BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Kallonshi kaka tayi, ita dai duk da ta lura yaron yana da yan matsaloli amma kan daya wayar mata yasa yake birgeta, malam rabi’u kallonshi yayi, (kunsan barebari da fad’a da zuciya) sai kawai ya ga ai tsagwaron marar kunya ne wannan, dan haka ya kalleshi da kyau yace “Magana nake a kan ku, shin ku su waye? Su waye iyayenku a duk garin maradi? Ina kuka san Mari?kuma kuna nufin kun zo neman auren Mari ne ko me? Ina iyayenku suke da ba zaku turo su ba? Ina son sanin amsar wannan tambayoyin yanzu daga bakinku.”
Duka gira Ammar ya d’aga sama alamar mamaki ido bud’e sosai, gyara zamanshi yayi yanda zaiji dad’in magana, lura da hakan da Amar yayi yasa shi kallonshi yana mishi kallon “Karka siyar mana da halinka dan Allah ko dan Junaid.”
Cike da jin masifa yace “Kai jira zan bashi amsa ne kawai, to ko tsohuwar gidanmu dake da k’wank’wamai ai ina ji da ita bare wannan malamin.”
_Yan uwa a yanda labarin gasken ya kasance saboda Ammar yasa aka sha daga sosai kafin rabi’uya ya amince da auren Junaid da Mari, dan yace yaron k’arshen marar kunya ne bashi ba wannan zuri’ar, amma saboda yanayi yasa zan tak’aita masifar dan akwai abubuwa dayawa anan gaba da zasu faru._
Kallonshi Ammar yayi harda alama yake mishi da hannu danya gane yana fad’in “Ni, da wannan da kake gani, uwar mu d’aya ubanmu d’aya, ince dai a garin maradi kasan lieutenant Hassan Gaga? To in ma baka sanshi ba ka tambaya zaka sani, duk wani mai shige da ficen kaya zaisan waye lieutenant Hassan, dan shine babban douanee a garin nan, idan bai yarda ba sai kayanka su shekara dubu a ajiye kuma a wulak’ance.”
Nuna Junaid yayi yace “Shi kuma wannan d’ane ga colonel Hussein Gaga, shi ma d’in idan baka sanshi ba ka fara kallon tv zaka san waye shi, ko kuma ka zama d’an tada k’ayar baya a cikin al’uma zaka fahimci waye shi.”
Nuna Jibril yayi yace “In dai har garin maradi kake tabbas zaka san d’an kasuwa Labaran Gaga, wanda yan kasuwa suka bashi matsayin chairman d’in su, dan haka tsoho karka d’auka wata bishiya ce aka girgiza muka fad’o, da kuma nayi niyya wallahi ba zan zo nan da niyyar neman aurenta ba kawai, sai dai na zo da sadakinta a d’aura auren mu tafi da matarmu.”
Malam rabi’u da al’amarin ya gama zund’umeshi shima kallonshi yayi zaiyi magana sai kuma Ammar yace “Kuma ka tambaye mu wai ina muka had’u da ita? Ai ina ga kamar kunfi kowa sanin inda zamu had’u da ita tunda kun koreta daga gareku, kenan ina kuke son tayi rayuwa?”
A hassale malam rabi’u yace “Ka ce idan da kayi niyya da zaka zo da sadakinta? To jini da kyau marar kunya fitsararre, ni kuma bawai ina raye ba, wallahi ko bayan ba raina auren Mari ya haramta gareku, dan ga dukkan alama baku samu tarbiyya a gidanku ba, na ga kuma shafaffe da man daya isa a kaf dangin nan nawa daya isa ya d’aura auren Mari ba da amincewa ta ba.”
Wata dariya Ammar ya shek’a wacce ko hak’oran shi basu fito ba sai sautin kawai kafin ya tsagaita yace “Ni kuma Ammar in dai har d’an uwana Junaid bai janye k’udirinshi na son auren Mari ba, na rantse da Allah ko saceta ne sai nayi na kuma d’aura musu aure.”
“A matsayinka nawa? Kai bari dai in mik’e kaga tsawona” Cewar malam rabi’u yana mik’ewa tsaye, Ammar na kallon idonshi yace “A matsayina na yayanshi, zan uya wakiltar iyayenmu akan al’amarin daya shafi dukansu nan, saboda babu wanda ban bawa watanni da haihuwa ba.”
Jibril da shi dai tun shigowarsu yaji gabanshi sai fad’uwa yake, yana kallon tsohon kuma sai yake ganin wani yanayin mahaifinshi a tare da mutumin, baisan dalili ba amma yaji tsohon ya shiga zuciyarshi daga *kallo d’aya*, tunda suka fara musayar yawun nan yake jin baya jin dad’in abinda Ammar d’in keyi, yanzun ma mik’ewa yayiya kama hannun Ammar ya matse sosai ya kalli tsohon yace ” Dan Allah kaka kayi hak’uri, yana da zuciya ne.”
Malam rabi’u shima sai yanzu ne ya kalli Jibril d’in kallo na tsanake, shi kanshi gabanshi ne ya fad’i, Jibril dake rik’e da hannun Ammar fita yayi da shi waje inda malam ya bi Jibril da kallo, wata zufa ce yaji tana tsatsafo mishi ba gaira babu dalili, take ya fara tuna abubuwan da yayi zamanin k’uruciya wanda har yanzu wannan banzar d’abi’ar bai wani barta ba sai dai in bai samu dama ba, sai dai ya kasa tuna wace uwar ce ta haifa mishi wannan yaron? (Ko kuma ta haifa maka wannan jikan ba, wato shi aiki ko na alkairi ko na sharri dama kana iya mantawa idan kayi, amma wanda kayi wa baya mantawa), Amar da Junaid da kaka ne suka dinga bawa malam hak’uri suna tausarshi, da k’yarsuka shawo kanshi bayan Junaid ya nuna mishi yana so su taimaki rayuwar Mari wacce ke tallar kanta ga kowane namiji yana biyanta, sosai ya jima yana mishi nasiha cikin girmamawa, gamsuwa malam yayi hakan yasa yace ya amince da buk’atarsu, amma indai da gaske yake to dole ya turo iyayenshi dan suyi magana ta manya, alk’awari suka mishi kan zata turo manyansu kafin daga bisani suka mishi sallama suka taso suma.
Jibril dake rik’e da hannun Ammar suna fitowa ya fizge hannunshi, bud’e mota yayi ya fito da gorar (bidon) ruwa ya bud’e ya sunkuya yana dararawa a kanshi, saida suka k’are yayi cilli dashi yasa hannu aljihu da niyyar fito da abinda zai goge fuskarshi, lalitarshi ce ta fara fitowa dan haka ya rik’e a d’aya hannun ya sake mayar da hannun aljihu zai fito da shi, kai mai tsautsayi da Allah ya aiko ka kana ganin bak’i ne a garin sai kuwa wani matashin saurayi yayi wup da lalitar ya sura a guje, da sauri da kuma mamaki suka kalli juna shi da Jibril, haba ai saiya mik’awa Jibril mouchoir d’in ya fito da wayarshi a gaban aljihu ya damk’a mishi, da mamaki Jibril ya ke kallonshi yace “Me zakayi Ammar?”
“K’ure mishi gudu zanyi.” Cewar Ammar dake hangen yaron nata gudu.
*Kai jama’a*
*Sai A shafi na gaba muji wai da gaske artawa zaiyi ko kuwa zai rabu da wannan daya tari aradu da kai.*
_Rashin comment, hummm, saura kad’an ku daina jina._
05/06/2020 à 20:21 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BADAK’ALA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
_*AHALI NA*_
*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`
_Bismillahir rahamanir rahim_
_9_
Kamar a almara Jibril ya hangi Ammar ya zage k’arfi ya palla a guje ya bi bayan yaron, tuni hankalin jama’a ya koma kansu ana kallo, yanda yake gudun kamar wanda aka ce idan ya fad’i ya rasa gasar shiga soja kenan, shi kanshi gudun da akeyi saiya birgeka, dama kuma haka Allah yake hallitarsa, idan ya maka kyau sai kaga komai kayi saiya maka kyau ko kuma wani yaga kyanka, duk gudun yaron nan saiga Ammar ya cimmasa har yana neman take shi, k’afa yasa ta baya ya harbi nashi k’afafun hakan yayi sanadiyar fad’uwar yaron warwas a k’asa, kafin ya ankara yasan fad’uwa yayi Ammar ya shak’o wuyan rigarshi tare da bank’are hannunshi ta bayan wuyanshi ya murd’e ya amshi lalitar, ba tare daya sakeshi ba kuma ya izo k’eyar shi gaba izuwa inda suka bari, mutane dake kallon k’aramin kafce wasu na tunanin su bayar da hak’uri su raba, sai dai tunanin su yafi basu cewa soja ne duk da cikin wani yadi yake kalar ruwan madara shara-shara, dan haka meya kaisu shi ma yaron tsautsayi ne da kuma k’arar kwana, yaron da yaga Ammar na dawowa dashi fashewa yayi da kuka yana so ya durk’ushe ya bashi hak’uri amma ya k’i barinshi ma ya kai k’asan, cikin kuka dake nuna tashin hankali yake fad’in “Dan Allah baba na kayi hak’uri, wallahi yunwa ce tasa nayi maka k’wace, ka rufa min asiri kayi min rai.”