BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Kallonshi Alhaji yayi yace “Dan kana da mata da yara sai akace ba zaka k’ara aure ba? Ko kuma dan kai babu burin yin hakan a ranka sai kuma ubangiji ya barka haka? Duk kunbi kun d’orawa kanku rayuwar turawa saboda kawai kunsha boko kun k’oshi, Allah ya hore muku abinda zaku zauna da mace hud’u amma kuna mak’ale a mata d’aya d’aya, to ban lamunta , wannan karan k’addararka ta zo maka da sake k’ara aure bayan ka fara girma, kuma ta hanuna wannan k’addarar ta jefo auren naka, kayi na farko saboda uwarka, yanzu zakayi na biyu saboda ni ubanka, idan kuma ban isa ba na gani, wallahi ba kai ba har uwarku da kuka ga ina zubawa ido wannan karan sai mu samu matsala da ita akan auren nan.”
Lieutenant da gabanshi ke dukan uku uku yake takaicin musawa mahaifin nashi wanda sanadiyar haka yau gashi yana kallon fad’an shi da abune mai matuk’ar wuya ganin hakan tare da shi, cikin girmamawa yace “Dan Allah Abba kayi hak’uri ka gafarce ni, wallahi bana da tunanin bijirewa buk’atar ka, kawai yarinyar ce na duba, amma kayi hak’uri insha Allah ba zan baka kunya ba.”
Shiru Alhaji yayi ya kawar da kanshi suka ci gaba da tafiya, saida suka kusa daf da gidan ya juyo a nutse yace “Shin ka ma san yarinyar nan wa take so? Kasan waye ta jima tana dakon soyayyarshi a zuciyarta?”
Kai ya girgiza shi kuma yace “Kai ne, kai ne wanda take so, kai ne kad’ai mutumin da zata iya zaman aure dashi tayi farin ciki, da kunne na naji tana fad’in haka wanda maganar daga zuciyarta take fitowa, babba kayi hak’uri idan na takura ka, sannan ka min biyayya ta hanyar nuna wa yarinyar nan soyayya da gata, zan so ace ta manta da maraicinta, ku har yanzu baku san meye maraici ba, baku d’and’an d’acin dake cikin maraici ba dan haka ba zaku fahimta ba har sai ranar da kuka wayi gari kuka ga bama raye a doron duniya, amma ina baka tabbaci akan yarinyar nan zakayi alfaharin wannan had’in dana maka.” Jinjina kai yayi alamar gamsuwa a haka suka ci gaba da tafiya sannu sannu har suka iso gidan.
*Tunda* Jibril ya je mayanka bai dawo ba saida tik’ek’en sa wanda Huda ta zayyana masa kamaninshi, a babbar mota aka saka shi wacce samanta ke bud’e shi kuma yana gaba dan jagorantarsu, suna zuwa har k’ofar gidan ya samu yaro ya aika yace a kira Mari, ta so fitowa da Huda amma tana can yau ta samu kayan mak’ulashe ko takan uwar bata bi ba, tana fitowa ta ganshi suka sake ido hud’u hud’u, rumgume hannayenta tayi a k’irji ta kalli san dake bayansu ta kalle shi tace “Sai gashi bayan shekara bakwai mun sake had’uwa, bawan Allah mena maka a rayuwa daka tarwatsa min tawa rayuwar? Laifin me na aikata maka daka zab’i hukunta ni ta hanyar raba ni da iyaye na? Kuskuren mane aikata a kanka daka gwammaci ka rama ta hanyar yi min ciki na haifi yarinyar da ake kiranta da shegiya? Meyasa? Ko fa saninka banyi ba a waccen ranar, amma ka kasa tuna komai ka zalince ni sannan ka tafiyarka ka barni da abun kunya, kai wane irin marar imani ne?”
Tunda ta fara magana yayi k’asa da kanshi yana k’ok’arin b’oye hawayenshi, saida ta gama ya kalle ta yace “Kiyi hak’uri Ma…”
Bata bari ya k’arasa ba ta gaure shi da Mari a gaban mutanen dake jiranshi ya fad’a musu yanda zasuyi da san nan, ko dafe kunci baiyi ba bai kuma nuna abun ya dame shi ba, dan yasan ya cancanci fiye da haka ma a wurin ta, cikin shak’ewar muryar da tasha kuka tace “Kai har kana da bakin da zaka bud’a ka bani hak’uri? To bari kaji da kyau, wallahi ba son auren d’an uwanka nake ba, amma zan aure shi saboda kai sannan na shiga da ‘yata gidan ubanta, abinda zan fad’a maka kawai shine kada ka yarda wani ko wata ace za’a gorantawa ‘yata cewa ita agola ce ko shegiya, wallahi duk wanda ya fad’i haka saina tona maka asiri, wannan shine dama, ka b’ace daga k’ofar gidan nan.”
Zata wuce ya tare gabanta yace “Dan Allah Mari ki saurare ni.”
Kallon da take masa kamar zata ci namansa d’anye dan haka yace “Ki dake ni mana idan hakan zai saki ki huce laifin dana miki, amma ina rok’onki ki bani dama na fara cikawa ‘yata burinta ta hanyar yanka mata waccen sa a sake zana mata suna, ina so masu mata gorin ba’a yanka mata ragon suna ba su san ‘yar gata ce ita ma.”
Wani kallon mamaki ta masa tace “Gata? Yar gata fa kace? Shin kasan wahalar da nasha da ita kanta Huda?”
Had’e hannayenshi yayi yace “Dan Allah fa nace Mari, na rok’eki ki amince na faranta mata rai.”
Tab’e baki tayi tace “Ka amince da abinda na fad’a maka cewa ban yarda kowa ya zagar min ‘ya ba? Sannan ka yarda zan je da ita gidanku ba’a matsayin agola ba?”
Da sauri yace “Na amince Mari, babu ma wanda zai goranta mata.”
Sake tab’e baki tayi tace “Shikenan, sai kayi abinda ya dace.”
Juyawa tayi ta shiga ciki shi kuma yace yaran su d’an jira kad’an, yana rufe baki kuma sai kiran sallah la’asar, dan haka sukayi alwala suka shiga masallaci, ana idar da sallah yace akwai zanen suna na Huda wanda ba ayi ba a baya, nan fa aka sake rad’in suna kowa ya sake shaidawa ya bayar da kud’i aka siyo carton d’in alawa aka raba, wannan gabjejen San aka kayar aka yanka shi, daga nan shi kuma yace ya gama nashi burinshi yaga an zubar da jinin dama, nan fa nama aka dinga wadak’a da shi sai gashi har masu goranta mata sun manta suna wawasar nama ana sadaka, Iklima kam a tsakar gidan su habaici da zagi babu irin wanda bata aikawa matan gidan ba banda Mamar Husna, ana tsaka da haka motar da zata d’auki su Mari ta zo, ai kuwa Iklima tace k’afar ta k’afar Mari, tare suka d’auki hanya da Huda sai fatan sauka lafiya.
*Bayan* fitarsu Alhaji ba jimawa Ammar ya shigo gidan har falon Hajia, wannan karan Ummy ce zaune da yan biyunta sun sakata tsakiya, amma daga wacce faranti ke kan k’afafun ta tana ta gwaigwayar kankana ma zaka fahimta, Hamna na gashinshi ta zabura ta aje farantin zata haura d’akin su, da k’arfi Ummy ta jawota ta zaunar da ita tace “Haukan banza, sau nawa zan ce miki ke ba yarinya bace ki daina sarar gudun nan.”
Ganin yayi tsaye yana mata wani kallo yasa Ummy had’e rai tace “Kai kuma lafiya? Meye ka wani tsaya mana a gaba haka?”
Kallon Amna yayi yace “D’auki kisha.” Girgiza kai tayi alamar toh ta sunkuya ta d’auki farantin da yer uwarta ta aje tasa kankanar gaba ta fara sha ba dan ranta na so ba, dan ita ko warinta bata cika so ba amma haka ta ke sha, Ummy ce ta kalleta tace “Ke da baki shan kankana shine zaki sha ki takura kanki, mtsss wallahi abun haushi baya k’are muku.”
Kallon Ummy yayi ya kalli kankana dake bayanta sai k’ara b’oyewa take ya matso, hannu ya kai zai kama kunnenta Ummy ta buge hannun tana fad’in “Wallahi ubanka zan ci idan ka tab’a min ‘ya, wai kanka d’aya kuwa.”
Sake had’e rai yayi cikin jin zafin zagin data masa yace “Ki bari ki ga me zanyi, tarbiyar da kuka kasa mata ce zanyi mata.”
Da k’arfi tace “Tarbiyya? Kai tarbiyyar ce da kai da har zaka wa wani? Dallah malam fitar min anan wurin kafin ranka ya b’ace.”
K’asa yayi da hannunshi kamar zai kama kunnen Hamna hakan yasa Ummy yin k’asa da sauri da niyyar rik’e hannun, cikin azama ya saka d’aya hannu ta sama ya kama kunnenta ya murd’e, wata uwar k’ara ta saki a kunnen Ummy ta fashe da kuka tana k’amk’ame ta, k’ok’arin yakice hannun ta fara yi amma ina ta kasa, shi kuma Hamna data bud’e bakin nan yayi nasarar buga mata hannu dole tayi shiru ta rufe bakin da hannaye yana fad’in “Wallahi kashedi na k’arshe zan miki, idan kika yarda kika sake fita daga gidan nan babu hijabi sai na ci k’undun ubanki, kuma wallahi tun a inda na had’u dake zan fara bugaki har cikin gidan nan, tunda dai ba kya jin magana ke, munafuka kawai.”