BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Wani irin zabura da taji zuciyarta tayi yasa ta d’an dafe k’irjin ta ta rintse ido, cije hak’oranta tayi a ranta tace “Shikenan Hamna kinja min masifa ina zamana, da nasan shi zai nemeki wallahi da ban yarda da abinda kika fad’a min ba, ohh ni, *tawa ta same ni*.”
Wani tsinannen rank’washi (k’ozo) ne daya sakar mata a kai har saida taji jinin al’adarta ya bulbulo da k’arfi, cikin d’aga murya yace “Ba dake nake magana ba, ‘yar banza kai mai zubin mage, kina ji ina magana zaki min shiru.” Dafe kai tayi ta fashe da kuka bilhakk’i tana fad’in “To yah Ammar ai…”
Shirun da tayi yasa yace ” Ai me? Fad’i ina jinki ko na cire miki hanci yanzun nan.”
Cikin kukan tare da d’aga murya dan ta samu mai kawo mata agaji tace “Ni ce fa.”
Sunkuyawa yayi ya lek’a fuskarta hakan kuma yasa har saida numfashinsu ya gauraya, dayake ta gama wanke bakinta ne ta fito kuma ta d’auki turaren baki mai fitar da k’amshin ayaba yasa kamar ya cabki bakinta ya tsotsa, ita kuma d’an kawar da kanta tayi gefe, cikin wata irin murya yace “Ke ce kankana kike nufi?”
D’aga kai tayi da sauri alamar eh, jinjina kai yayi dake nufin ok zaki sha mamaki, mik’ewa yayi daga sunkuyon yasa hannu ya fara cire d’amarar k’ugunshi (bel, ceinture), a matuk’ar firgice ta kalleshi dan ganin me yale shirin yi, yana zage shi gaba d’aya ta zabura ta mik’e zata zuba a guje, hannunta ya rik’o tare da wurgata kan gadon ta fad’a kwaram, a lokacin ne kuma idonshi suka sauka kan jinin daya d’an fara b’ata zanin gadon, dan ko audigarta bata saka ba ta tsaya shafa mana, wani tarrr yayi da idonshi ya nuna mata wurin da yatsa yace
“Ita sarauniyar shan kankanar nasan dai aman ruwa take♀️, ke kuma kenan na jini kike?”
Girgiza kai tayi ba tare data daina kukan nan ba, sake dungure mata kai yayi yace “Dan ubanki ki min shiru, magana ce fa kawai muke ban kai ga dukanki ba.”
Tsaf ta had’iye kukan tana wik’i-wik’i da ido, d’orawa yayi da “Amna ni k’aramin yaro ne?”
Kai ta girgiza mishi da haka yace “To meyasa zakiyi tunanin raina min hankali? Shin kinsan tayaya d’azu nasan cewa kina fashin sallah?”
Ita dai da kai kawai take amsa mishi, ci gaba da cewa yayi “Shine har zaki nuna min kanki a matsayin kankana, kenan ni sakarai ne mahaukaci? Haka ranar ma tayi shiga irin taki taje min dan na bata wayarta, shine yanzu ma ta fita daga gidan da niyyar idan wani ya tambayeta kice ita ce anan ke kuma a can.”
D’aga belt d’in yayi da niyyar tsorata ta kawai, amma Amna da tsoro ya mata waya sai tayi wuf da Ammar ta rirrik’e rigarshi ta d’ora kanta a k’irjin shi tana fad’in “Dan Allah yah Ammar kayi hak’uri.”
_Ai ko malam ko uba zai dakeka kayi wuf da shi to ka gama dasu aradu, bare wani Ammar, nifa wannan karan bana yinka._
Sanyin da jikinshi yayi yasa shi sakin belt d’in bai shirya ba, lumshe ido yayi saboda tula tulan nonuwanta da suka zauna daram kan k’irjin shi, take yaji daga k’asa anyi wani ziiiiiii da yasa shi cewa “Ya salam.”
Ba tare daya bud’a ido ba cikin kasalalliyar murya yace “Amna ya kike so dani? Na mutu?”
Jin wata tattausan murya da bata tab’a ji ba yasa ta d’ago kanta, da sauri ta matsa baya ta saki rigarshi a d’an tsora ce, k’asa tayi da kanta cikin muryar kukan shagwab’a tace “Dan Allah yah Ammar kayi hak’uri karka dake ni, wallahi ba laifi na bane, Hamna ce tace nayi inba haka ba wai saita ja min matsala wajen Hajia, kuma ni nasan zata iya saboda tana yin kamar ni wani lokacin tayi abu.”
D’ago kai tayi ta kalleshi, duk da wani sabon yanayi ta gani a tare dashi, ya wani saki ido dabaki yana kallonta kamar ya fizgota jikinshi amma haka ta daure ta sake marairaicewa tace “Kayi hak’uri dan Allah, ba zan sake ba.”
Belt d’in shi ya nuna mata da ido yace “Mik’o min.”
Da sauri ta d’auka amma da zata mik’a mishi saida ta ja baya, karb’a yayi tana kallo harya mayar a k’ugunshi, cikin amon muryar data kasa fahimta yace “Ai nasan inda take, zanje can na sameta na yanka mata kazar wahala sannan na d’auko ta.”
Juyawa yayi da sauri harya bud’e k’ofa kuma ya juyo ya kalleta yace “Wallahi na bada baya kika kuskura kika kira kankana kika fad’a mata ina zuwa, hummm.”
Saida ya gyara tsayuwa yace “Kinsan me zan miki?” A hankali ta girgiza kai, ba yanayin wasa a fuskarshi yace “Wallahi zaune zanyi na b’ata lokaci wajen cire miki duk sinadaran dake jikinki, kin gane?”
D’aga kai tayi kawai almar eh amma ba tare data fahimci sinadaren da yake nufi ba, yana fita ta sauke ajiyar zuciya tace “Yanzu da shine ake nufin nayi rayuwar aure? Amma tayaya?”
Yana fita baibi ta kan Hajia ba ya fice daga gidan ya nufi hotel d’in dan d’aukar Hamna…
*Bébé Abdul latif ba lafiya, addu’arku masoya*
17/06/2020 à 11:45 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BADAK’ALA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
_*AHALI NA*_
*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`
_Bismillahir rahamanir rahim_
_18_
“Ni sunana Alhaji Suleymane Gaga, wannan kuma babban d’ana kenan mai sunan mahaifina, *Hassan*, amma ina kiranshi da babba, a gidana ‘yer d’an uwanka Zeituna take aiki, kuma mun zo ne akan maganarta yanzu haka.”
Kallonsu yayi dukansu kafin yace “Alhaji kace manyan bak’i ne ku? Ai duk garin nan babu wanda baisan da zamanku ba, Gaga, Gaga, ai suna ne daya zaga ko ina a fad’in garin nan dama kewayenshi, sai dai kuma kun saka zuciyata cikin rud’u jin kunce kun zo akan maganar Zeituna, dan Allah idan laifi tayi ku dubi Allah ku yafe mana, karku ce zakuyi shara’a damu ko kuma ku rufe ni, ita da tayi laifin can ku hukuntata saboda yar banzar yarinya ce bata jin magana.”
Lieutenant da bai fahimci komai ba kallon mamaki yake wa tsohon (dan kuwa ba zaka kirashi da dattijo ba), ance yar d’an uwanka, amma ka ce ita a hukunta ta kai a rabu da ka, to wane irin rik’o kake wa yarinyar? Alhaji ne yayi murmushi wanda shi jin haka bai dame shi ba idan aka kwatanta da abinda yake shirin aikatawa, cikin lumana yace “Ko d’aya, babu laifin data aikata, mun dai zo neman aurenta ne idan har za’a bamu.”
Zabura yayi yana fad’in “Me? Aurenta? Zeitunar? Ku kuwa me kuka gani a jikinta da har zaku zo neman aurenta alhalin kuna manyan mutane haka kuma masu kud’i, wai ko dai ba Gagan da nake ji ana fad’a ba har a redio mai masana’antu da dama?”
Wani murmushin dattako yayi yace “Ni ne da kaina, idan kuma kana son k’arin haske saina maka dalla dalla yanda zaka fahimta.”
Shi fa a saninshi yayanshi duk masu mulki da iko ne, ni kam ina zance ya min dalla dalla nasan ko da sojan cikinsu zai had’a ni, dan haka kawu Mamu yace “A’a Alhaji, ina dai mamaki ne, amma to wa yake son Zeituna da har ka zo neman mishi aurenta?”
Jim Alhaji yayi ya d’an sauke wata sanyayyar ajiyar zuciya ya kalli lieutenant dake kallon bakin Alhaji yaji wa zai nemawa auren wannan k’azamar yarinyar, kallon kawu Mamu Alhaji yayi ya nuna lieutenant yace ” *babban d’ana* Hassan.”