Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Toh dan masani, sannu da kokari”
“Yauwa sannu dai Hajiya”
“Ya gidan ya iyali da komai”
“Komai lafiya kalau, Hajiya”
Ta dauko katon madubi ya dora a cinyarsa.
“Daman… ”
Zata fara bayani ya daga mata hannu, ya dangwalo yawun bakinsa yayi rubutu da shi, sannan ya kalleta ya girgiza kai ya maida idonsa a gurin madubin, ya fi karfin minti ashirin a haka sannan ya dago ya kalleta ya ce.
“Kanwar Kulu ta kawo ki nan ko?”
“Eh haka ne, can gidansu na fara zuwa sannan aka kawo ni nan”
“Na gani ai, kuma kin zo nan ne saboda mijinki zai kara aure, gashi kuma ya canja miki, ga danki yana son auren yar kishiyarki da ta fita, kuma kina fargabar kar ciwon da kika aika mata ya karya ta tashi mijinki ya ce zai dawo da ita, sannan kina yawan faduwa har ki ji ciwo a kafa har kika tsoron ko an miki ture ne”
Ta daga masa kai.
“Hakkun babu musu a maganarka take”
Yayi dariya.
“An fada mana komai ai”
“Haka nake so, yanzu so nake a hana ďana auren yar iskar yarinyar, kuma a hana mijina aure, sannan a dauke hankalinsa daga gurin kowa sai ni, idan da hali ma wannan matar da take tare da shi abokiyar zamana ita ma a koreta, sannan bana son mijina ya dawo da Iyami, kuma ciwon kafar nan ba turo min aka yi? Ni har tsoron faduwar nake ji kar naje na fada a inda be kamata ba kafar ta cire ko ta karye na shiga uku”
“Duk za’ayi Hajiya, amman sai kin daure kuma kin shirya domin ni bana aiki da wasa, ciwon kafarki kuma babu wani ture babu aljannu babu komai, daga Allah ne”
“Toh Alhamdulillah yanzu hankali ya dan kwanta, kuma daman ni ai haka nake so, yanzu miye abun yi?”
Ya aje madubin dake jikinsa gefe daya ya dubeta.
“Ina mai tabbatar miki da wani abu, tabbas mijinki zai dawo da abokiyar zamanki da kike tsoron ya dawo da ita, matukar baki tashi tsaye ba”
Hajiya Kaltume ta dora hannu a kai tana jin wani karin tashin hankali na kusantota.
“Shiyasa na zo gurinka ai, dan Allah a hana ya maido da ita”
“Za’a iya hakan ne kadai idan zaki iya daukar nauyin jini, amman muddin matar nan tana raye babu makawa sai ta dawo gidanki”
“Dan masani me kake nufi kenan?”
“Ni matsala ta bana boyo kuma duk abun da na gani ina fadawa mutum gaskiya, amman ina aiki na gaskiya, abun da ya fi kawai mu yi ma matar nan halbin kasko domin matukar tana raye Wallahi ina mai tabbatar miki mijinki sai ya sake zaman aure da ita”
“Dan masani babu wata hanyar sai kisa? Kar abun yayi min yawa?”
Yayi dariya.
“Ashe baki shirya kenan kika zo, baki shirya mallakar mijinki ba, kuma baki shirya hana kishiyarki dawawa ba, gaskiya ban ga wata mafita a nan ba bayan wannan, domin madubin nan baya kara kuma ya nuna min akwai sauran zama a tsakaninsu”
Hajiya Kaltume ta yi shiru na wasu dakiku sannan ta sauke ajiyar zuciya ta ce.
“To maganar mallakar Alhaji fa? Da kuma hana dana aure”
“Za a yi miki na mallaka zaki mallake Alhaji ki koma kamar uwarsa, karki damu da wannan amman fa zaki zuba kudi”
“Kamar nawa Malam?”
“A kalla za a kashe 50k”
Ta yi murmushi 50k abu ne mai sauki idan dai zata samu biyan bukata.
“50k ma matsala ba ne, zan bada fiye da haka ma, amman a duba idan akwai wani aiki mai sauki da ba sai kisa ba sai ayi”
“Bari kiji na fada miki, matar nan ma tana nan ta fara tashi domin wanda kika saka yayi miki aikin nan ya fara karya aikin, tabbas kuwa zata dawo cikin gidanki, kuma dawowarta yana nufin fitarki”
“Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un, fita ta kuma? Ai ni shi ne tashin hankalina, ta zauna ma ya na kare balle ita tana ciki ni ina waje?”
Gaba daya sai hankalinta ya tashi ta ji wani gumi na keto mata.
“Amman kana ganin idan an aikata aikin zai yiyu?”
“Me zai hana? Saboda hasarin halbin kasko idan be sameta zai iya fadawa akan jininta shakiki kamar danta ko yarta”
Hajiya Kaltume ta taba hannu biyu.
“Shikenan ma daman yarta ta isheni a duniyar nan, a aikata mata kawai ka ga aikata mata zai saka su ji tsoro su hana Yasir Rukayya, kuma zan huta nima hankali ya kwanta, amman ina lafiya idan aka ce zata dawo kuma ni na fita”
“Idan aka yi haka babu ita babu mijinki har abada”
“Toh yanzu yaushe za’ayi aikin”
“A yanzu ma idan kika bada kudi, sai a dauko kayan hadi a kira aljannu, cikin dare za’ayi halbi kin ga ruwan da yake cikin kaskoncan? A cikinsa za a halba idan aka gabatar da aiki aka yi halbi da dare kamin safe sako ya isar mata, amman fa tabbas idan be sameta ba zai fada akan yarta balle ma ita muke fatan ya samu”
“Akan samu irin haka ne, ayi ma mutum aiki kuma ya zama be fada kansa ba?”
“Ban taba samun irin haka ba, gaskiya wani lokacin ma akan fada ma mutum biyu da uwa da jininta, kawai ina tabbatar miki karfin aikin ne”
“Zan biya kudin, zan bada 200k gaba daya, ina son a hana dana aure kuma a janyo hankalin mijina a gareni sannan kuma a hana shi aure wacan yarinyar da yake hasashen aure a yi musu farraqu”
Dan masani na jin 200k ya ji ransa yayi wasai kudin wata gona da wani gidan kauye har da fili ma.
“Hajiya ni ko ina tabbatar miki, kuma na miki alkawari tsakanin yau zuwa gobe zaki tashi da labari mai dadi akan kishiyarki, na mallaka kuma akwai aikin da zan hana sai ki aiko ko kuma ki zo da kanki jibi ki karba, da zarar ya ci an gama da shi, a game da auren da zai kara kuma wannan ni an san aikin da zan yi, mai irin sunan yarinyar ma ba zai sake sha’awa ba”
Hajiya Kaltume ta yi murmushi ya jinjina kai
“Haka nake so, so nake na mallake komai a gidan nan, ya zama be ganin kowa sai ni da Yayana, Hurriya ma ina son a cire masa ita a rai kwatakwata”
Ta saka hannunta a jaka ta dauko 200k ta aje masa.
“Idan bukata ta biya zan baka ninkin wannan, ni dai burina ayi aiki yayi”
“Aiki kam ya gama, tashi ki yi tafiyarki”
“Na Gode dan masani”
Ta mike tsaye tana jin kamar an yaye mata damuwarta gaba daya, tunanin kar ta daukarwa kanta hakki da yawa duk ya kau saboda ta ji ance zata fiya Iyami ta dawo. Bata bar garin ba sai da ta sake komawa gidansu Kulu ta yi musu alheri kowa ta bishi da 1k sannan ta shiga motarta direbanta ya kama hanya, suna mata addu’a bayan sun gama murna da jindadin kyautar da ta yi musu. Ta isa gida cikin farinciki kamar wata wanda ta aikin jihadi, tana shiga bangarenta ta yi wanka ta yi sallah sannan ta fito ta shiga Kitchen da taimakon Salma da Khairy suka gama girkin dare, sannan ta koma dakinta su kuma zauna a falo. Bayan gama sallah magariba ne yar yayarta ta shigo gidan daman ta kan zo jefi jefi idan an yi hutu. Hajiya Kaltume ta yi murna da zuwanta sosai daman suka sha hira a dakin kamin ta shiga da kayanta a dakin Khairy. Misalin karfe tara daidai Hajiya ta dauki abinci mijinta ta shiga bangarensada kanta ta kai masa, so take ta dawo da al’adarta ta kai masa abinci da kanta saboda ta samu damar tsare shi kuma ta tabbatar ya ci abincin idan ya saka maganin da bokanta dan masani zai bata. Sai dai gaba daya ya lura da yanayinta be sauko ba daga tsabanin da suka samu jiya, har yanzu fuska a daure take kuma tun bayan da ta gaishe shi ya amsa be sake ce mata komai ba, ita kuma bata yi yunkurin wani abu ba, har sai da ya fara cin abinci, sannan ta dawo gabansa ta zauna ta zuba masa ruwa.
“Wai Alhaji yanzu saboda dan tsabanin da muka samu jiya shi ne kake ta wannan fushin? Yaushe rabon da ka yi fushi da ni haka?”