BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

*SADAUKARWA GA*

‍‍‍ _*AHALI NA*_‍‍‍

*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`

_Bismillahir rahamanir rahim_

_24_

Aikin gama kam ya gama, rana ta farko daya fara sanin ‘ya mace a duniya kamar yanda ita ma shine na farko gareta, zaune yake bakin gadon yana bubbuga kanshi da hannayenshi yana so ya farka daga mummunan baccin da yake, amma ganin ya k’i tashi yasa ya mik’e da k’arfi tare da kaiwa bango naushi yana fad’in “Meyasa? Meya sameka Ammar? Me ka aikata? Tirr da kai.”

Fuskantar gadon yayi idonshi rintse baya son ganin Hamna a wannan halin, saida ya sauke numfashi mai k’arfi kafin ya bud’e ido a hankali da addua’r Allah yasa yagababu kowa kawai gizo ne ko mafarki, tarau ya sauke ido kanta tana jan numfashinta da k’yar sai matsawa take har tana neman fad’uwa daga kan gadon tana kuka, kallonshi ya kai kan ta’asar da yayi hakan yasa shi cabko wuyanshi ta baya da k’arfi ya sake rintse ido yace “Shiiit, Ammar alawadaranka, ashe dama d’an iska ne kai kamar yanda suke fad’a, meya kaika aikata wannan b’arnar?”

Hamna data sauka daga kan gadon ne ta rakub’e ta had’a kai da gwiwa tana ta k’ara dunk’ulewa cikin zanin gadon data janyo ta rufe jikinta sai k’ara sautin kukanta take, lallai yau ta koyi wasu darusa da dama na rayuwa, na farko ta fara jin *tsoronshi* ta yanda take jin ba zata sake shiga harkarshi ba, na biyu kuma ta *ji wata tsanarshi ta gauraya jini da tsokarta*, na uku kuma duk *abinda Allah ya hukunta* shine zai sameka ko baka so, domin kuwa saida Ummy tace mata ta rufe d’akin saboda ko bacci ya d’auketa tunda su suna aiki basu ga ranar gamawa ba, sannan har yer uwarta Amna saida tace me zaisa taje d’akin Ummy karatu bayan ga nasu d’akin, bata tunanin Abba ya dawo ya kuma buk’aci d’akin? Amma haka ta shareta ta taho, ashe wannan mummunar k’addarar ce ke bibiyarta, bak’ar ranar da d’an uwanta na jini zai mata fyad’e, ita kam tsakaninta dashi sai Allah isar mata, dan kuwa ba zata yafe masa ba har abada.

Kallonta yayi duk yanayin tashin hankali da rashin jin dad’i ya bayyana a tare dashi, kallon littafinta yayi na karatun wanda ya turmushe da kuma kankanar data zube, girgiza kanshi yayi yana tunanin ta ina ma zai fara rarrashinta? Da wane ido zai kalleta yace zai bata hak’uri? Me zai fad’a mata ta yarda dashi? Wane kallo mutanen gidan nan zasu mishi? Ya ma akayi ya zarce daga ya d’an mata horon da bai wuce sumbata ba? Sai kawai ya tsinci kanshi yana sukuwa akan ‘yar mutane yana hak’arta kamar rijiya, bayan kuma babu aure tsakaninsu, kai Ammar ya ma zakayi da yer uwarta ne wacce kayi niyyar aura? Me zata ji? Yer uwarta da suka fito ciki d’aya? Rashin samun madafa ya sashi sake kaiwa bango dukan tsiya wanda yasa har saida jini ya shake gabce mishi sanadiyar ciwon da yaji ranar, da saurin bala’i ya bud’e k’ofar d’akin ya fita dan hakan shine ma daidai a wurinshi, saida ya zo zai wuce ya kalli k’ofar Alhaji, ji yayi wasu hawaye na neman taho mishi na tausayin tsohon, mintuna nawa ne daya saurari addua’r shi, amma ace haka ta faru dashi, lallai wannan k’addara ce, dan ba dan Allah ya rubuta hakan zai faru ba da babu abinda zai fito dashi neman abincin ci, duba da yasha kwana da yunwa kuma baya damuwa, sannan ko da *11:00* na dare Hajia tasa an rufe mata k’ofar falon nan, amma yau sakamakon sabga yasa ba’a rufe ba har ya iya shigowa, sannan da farko yayi niyyar barin d’akin, amma addua’r Alhaji data tsayar dashi har tasa yaje d’akin Ummy, gashi yanzu ya aikata abinda baisan ina tashin hankalin zai tsaya ba, da sassarfa ya taka zai fita ba tare daya lura ba yayi karo da mutum, da sauri ya kalli wanda suka had’u ashe Ummy ce rik’e da jug na ruwa, wani kallo ta masa kamar zata cinyeshi tace “Kai kuma meye haka? Me kake yi anan a wannan lokacin?”

Kafeta yayi da ido kawai dan rashin gaskiya yasa yana tunanin kamar zata karanta a goshinshi abinda ya faru, shirun daya mata yasa taja dogon tsaki ta wuce ta barshi nan, da sauri shima ya fita ya koma b’angaren su ko k’ofar bai rufe ba ya wuce d’akin shi, yana shiga wanka ya shiga yayi na tsarki kafin ya tsaya gaban panpo yana sako mishi ruwa, ido rufe ruwan ke sauka yana hasko duk abinda ya wakana, “Tabbas nine na fara bud’e kankana, ni ta fara sani, ashe duk wayewar nan tata bata sa ta zubar da mutumcinta ba, ina ma ta hanyar aure hakan ta faru?”

*Ummy* na shiga d’akin ta tsaya turus saboda ganin bak’in abubuwa, babu zanin gado shinfid’e sai ma alamun jini-jini, farantin kankana tarwatse tare da kankanar, littafin karatu ya turmushe sai kuma pilow dake kan gadon suma duk a k’asa, tana cikin duba wannan abubuwan ne taji sautin kukan Hamna, saida ta sake kallon wurin da kyau tare da matsowa kad’ai ta ganta, ganin dunk’ule cikin zanin yasa Ummy sakin jug d’in ta k’arasa da gudu ta durk’ushe ta rik’ota tana fad’in “Subhanallahi, Hamna lafiya? Meya sameki haka? Meya faru dake? Lafiya k’alau na barki, meya faru?”

Hamna sake fad’awa tayi jikin Ummy ta sake fashewa da kuka sosai, gaban Ummy ne ya ninka fad’uwa tare da k’arfin halin cewa “Hamna dan Allah ki fad’a min, meya faru na ganki?”

Kuka kawai take ta kasa cewa komai tana tunanin ta fad’a ko tayi shiru, Ummy kuma data gama fahimtar meya faru hawaye ne suka taho mata ta k’ara k’amk’ame Hamna a k’irjinta tana fad’in “Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un, Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un, Hamna Ammar ne?”

Kukan data sake fashewa da shi ne yasa Ummy ma fashewa da kukan da k’arfi, d’ora bakinta tayi kan gashin Hamna har hawayenta na zuba saman kan tana fad’in “Hamna kiyi hak’uri, laifi na ne, laifina ne Hamna, kiyi hak’uri dan Allah, Ammar ya zamar min kamar dodo, bansan me nayi masa ba da yake son ganin ya d’ora min hawan jini, ba zan tsine masa bane kawai dan kar ya k’arasa zamar min tashin hankali.”

Kuka suka ci gaba da rerawa kafin daga bisani Ummy ta d’agota ta kalleta ta dafa kumatunta tace “Hamna kiyi hak’uri kiyi shiru kinji, bara na taimaka miki.”

Mik’ewa tayi ta shiga ban d’aki, heater ta kunna mata ruwa masu yawa kafin ta fito ta fara gyara d’akin, duk tana aikin nan tana zubar da hawaye na takaicin abinda Ammar yayi, tana tunanin abinda zai faru idan mutan gidan nan suka samu labari, da wane ido zata kalli mahaifinshi? Me zata fad’awa mahaifiyar Hamna da mahaifinta ma? Wane irin kallo zasu mata? Me zasu ce? Hajia fa? Babban tashin hankalin kenan Hajia? Da wannan tunanin ta gama kimtsa d’akin taje tasa ma k’ofar d’akin makulli ta rufe sannan ta kamata suka shiga ban d’aki, saida ta nuna mata ta shiga cikin bahon wankan suka lura da jinin dake bin k’afafun ta, a marairaice Ummy ta kalleta tace “Ki shiga kiyi wankan, idan kika fito saina dubaki watak’ila kinyi k’ari ne.”

Shiga tayi ita kuma ta fito ta d’auke zanin gadon da tattare kayan jikinta, duk da basu yage ba amma sunji matsa, ta jima tana jiran fitowarta kafin ta fito ta zaunar da ita, wani zama tayi kamar akan wuta saboda zafin da take ji zaman ma tayi ne dan Ummy ce ta zaunar da ita, kallon kumburarrin idonta Ummy tayi ta dafa kafad’ar ta tace “Hamna zan iya rok’onki wata alfarma? Dan Allah? ”

Cikin lumshe ido ta kalleta tana cije leb’en k’asa ta jinjina mata kai kawai alamar eh, nisawa tayi tare da kallonta a tsanake tace “Hamna, bansan taya zan fara baki hak’uri akan abinda ya faru ba? Haka bansan meya had’a ku ba har haka ta faru? Amma dai Hamna aikin gama ya riga daya gama, muyi tunanin abinda zai biyo baya Hamna idan abu nan ya fito fili, Hamna, shin kina son zumuncin dake tsakanin mahaifinki da mahaifinshi ya wargaje? Ko kuma zaki so mutumcin dake tsakani na da mahaifiyarku ya tarwatse? Ko kuma zaki so ganin Hajia cikin wani mawuyacin hali sakamakon abinda ya faru dake?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected