BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Duk iyayen na zaune akan teburin cin abinci suna ci suna hira, kuma hakan ya faru ne saboda Alhaji na wurin, ba dan haka ba babu wanda ya isa ya cika Hajia da surutu alhalin tana cin abinci, Amar ne ya shigo tare da Ammar kamar wasu zakuna, Amar ne yayi sallama suka nufi kan teburin yana gaishe da mutanen wurin, Ammar na zuwa hannu ya zura gaban Hajia ya d’auki robar ruwan da take sha ya kifa bakinshi yasha sosai, kowa kallonshi yake har da ita kanta Hajiar, saida ya sauke robar ya kalli kowa dake wurin shima yana murmushi, lokacin da kallonshi ya sauka kan Zeituna wacce kanta ke k’asa ne ya fad’ad’a murmushin shi yace “Ina wuni.”
Da sauri ta d’ago kanta lokaci d’aya kuma ta mayar dashi k’asa dan bata zaton da ita yake, duk wanda ke gurin kallonshi sukayi da matuk’ar mamaki, *yau Ammar ne ke gaishe da wani?* gaisuwar ma ga wacce ba’a tsammanin zai iya gaisheta, ganin irin kallon da suke mishi yasa ya sake kallon Zeituna yace ” Dake fa nake, *uwa*.”
Sake d’agowa tayi cike da tsoron abinda zai iya fad’a mata, suna had’a ido bata san lokacinda tace “Yah Ammar ina wuni.”
Murmushi ya mata yace “A’a uwa, ki kira ni Ammar kawai, ko kuma ki kirani da *d’an ki*, tunda ke ma uwata ce.”
Wata irin dariyar rainin hankali Hajia ta bushe da ita har da gaggab’awa take, wani kallo Ammar ya mata kafin ya kalli Ummy yace “Ummy ina amaryata take? Ina so zamuyi magana ne.”
Hararan sama da k’asa ta masa taja dogon tsaki, mayar da kallonshi yayi kan Zeituna yace “uwa dan Allah zaki iya fad’a min inda take?”
Zeituna da ita dai al’amarin d’an mijin nata ke tsorata ta da sauri tace “Tana d’akin…” Da sauri Ummy ta katseta da cewa “A’a Zeituna, rabu dashi kawai, uwar me zai bata yanzun?”
Tab’e baki yayi ya kalli Zeituna yace “Uwa zan iya baki sak’o wurinta?”
Kamar sakarai haka take kallonshi baki bud’e ta jinjina masa kai alamar eh, da hannu ya mata alama yace ” Zo to, sirri zamuyi.”
Mik’ewa tayi tsaye zata tafi lieutenant ya daka mata wata harara yace “Wai ke me yake damunki ne? Kanki d’aya kuwa ko kuma ke ma irinshi ce?”
Alhaji ne yace “Babba, ka barta dan Allah.”
Murmushi Ammar yayi yace “Abba kwantar da hankalinka mana, babu inda zan tafi maka da matarka, nima fa uwata ce.”
Wata harara lieutenant ya wurga masa wanda tasa Ammar kwaso shoki, har zai sauketa akan idon lieutenant sai kuma ya juya ya kalli Amar dake gefenshi ya watsa mishi ita a fuska, Zeituna na zuwa kusa dashi saida ya k’ara matsawa kusa da ita ya juya baya suka bawa mutanen baya kafin ya sassauta murya yace “Uwa ki samu Amna a d’aki ki fad’a mata ta baki kayanta ki kawo min za’a d’auki awonta ne (mesure).”
Jin abinda ya fad’a yasa Zeituna sauke ajiyar zuciya ta kalleshi tace “Toh.” Da sauri ta juya ta nufi d’akin Ummy inda amaren suke, tana shiga ta same su tare da wasu daga cikin k’awayensu, gabanta ta tsaya tace “Amna, sak’o daga angonki wai ki bado kayanki za’a d’auki awonki ne.”
Kallonta tayi tace “Yah Ammar? D’inkin zai min?”
Da murmushi ta amsa mata da “Ni ma ban sani ba, tashi ki d’auko kawai.”
Mik’ewa Amna tayi ta fito Zeituna na biye da ita a baya, d’auko mata kayan tayi ta bata ita ma ta juyo dan kawo masa, tana zuwa ta same shi tsaye kusan Hajia sai kallonta yake, ita kuma ta had’e fuska sai hararenshi take, Amar dai dariya yake musu har yace “Dan Allah Hajia ki ci abincinki kar ki biye masa, so fa kawai yake ki biye masa kuyi fad’a.”
Tab’e baki tayi tace “To ai yanzu ni ya daina bani wahala shalele, ka rabu dashi zaiyi ya bari ne inya gaji.”
Da wani murmushi a fuskarshi yace “Da gaske Hajia? To zan gani.”
Zeituna na bashi kayan a leda ya karb’a ya matse ledar a hammata, ba zato ba tsammani ya daddage ya samu hak’ark’arin Hajia ya danna mata cakulkuli, ( Hajia mutan makka), ai wata zabura Hajia tayi daga kan kujerar tare da sakin ihu har cokalin hannunta ya fad’i abincin cikin cokalin ya zube, haba wa ai sai Amar ya fashe da dariya tare da taimakon Alhaji da Husseina, Ummy kam da Zeinabu da Soueiba duk rufe bakinsu sukayi suna toshe dariyarsu, Ammar da tuni ya zura a guje shima dariyar yake, yana kaiwa bakin k’ofar fita daga gidan ya had’e da Hamna ta shigo tare da k’awar ta wacce ya amshi lambarta, tsayawa yayi suna kallon juna da ita b’angare d’aya kuma yana kallon Hamna da wutsiyar ido, washe baki tayi tace “Lah mai kyau, sai ganshi dai yau mun had’u, dama kuma ina son ganinka dan naji dalili da yasa baka kirani ba.”
Yanda ta kafeshi da ido alamar tana jiran amsa yasa yayi murmushi ya kalli Hamna yace ” Hum! Kinga ranar da kika bani lambar nan, saboda ina tuk’i daga na bawa k’awarki ta saka min sunanki akai, sai kawai tace min wai ta goge, to har yanzu ina so na sani ne gogewa lambar tayi ko kuma gogeta akayi, shine abinda na kasa fahimta.”
Wani marairaicewa yayi yace “Dan Allah budurwata ki tayani tambayarta ta fad’a min, na shiga damuwa sosai saboda rashin kiranki da banyi ba, da zaran na kwanta bacci ke nake gani a idona, idan ina wanka ma ke nake ji kamar kina goga min bay…”
Hamna ce ta fizgi hannunta tana fad’in “Dallah *Ami* wuce mu tafi, k’arshen marar kunya ne wannan yanzu saiya fad’a mana abinda kanmu ba zai iya d’auka ba.”
Juyowa yayi ya bita da kallo yace “Kunya? Ai laifinku ne inma bana da kunyar, tunda sanda ake rabonta ina bacci kuma babu wanda ya tasheni.”
Tsaki Hamna tayi wanda yasa ya juya da hanzari ya kamo k’aramin kallinta, duk da ta tsorata da yanda ya fizgota ya kuma kalleta da jajayen idonshi hakan bai hanata cewa ba “Dallah malam sake ni, ni yanzu sam bana son had’a hanya…”
Bai bata damar k’arasawa ba ya kama dogon hancinta yaja sosai, siririyar k’ara ta saki take idonta suka kawo ruwa saboda zafin da taji, k’ank’ance idonshi yayi yace “Na sake jin tsaki ya fito daga bakinki zuwa kaina wallahi zaki rasa hak’oranki.”
Sakinta yayi ya juya zai fita Ami tace “Mai kyau.”
Tsayawa yayi ya juyo a hankali ya kalleta, matsowa tayi tace “Nace ka kawo wayar taka saina saka maka lambar ko?”
Saida ya kalli Hamna yace “Ki barshi kawai, wacce ta goge lambar uta zata sake bani ita da kanta.”
Yana fad’a ya juya ya fita ita kuma ta kalli Hamna tace “Dan Allah besty ki bashi lambar, wai ko dai ba kya so na auri yayanki ne?”
Dafe goshi Hamna tayi ta mata kallon sakarai tace “Ki farka idan ma bacci kike, nan da kwana uku za’a d’aura aurenshi da Amna.”
“Me?” Ta fad’a da d’an k’arfi, kallon k’ofar daya fita tayi tace “Amma kuma alamunsa bai nuna haka ba.”
“Shi wani irin mutum ne da ba’a gane gabanshi da bayanshi, k’ok’arin sanin asalin Ammar zai iya tarwatsa miki k’wak’walwa, dan haka ki fita a harkarshi kafin ya fad’a miki abinda zaisa kiyi nadamar sani na a rayuwa, dan ko kad’an bashi da tabbas.” Jinjina kai kawai tayi suka shiga ciki.
*Da asuba*…
*Alhamdulillah*
09/09/2020 à 17:58 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BADAK’ALA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_