BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da k’arfi ta k’ara zaro ido ta kalleshi, shi ma alhajin kallonta yayi da mamaki ya kuma kalleshi yace “Matarka kuma? Ta ina?”

Rik’e k’ugu yayi yace “Au! Tambaya ta ma kake? To matata ce ko bata fad’a maka ba?”

Hamna ya kalla da mamaki ya ma kasa cewa komai, kallonshi tayi tace “Karka kula shi dan Allah muje na rakaka kawai, baya da lafiya ne.”

Kallonta yayi yace “Kafin na gama sabautashi ki daure ki min shiru da bakinki, meye na ki na gaggawar son tafiya ke da yau acan zaki kwana.”

“Ina?” Ta fad’a da k’arfi, saida ya kalli mutumin yace “Lahira mana.”

Baya taja da sauri tana fad’in “Ammar bana son iskanci wallahi, ka fita a harkata mana.”

Kallon kumatunta yayi, jinjina kai yayi tare da addua’r Allah ya bashi k’arfin zuciyar da zai uya dalla mata mari, mayar da hankalinshi yayi kan mutumin yace “Bawon Allah kai nake saurare, meya had’aka da matata nace?”

Cikin nutsuwa mutumin yace “Kaga, ni ba…”

Da sauri ya katseshi da cewa “Ina zuwa, bara ka gani.”

Wayarshi ya fiddo ya d’an daddana kafin ya nuna masa yace “Idan ba matata bace to ta uban wacece?”

K’uri mutumin yayi yana kallon hoton Amna da Ammar suna tare da Ameer Ameera, amma da yake a zaune take kuma ga kama sosai da kwalliya a fuskarta sai kawai ya d’auka tabbas Hamna ce, kallonta yayi yace “Hamna, taya…”

Ammar ne ya katseshi da fizge wayarshi yace “Malam saida izini na zakayi magana da ita.”

Kallon Ammar yayi yace “Kayi hak’uri bawan Allah, ka tabbatar matarka ce ko kuma dai tsohuwar matarka?”

Wani kallo ya mishi yace “A ganinka haukana zai iya sa na mallaki wannan kayan kuma na rabu da ita? Kai ba kayan bane ka biyo?”

Matse baki kawai yayi yace “In kuwa har matarka ce yanzu to akwai buk’atar ka sake saka ido akanta, kayi hak’uri.”

Kallonta yayi yace “To kai baka ganta bane? Mahaukaciya ce fa ta sakawa a gidan gaba, yanzu haka magani take d’auka.”

Girgiza kai kawai mutumin yayi ya wuce abinshi, kallonshi tayi sai kawai ta fashe da kuka ta juyawa da sauri zata koma ciki, da k’arfi yasa hannu ya jawo gashinta yayo baya da ita, sam bata tsammanin haka ba sai kawai ta fad’o a jikinshi gaba d’aya, cit wurin yayi kafin ta fara k’ok’arin tashi da k’afarta, sakinta yayi ta mik’e daga jikinshi inda suka sake kallon juna, cikin masifa da neman sababi tace “Wallahi Ammar ka fita a hanyata, ya zaka korar min saurayi na wanda nake tunanin shi zan aura? Kana da matsala dani ne?”

Sunkuyar da kansa yayi ya d’ago idonshi kamar wani zaki yana kallonta, tambaya yake wa kansa me yasa bata nesanta kanta da wasu ne? Ya jima yana kallonta haka ita ma tana kallonshi kafin ya gyara tsayuwa yace “…

*Alhamdulillah*
14/10/2020 à 00:58 – Ummulkhairi: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*BADAK’ALA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_

*SADAUKARWA GA*

‍‍‍ _*AHALI NA*_‍‍‍

✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ ️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_58_

“Hamna ame kika d’aukeni?”

Sauda ta d’aga masa gira sama ta kalleshi tsaf sannan tace “A babban mah…mana.”

Wani kallo ya mata jin rainin hankalin data masa, mahaukaci take so tace amma shine bata k’arasa ba, kenan mahaukaci take kallonshi? Ai kuwa zai nuna mata a aikace, matsawa yayi kusanta zaiyi magana sai ta k’ara ja baya tace “Malam tsaya daga can mana.”

Jiniyar motocin da suka ji ne yasa su juyawa duka suka kalli k’ofar, mahaifinta ne ya dawo cikin rakiyar masu bashi tsaro kamar kullum, suna kallo akayi pakin motocin aka bud’e mishi ya fito, sauran motocin duk wajen ajiyesu aka nufa dasu inda wasu jami’ai biyu ke biye a bayanshi, kallonshi tayi ta harareshi sama da k’asa ta juya baki tare da jan dogon tsaki tace “Malam ka shirya saina sa ka bawa saurayi na hak’uri, sannan da kanka zaka bashi aure na a matsayinka na babban yayana.”

Shigewa tayi a lokacin kuma mahaifinta ya k’araso, saida ya d’an rumguma Ammar a jikinshi suka gaisa, tare suka shiga babban falon, suna shiga Aissata ta tarbe shi sai ma’aikata da suke ci gaba da gyara wajen cin abinci, Ammar kuma kallon kawun nashi yayi yace “Ina zuwa tonton.”

Bayan Hamna ya bi data haye sama d’akinta, ko zaune ba tayi ba taga ya fad’o mata d’aki yana cire mata cazar waya a jikin bango data saka, da mamaki tace “Malam lafiya? Me ya shigo da kai d’akina?”

Rintse ido yayi ya sake bud’esu akan ta tarau, da k’arfi ya d’aga cazar ya zuba mata a baya, wata uwar ihu ta sake tare da juyawa ta fara taka rawar da babu shiri tana matse k’afafunta da taji fitsari na barazanar danno mata kai, kuka take da iya k’arfinta ta rasa me ke mata dad’i, bata gama jin azabar ba taji ya shak’o wuyan gashinta a daidai infa ta d’aureshi da ribom ya jawota, hannu tasa ta rik’e hannun nashi d’aya kuma ta rik’e rigarshi daidai mab’allan rigarshi tana sakin wani kukan tana fad’in “Kayi hak’uri yah Ammar, kayi hak’uri dan Allah ba zan sake ba, karka dake ni dan Allah na tuba.”

Tunda suka ji ihunta suka d’aga kai sama suna kallo, suna ganinsu ya sauko da ita k’asa har gabansu ya gurfanar da ita, tonton ya kalla fuskarshi babu alamar ya tab’a dariya a rayuuwarshi yace “Ku zama shaidata, wallahi saina karya yarinyar nan idan ta sake tara mana yan iska a gida, sannan…”

Ya fad’a yana sake kallonta yace “Ki tattara kayanki gobe zaki koma gida, nan dan kinga babu mai saka miki ido yasa kike abinda kika ga dama, to zaki koma can gaban Hajia da Ummy.”

Cazar hannunshi ya jefa mata a jiki ya sunkuya ya nuna ta kamar zai tsone mata ido yace “Ki tuna da cewa indai akwai rai da rabo, sannan akwai lokaci to wata rana zanyi iko akan ki.”

Kamar zai taka ta haka ya wuce ko kallonsu tonton bai sake yi ba, da kallo ya bishi baki sake, shi fa ba mamakin abinda yayi bane yake bashi, kalamanshi na k’arshe da kuma yanda abun ya b’ata mishi rai, to duk me yayi zafi haka? Dawo da kallonshi yayi kanta yace “Koma ciki, sannan ki had’a kayanki gobe zaki koma, ba zan iya jarabar yaron nan ba.”

Cikin kuka ta mik’e tace “Wallahi Abba babu inda zanje, haka kawai sai kace wani uba na.”

Nunata yayi da yatsa yace “Ke ki bar bala’i yayi kwana, ina ce yanzu a gaban uban naki ya miki wannan k’wak’waran kashedin? To dan haka ki d’auka ma yafi ubanki.”

Tumurmusa k’afafu ta shiga yi tana fad’in “Allah Abba ba zan koma ba, ni nafi son zama anan, kawai dan ya fad’a shikena ba zaka ce masa komai ba.”

Matsawa yayi kusanta ya dafa kafad’arta cikin taushin murya yace “Yar albarka, kiyi hak’uri ki tafi kinji, shi da gobe ne zasu tafiyarsu, daya tafi saiki dawo idan haka kike so, pour les moment dai ki tafi kinji ko.”

Jinjina kai tayi tace “Ok Abba, amma ka fad’a masa ya daina takura min ya fita a harkata, inba haka ba zan masa rashin mutumci.”

Jinjina kai sha yayi ya shafa kanta yana kallo harta haye sama, kallon Aissata yayi wacce ita hausar ma bata gama ji da kyau ba yayi murmushi, ciki ya wuce da jinjina al’amarin yaron nashi mai kama da d’an uwanshi colonel a zafi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected