orafin ni na lalataki kika raina shi.”
Sake gyara kwanciya tayi tace “To Ammie idan banyi ba wa zan ma, shekaru na d’auka babu soyayyar uwa a tare dani saita uba, shiyasa ma ban damu da Abba ba kamar yanda na damu dake, Ammie nayi rayuwar kad’aici da maraici wanda har yanzu idan na tuno na kanji ba dad’i, soyayyar uba goma d’aya take data mahaifiya k’waya d’aya tak.”
Hannu Ammie tasa ta juyo da fuskarta tuni hawaye sun fara mata zuba, goge mata yake tana fad’in “Nasan da haka takwarata, shiyasa ma har yanzu bana kallonki a matsayin wata babba, nasan kinyi kewar mahaifiya a kusa dake, kin rayu cikin mutanen da baki da wata alak’a ta jini dasu, amma yanzu ba gashi komai ya wuce ba kina tare da ni.”
Rumgume Ammie tayi sosai kamar tana bata nono, tana jin soyayyarta na sake shiga zuciyarta, sai dai har yanzu tana ji ina ma zata ga mahaifiyarta ido da ido ko na awa d’aya, da zata k’arar da lokacin wajen nuna mata irin yanda take son rayuwa da ita.
Sallamar su Raihan ce tasa ta tashi zaije tana kallonsu cikin kayan makarantarsu, Ameer ne ya taho da gudu ya fad’a da jikinta yana kuka wai shi ba zai je makaranta, kallonshi tayi tace “Haba dai Babana, da girmanka da komai ka ce ba zaka je makaranta ba, dubi fa kowa ya shirya kuma tafiya zasuyi , kamata yayi ace kaine ma shugaban tafiyar nan, ko ba kaso ka zama kamar Abba ne?”
Cikin kukan ya amsa da “Ina so.” Murmushi ta masa tace “Good man kenan, dan haka ka wuce gaba ka rigasu shiga gaban mota, kaji ko.”
Aida gudu ya juya ya bar d’akin, sai lokacin ta kalli Abdul da suke gaisawa da Ammie, suna had’a ido yayi k’asa tana gaisheta, amsawa tayi tare da cewa “Har kun gama shirin kenan?”
Da alkunya ya amsa da “Mun gama Ammie, amma kuma bamu ga Dady ba.”
Murmushi tayi tace “Sai dai kuyi hak’uri kam, amma yanzu haka dadynku na sararin samaniya akan hanyarshi ta zuwa Belgium.”
Raihan ce tace “Ammie Belgium fa, amma shine ko ya mana sallama.”
Raudat ce tace “Ai zai dawo gidan ya samemu, Allah ba zan mishi magana ba.”
Sameera ce tace “To sarauniyar masu wayon duk duniya, kuna bacci ya tafi, amma bai fita daga gidan ba saida yace na tabbatar na sumbaci dukanku a madadin shi.”
Khalifa sarkin surutu da sauri ya fad’o jikinta yace “Ni ne farkon da za’a farawa, dama ko a haihuwa nine farin cikinshi na farko.”
Tab’e baki Raihan tayi tace “Dallah malam matsa min daga nan, taya zaka zama farin cikinshi na farko bayan an haifeni kafin kai.”
Matsowa tayi kusan Sameera ta sunkuya tace “Ammie ni ce farko.”
Hararansu Sameera tayi tace “Ga Abdul babban amma saiku da kuka fi kowa son girma.”
Hannun Abdul ta kamo ta matso dashi kusanta, kunya ce ta rufe shi dan shi yanzu kallon suruka yake mata ba uwa kad’ai ba, haka ko ta dafe kumatunshi ta sumbata tare da shafa kanshi tace “Allah ya albarkace ku yarana.”
Cike da jin dad’in addu’ar ta yace “Ameen Ammie, mun gode da addu’ar ki gare mu.”
Jabeer ta kamo shima ta masa kafin Raihan da Khalifa da kuma sauran yaran, bye bye suka musu suka tafi har Khalifa na juyowa ya kalli Ammie yace “Yar tsohuwa naga sai kallona kikr yau ban kulaki ba ko, to zan siyo miki goro idan zan dawo.”