BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Har tsakiyar mutanen da take zauna ya ja hannunta inda hankalin kowa ya koma kansu, janta kawai yake ita kuma tambayarshi take ina zai kaita lafiya? Saida ya kaita kusan d’akin mai gadi ya tsaya ya saki hannunta, rik’e k’ugu yayi da duka hannayenshi yana kallon fuskarta kamar ba gobe, ajiyar zuciya ya sauke mai k’arfin gaske.

Cikin wata sanyayyar murya amma sautin ta zai nuna maka babu wasa a cikinta kuma mamallakin muryar zai iya yin komai a yanzun yace “…

*Alhamdulillah*
14/10/2020 à 00:58 – Ummulkhairi: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*BADAK’ALA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_

*SADAUKARWA GA*

‍‍‍ _*AHALI NA*_‍‍‍

✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ ️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_63_

“Ummy, da gaske wai Shureim d’ana ne?”

A firgice ta kalleshi yayin da taji har ruwan jikinta na neman tsayawa, yanda ta zaro ido zai nuna maka bata da gaskiya, gudun kar ya fahimta sai tayi saurin b’atar da firgicin ta jawo mamaki ta dasa a fuskarta tace “Ammar, wace irin magana ce wannan? Wane Shureim d’in?”

Da hannu ya mata alamar ya isa haka tare da cewa “Ummy, kin sani na sani abinda ya faru, idan zan iya kawo miki hujojji na sai mu kwana anan ban gama ba, tun waccen lokacin ma nayi shiru ne saboda gudun b’acin ranki, Dan Allah Ummy inhar gaskiya ne abinda naji ki fad’a min.”

Cikin fad’a tace “Ammar wace maganar banza ce wannan? Ya zaka tasa ni a gaba kana tambayata wai Shureim d’anka ne? Zargina kake da cin amanar mahaifinka ko me? Ni sam ban ma fahimci me kake nufi ba.”

Matsawa yayi daf da ita murya k’asa k’asa yace “Ummy ba haka nake nufi ba, Shureim an ce d’ana ne dana haifa tare da Hamna, shine nake so naji gaskiyar.”

Cikin b’acin rai da d’aga murya ta rintse ido tace “Ammar bana son maganar banza, uwarka ce ya zaka sani gaba kana min wannan tambayar rashin mutumcin? Fad’a min wane d’an iskan ne yake son shiga tsakani na da kai da har ya fad’a maka wannan banzan shirmen?”

Cikin fitar hayyaci da b’acin rai da yanayin da shi kanshi baisan yayi magana dashi ba ya d’aga murya sama da ta ta yana fad’in “Ummy babu wani dake son shiga tsakani na dake, magana ce ta fito kuma ina so na sani nima, a matsayi na na d’anki ina da hakk’in da zan san haka.”

Saida ya dasa aya ya iya jiyo sautin muryarsa can sama, dafe kanshi yayi da hannu biyu yana d’an murzashi a hankali, kallonta yayi ya rik’o hannayenta duka buyu yasa idonshi cikin nata yayin da take mishi kallon mamaki yace “Ummy ki daure ki fad’a min mana, da gaske d’ana ne ko kuma k’arya aka fad’a?”

Cikin zubo da hawayen da suke nuna ta k’are min ta kafe shi da ido tace “Ammar waya fad’a maka maganar nan? Wane d’an banzan ne?”

Kamar zai fashe d a kula yace “Ummy abinda nake so naji daban, abinda ke ma kike so kiji daban, amsar tana da sauk’i fa Ummy idan kikayi niyyar fad’a min, kawai zaki ce min eh ne ko kuma a’a.”

K’yabta ido tayi tana kallon gefenshi, jinjina kai yayi yace “Zan tabbatarwa kaina.”

Ko da ya fad’a ya wuce da k’arfi ya tunkari falon Hajia, da gudu gudu ta bi bayanshi tana fad’in “Ammar ina zaka je? Me kake shirin yi ne wai? Ammar…”

Bai tsaya ba har saida ya shige falon, shigarsu yayi daidai da fitowar Hajia daga d’akin tare da duk yan kuci-kucin yaran suna ta mata shirme, da sauri ya tunkareta inda ya ga Shureim, hannunshi ya kama ya juya zai fita dashi Ummy ta rik’e hannun Shureim ita ma, juyowa yayi yace “Ummy dan Allah sake shi.”

Matsowa tayi kusanshi tace “Ammar baka da hankali ne wai? So kake ka min terere cikin mutane? Ina zaka kai shi?”

Gyara tsayuwa yayi yace “Asibiti zamu je.”

Ko da taji yace asibiti tasan me zaiyi acan, sunkuyar da kai tayi k’asa sai Hajia data matso kusansu tana kallon kowane tace “Ku kuma lafiya? Meya faru ne haka?”

Kallon Hajia yayi yace “Hajia, Shureimmm…”

Yanda Ummy tayi saurin rufe masa baki yasa shi jan k’arshen sunan, kallonta Hajia tayi ta fahimci bata so taji, sai kawai ta kama hannun Ummyn da Ammar ta tura su d’akinta, Shureim ta kama hannunshi shima suka shiga ta mayar da k’ofar ta rufe, zaune tayi kan gado ta kallesu ta nuna musu kujerar dake d’akin mai kama data gwal tace “Ku zauna dan Allah.”

Ummy na kallon Ammar ta tsoma mazaunanta kamar tace wayyo ita wayyo kanta, a nutse ta kallesu ta tattara hankalinta gaba d’aya kansu tace “Me yake faruwa Sa’ada?”

Cikin in’ina tace “Hha.jia, ba kommai..hajia.”

Murmushi tayi ta kalli Ammar tace “Ammar lafiya? Me yake faruwa da kake d’aga murya fiye data mahaifiyarka?”

Ummy ya kalla ya sunkuyar da kai yace “Kiyi hak’uri Ummy ki yafe min, wallahi bansan na d’aga murya fiye da taki ba, kiyi hak’uri dan Allah.”

Dan motsa kanta tayi wanda yake nuna tace ba komai, Hajia ya kalla yace “Hajia, in baki manta ba na fad’a miki abinda ya faru tsakani na da Hamna shekaru kusan biyar kenan.”

Sororo Ummy ta kalle shi da wani fitinannan mamaki, ya fad’a mata? Yaushe akayi haka bata sani ba? Kuma shine Hajia bata nuna mata ta sani ba? Tana kallon bakinshi taji yace “Shine yanzu aka fad’a min Shureim d’ana ne, Hamna ce ta haife shi, kuma ina tambayar Ummy amma ta k’i fad’a min, Hajia ina so na sani d’ana ne ko kuwa.”

Hajia ma mamaki ne ya bayyana a fuskarta, kallon Ummy take tace “Sa’ada.”

D’ago kai tayi ta kalleta, d’orawa tayi da “Da gaske ne abind yake fad’a?”

Cikin sanyin jiki tayi shiru ta kasa cewa komai, ba zata yarda ta sake yin k’arya ba, tunda gashi wacce tati shekaru ma yau ta fito, sai dai kuma ba zata iya amsa kai tsaye da eh ba, ganin wannan shirun na ta yasa Ammar kallonta da mamaki yace “Ummy me yasa kika yi haka?”

Kallonshi tayi saita sake yin k’asa da kanta ta fara zubar da hawaye, girgiza kai yayi kamar zai yi kukan shima na tausayin mahaifiyarshi yace “Ummy me yasa kika aikata haka? Dama har soyayyar da kike min ta kai wannan matakin?”

Fashewa ta sake yi da kuka sai kawai yace “Ummy in kinyi hakane saboda ki kare mutumci na dana Hamna, ai da fad’a min kikayi saina tayaki kare wa har zuwa lokacin da kike so kowa ya ji, idan kuma kinyi ne saboda gudun abun kunya da kallon da mutane zasu mana, Ummy ai naga ba akai na aka fara abun kunya ba, a gidan nan bani ne farkon daya fara aikata irin wannan laifin ba, Ummy ina kika kai tonton Labaran? naga shima ba da aure aka same shi ba kuma yana rayuwarshi hankali kwance, hasalima ba tare daya tab’a ganin mahaifinshi ya taka wani babban matsayi na rayuwa.”

Cikin nuna mata da hannu ya ci gaba da fad’in “Sannan ki dubi Huda, gata nan tana rayuwa cikin dangin mahaifinta ba tare da tsangwamar kowa ba, haka ma Junaid, rayuwarsa yake yi bai damu ba, kuma babu wanda yake iya d’aga ido ya kalleshi ya fad’a masa hanyar da aka same shi, Ummy sai ni ne dan na aje d’an gaba da fatiya za’a min zund’e da kinibibi, Ummy hakan ma ai tayar da lissafi ne yayi, kinga kenan zai zamana a kowane d’aki akwai shege.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected