VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

“Kuma Allah ya hada jininsa da ke, duk ya zo garin nan sai ya zo nan”

“Kin ji Namra da wata magana, uwa daya uba daya ai ta wuce wasa, ko kin manta alakata da mahaifinsa ne, ga kuma Hajiya Turai a bata da kawa a familynmu sai ni”

“Duk da haka dai Momy, Wallahi idan baya ra’ayinki ba zai zo ba, ba ke kadai kuke uwa daya uba daya da mahaifinsa ba amman ke kadai ce yake zuwa gurinki, duk ya zo gurinsu Hajjo sai ya zo nan, waya ma akai akai yana yawan kiranki”

“Haka kuma da maganarki, je ki taso masu aikin nan yau muyi tashi dole su zo su fara aiki, ke kuma ki shirya ki wuce makaranta”

“Okay”

Ta amsa sannan ta nufi sama, Momy ta dasa hirar da su Miwan.

“Ku yaushe zaku koma hutu ne wai?”

“January nan zamu koma, ni ai gaba daya na samu na bar garin nan na huta”

Musib ya ce.

“Kai gari kake son bari, ni Wallahi kasar ce ya isheni, ba dan halin Appa ba kamar mu zai hana a fitar waje, maza ne mu fa kuma yawanci yayan sa’ainsa duk suna waje suna karatu amman ya hana a fitar da mu kuma shi ba zai fitar da mu ba”

“Jami’ar nan kawai zaku kare a nan, amman masters da duk wani abu da zai biyo baya a waje zaku yi shi, na gaji da halinsa shi har yanzu be gama jefar da wannan halin nasa na da can ba, kuma a yanzu tun da na fahimci baya bin ra’ayi toh kowa yayi nasa ra’ayin kawai, duba yadda ya daga mana hankali jiya saboda kawai Hurriya ta zauna a nan”

“Wai me yasa ba zata bi mahaifiyarta ba?”

“Kai kana ganin uwarta zata yarda ta bita su zauna a can? Ai ba zata yarda ba tana ganin ga gidan arziki”

“Toh ai ko da sun koma Appa zai mata komai”

Musib ya sake fada.

“Amman dai ba kamar idan tana gidan nan ba, kuma Kaltume ba zata yarda Alhaji ya yi haka ba, yadda ba ta bar shi ya kula da yarsa Sapna ba haka ba zata bar shi ya kula wadannan yaran ba matukar suka bar gidan nan”

Miwan ya ce.

“Wai Momy saki nawa yayi mata ne?”

“Ina ruwana? Balle na tambaya can ta matse musu idan uku ne sun hutu, idan daya ne ma ya dawo da ita duk ruwansu ne ba nawa ba, ni ta harkokin gabana nake shirya ba a kaina take zaune ba, daga ita Iyamin har Kaltume babu wadda zata nuna min komai gaba da baya, mu da talauci sai a baki shi ma dan ambata kawai, su ko babu wadda bata tashi a cikinsa ba, ni ko babu wadda be san ubana ba a garin nan ba”

“Ai shiyasa Hajiya take shakkarki, yadda take ma Amma da yayanta bata mana haka”

“Ai bata ga fuska ba ne, ita kanta ta san na fi karfinta ta ko’ina, kuma ni bana jiran abun Alhaji ita da Iyamin dai suka dogara gareshi”

Hira sosai suka yi ta yi Momy na koda kanta a garin gusau ma jin take ba ko wace matar mai kudi ce sa’ar yinta ba balle kuma cikin gidan Alhaji Haruna Mai Yadi.

HURRIYA POV.

Tana shiga part dinsu sai kewar Amma ya kara daduwa a ranta, ta san da a jiya ne da kwanakin baya da Amma take gidan sai dai ta fito daga dakinta ta sauko kasa ta yi breakfast ba dai taje wani bangaren ta kwana ba har tana fargabar arba da Momy. Kujera ta nufa ta zauna ta rike hannayenta hawayen dake idonta suka zubo mata.

“Huriyya…”

Ta kalli kofar kitchen din da sauri tana zabura domin ta tsorata ba yi zaton akwai mai kallonta ba. Da sauri ta cire gilashin idonta ta share hawayenta da hannu biyu ta mike tsaye.

“Ya Yasir yaushe ka shigo?”

“Tun dazu abun karyawa muke hadawa da Hamad”

Ta fara takawa ta nufi kofar kitchen din da yake tsaye.

“Kuka kika kwana kika yi jiya ko? Idonki har ya kumbura, kuma kin san matsalar idonki why zaki jawa kanki wata matsalar”

“Yaya idan na tuna Amma bata nan sai na ji babu dadi, kukan zo min yake”

“Addu’a zaki yi, kuma ki daina damuwa Amma zata dawo da yardar Allah”

“Haka Appa yace maka?”

Ta tambaya tana kallonsa wasu hawayen na sauko mata zuciyarta kuma cike da daukin ya amsa mata da eh zai haka yace.

“Aa haka dai nake sashe, kuma ni na san haka zai faru ko dan ku, baki ga yadda hankalinsa ya tashi ba jiya saboda fada miki da Khairi ta yi, karki so ganin fuskarta yau sai da na kumbura mata baki”

Hamad dake can cikin kitchen yana juya plantain yayi murmushin jindadi jin cewar an kumburawa Khairi fuska. Hurriya kuma zuciyarta ta cika da tausayinsa.

“Da baka doke ta ba Yaya ai gaskiya ta fada min”

“Ba haka ya kamata ta yi ba, kuma be kamata daga ke har ita ace kuna shiga maganar manya ba, dan haka ke ma ki kiyeye kar na cire miki ido”

Ta yi dariya tare da maida gilashinta bayan ta share hawayenta. Saboda ya dauke musu kewar Amma ya zo part din ya fara hada musu abun karyawa yana cikin hadin ne Hamad ya shigo sai ya kira shi suka cigaba da yi tare, bayan sun gama suka hadu a dinning har Hurriya suka soma karyawa tea kawai Hamad ya sha sai yankan bread daya ya ce ya koshi, Yasir ya kalleshi sai dai be ce masa komai ba domin ya fi kowa sanin ba a cilasta Hamad yin abun da be tashi yi ba a kwashe lafiya, zai iya cilasta masa kuma ya ci amman kuma za su yi fada su rabu da bacin rai.

“Jiya ma haka yayi be ci abinci ba”

Hurriya ta fada tana tauna bread din dake bakinta.

“Ya saka tunanin abun da ya faru ne a ransa, kina ganinsa kamar be damu ba ko? Ya fiki damuwa daman mu maza haka muke muna boye abu a ran mu babu mai sanin muna da damuwa sai idan an bincika ko kuma an saka mana ido”

Hurriya ta dan yi murmushi kadan.

“Amman mazan ba kowa yake da zuciya kamar Hamad ba, ya cika fushi”

“Akwai su, wasu sunada fushi sosai a mata ma ana samu balle kuma maza, baki dai taba haduwa da su ba ne, ai halitta ce za a iya samunta a gurin mace haka ma gurin namiji, shi ma Hamad zai daina idan ya kara girma yayi wayo”

Bata sake cewa komai ba har ta gama karyawa sannan ta tashi da sauri ta nufi upstairs.

“Bari na yi wanka na saka uniform”

“To sai ki yi sauri domin kusa latti”

Ya mike tsaye ya fice daga bangaren zuwa bangaren mahaifinsa domin gaishe, kamin ya isa bangaren mahaifinsa ya hango shi tsaye waya a hannunsa yana dannawa, hakan ya saka Yasir ya cira kafa ya karasa gurin mahaifinsa sai yaja ya tsaya yana sauraren wayar da Appa yake.

“Kamar da karfe goma dai, amman ina son a kwashe komai kamin yara su dawo daga makaranta”’

Yasir ya dan kalleshi zuciyarsa na raya masa kayan Amma za a kwashe. Ashe kuwa ya canka daidai domin a karshen zancen sai Appa ya karasa da fadin

“Zan turo address din da kuma number wayarta ko da ba ku gane gurin ba”

Ya sauke wayar ya shiga message dinsa ya fara rubutu location din. Yasir ya mika gaisuwa cikin girmamawa kamar yadda ya saba.

“Lafiya kalau an tashi lafiya”

“Lafiya kalau Appa”

Daga haka Appa be sake cewa komai ba shi ma kuma be ce ba, daman baya tunanin Appa yayi maganar Amma ko wani abun da ya shafe ta da shi idan dai ba umarni zai ba shi akan wani abun ba, shi kuma be isa ya daga kai ya kalli mahaifinsa yayi masa magana akan lamarin aurensa ko wani abun da ya shafi matansa ba.

“Hurriya sun tashi kuwa”

Appa ya tambaya, domin tun tashinsa zuciyarsa take son zuwa duba yaransa sai dai gudun kar ace ga nuna banbanci ko kuma su ya fi kaunarsu da sauran yara ya saka ya danne ya boye abun.

“Sun tashi tare muka karya ma, amman Hamad be ci wani abun kirki ba?”

“Ba shi da lafiya ne?”

“Lafiyarsa kalau Hurriya tace jiya ma be ci komai ba”

Appa ya sauke ajiyar zuciya a hankali ba tare da ya bari sautin saukar numfashin ya fito ba. Har lokacin kuma be kalli Yasir dake tsaye gefensa ba kamar mai jin kunyarsa. Suna tsaye gurin har yara suka fara zuwa karbar chocolate da juice din da ya saba raba musu idan za su tafi makaranta, Appa ya koma ciki sai Yasir ya bishi ya riko masa suka fito da kayan waje sannan ya zauna a one of kujerarun dake gurin, ya fara raba musu suna karba yaran Hajiya Kaltume ne a gaba, Khairi kam baki ya kumbura gashi ta turo shi gaba ita ala dole an mata ba daidai ba fushi take, sannan Namra ta zo ta karba, a da can Hurriya da zumudi da far’a take zuwa karba kuma a kullum Hamad sai ya rigata karba, domin shi baya bata lokaci a komai ba kamar ita ba sarkin latti, cin abinci ma sai kowa ya cinye ita bata cinye nata ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected