BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Amna ce tayi k’asa da kanta yayin da Hamna kuma ta zabga mishi harara ta d’auke kanta, Ammar kam kawar da idonshi yayi daga kallonsu saboda ganinsu kamar ‘ya’yan gwarawa, kowace da d’aurin k’irji hallitarsu ta fito fili, ta bayan Amna ya bi ya wuce yana kallon Hamna dake masa wani kallon iya shege, tun kafin ya k’arasa Hadiza ta aje masa kujera tana fad’in “Ammar ina ka shiga? Sun ce kai ka kawosu amma shiru baka shigo ba.”

Sam babu fara’a a fuskarshi ya zauna akan labb’anshi ya amsa da “Masallaci na tafi Tanti.”

Da fara’a sosai tace “Haba shiyasa, to anyi sallah lafiya?”

Ciki ciki ya amsa da “Lafiya lau.” Kallonshi Tanti tayi tana murmushi a zuciyarta tana ayyanawa yau ‘yan mulkin ne akan shi shiyasa ko gaisheta ya kasa yi, kallonsu Amna tayi da har yanzu suka kasa sulhunta kansu, girgiza kai tayi tace “Auta, ki barta tayi sai kiyi kinji, ki zo ki kawowa yayanku ruwa yasha kya samu lada ma.”

Da sauri Hamna ta kalli Hadiza Amna ita kuma turo baki tayi ta sakar mata bokitin tana hararanta, cikin sand’a take takowa kamar wata marar gaskiya saboda ganin yanda Ammar ya had’e rai kamar hadarin gabas, cikin tsoron kar ya daketa ta samu ta shige d’akin ta d’auko hijab ta saka ta fito, ruwa ta d’auko mishi ta zuba ta bashi a lokacin da Hadiza ke tambayarshi meyasa bai tsaya d’aurin auren babban shi ba? Saida ya karb’i ruwan ya d’an kurb’a ya kalli Amna da jajayen ido yace “Wuce d’aki.”

Kallonshi tayi kamar zatayi kuka cikin muryar tsoro tace “Yah Ammar..dama…alwala zanyi kafin ta fito.”

Sake wurgo mata idonshi yayi wanda yasa gabanta fad’uwa, dan a yanda suka sani ko gaban mahaifiyarsu ta kama saiya kasheka da mari har ma ya d’auki madaki, ajiyar zuciya ta sauke mai sautin gaske saboda alamar daya mata da ido ta wuce, da sauri ta nufi wajen buta ta zuwa ruwa lokacin Hamna ta shiga wanka, bai sake tankawa ba har saida ya ga shigar Amna d’aki kafin ya kalli Hadiza dake kwashe abinci a kwanuka ya tab’e baki yace “Me yasa zanje d’aurin auren?”

Juyowa tayi ta kalleshi ita har ta manta ma data tambayeshi, tun yana k’aramin yaro take k’aunar shi har zuciyarta, ta sanshi tasan halinshi fiye da uwar data haifeshi, hakan yasa bata damu ba saima murmushi da tayi tace “Saboda mahaifinka ne mana, kuma zaiyi farin cikin ganinka a wurin a kusa da shi.”

Murmushin rainin hankali yayi tare da kallon farfajiyar gidan yace “Ba zan iya wannan abun kunyar ba, tsofai-tsofai da kai kayi wani wai aure, auren ma ba da babbar mace ba ko wata bazawara, yarinya mai k’ananun shekaru, ko ni dake d’ansa wannan yarinyar ta min kad’an na aureta wallahi bare kuma shi.”

Wani wawan tsaki yayi alamun dai abun ya dameshi sosai, banda dariya ba abinda Hadiza keyi kafin tace “Yaron kirki kenan, amma me yasa kake ganin ta maka kad’an?”

Sam babu alamar wasa ko kunya yace “Saboda ba zata iya d’aukata ba, zata iya mutuwa tun kafin aje ko ina, sannan ni banga albarkatun dake jikinta ba wanda zasu iya d’ebewa mutum kewa.”

Murje ido Hadiza tayi ta nuna abun bai wani dameta ba dan tasan halin katob’aran yaronta tace “To dama wacece zata iya da kai yarona? Ai sai yar baiwa, amma fa duk da haka ita yarinyar ta dace da mahaifinku, tunda kaga kai sabon jini ne ka mata yawa, shi kuma an kwana biyu zai iya tafiya da ita yanda ya dace.”

Cike da jin an fasa mishi kai yayi wani shak’iyin murmushi yace “Hmm; shi ma fa da sauranshi, dan yanzu haka zai iya samo mana cikakken k’ane.”

Kafin tayi magana Hamna ta fito daga wanka, har tayi alwala bakin panpo ta basu sake magana ba, saida ta zo daf dashi zata wuce ta gabanshi dan hanyar da zata iya sadaka da d’akin ce kawai yace “Tanti ai duk wacce na kwanta da ita na tashi ita ma kuma ta mik’e da k’afafunta, to wannan ita ce daidai dani saboda ni jaruma nake so ba raguwa ba.”

Da k’arfi Hamna ta kalleshi amma kash kamar ma baisan da tsayuwarta a wurin ba, cikin murmushi Hadiza tace “Zaka sameta mai jarumta yaro na, zanyi k’ok’arin ganin haka ta faru ko saboda jin dad’in ka.”

Juyawa tayi ta kalli mahaifiyar tasu dake ta harkar gabanta, sake juyowa tayi ta kalle shi tayi k’wafa ta wuce, zata shiga ciki taji ya sake cewa”Kankana.”

Cak ta tsaya ta juyo tana aika mishi wani mugun kallo, kallonta yayi ya gyara zama tare da shafar gemunshi yana dariyar iskanci ya kashe mata ido d’aya yace “…

*Alhamdulillah Allah*
09/09/2020 à 17:58 – Ummulkhairi: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*BADAK’ALA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_

*SADAUKARWA GA*

‍‍‍ _*AHALI NA*_‍‍‍

*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`

_Bismillahir rahamanir rahim_

_26_

Kallonta yayi ya gyara zama tare da shafar gemunshi yana dariyar iskanci ya kashe mata ido d’aya yace “Fita zanyi yanzu, zaki sha kankana ne na taho miki da ita?”

Sama da k’asa ta harareshi taja dogon tsaki ta wuce d’aki, ba tare daya daina murmushin ba ya bita da kallon *zaki gane kurenki*, Hadiza ce ta juyo ta bita da kallo tace “Ke Hamna lafiyarki kuwa? Meye na tsakin daga abun arzik’i? Bana son iskanci kinji na fad’a miki, wannan ba yayanki bane? Ko dan kinga yau ya sakar muku fuska ne.”

Mik’ewa yayi tsaye yana gyara zaman doguwar rigarshi yana fad’in “Tanti ni zan fita na dawo.”

Kallonshi tayi cike da kulawa tace “A’a, ka zauna mana ka ci abinci saika fita, nasan dai yanzu bakin ruwa zaka je ko?”

Murmushi kawai ya mata ya nufi k’ofar fita, da kallo ta bishi a ranta tana mamakin wani sauyi data gani a tare da shi tana fad’in “Yau Ammar babu saurin kai duka, har Hamna ta mishi tsaki amma ya nuna ko a jikinshi, lallai yau farar juma’a ce, ba dan haka ba ai da sai dai ta jiyo ihunta a d’akin.”

Wata zuciyar ta fad’a mata “Dama ai yau da gobe sai Allah, mutum yana canzawa kamar yanda zamani ke canzawa.”

Ba tare data daina kallonshi ba tace “Ko kuma dai dan za’a had’a shi da Amna ne, tabbas ma hakane, watak’ila kunyarta yake ji yanzu saboda sun zama surukai.”

Bata gushe daga tunanin ba taji muryarshi cikin d’aga murya yana fad’in “Mutumin ya kake?”

Da kallo ta bisu ganin shi da mai gidan nata suna gaisuwa irinta yaran zamani marasa jin magana, murmushi kawai take saboda yanda suka birgeta kamar wani d’a da uba, dawowa sukayi ciki har cikin runfar inda Shu’aibu ya kama hancin Hadiza yaja sosai yana mik’a mata sallayar hannunshi yana fad’in “Matanmu ya aiki? Ashe bak’i kikayi bayan tafiyata?”

Hadiza data saba take kuma jin dad’in zama da mijin nata murmushi ta masa tace “Sannu da zuwa, bak’i kuma ba bak’i ba kam.”

Ammar da soyayyar dattawan ke birgeshi sagala hannunshi yayi a kafad’ar Shu’aibu ya ja hancinshi yana fad’in “Duk ka jaye mana hanci uwa har yayi tsayi kamar karas, ka canza wani salo mana.”

Shima kama wuyanshi yayi suna dariya yace “Uwar ka dai ce ka shammata bani ba ja’iri kawai, kuma ma wani salo zan canza bayan na saba da wannan.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected