VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

“Ni ban yi mata tsanar da zaka roki mutuwa akan rayuwarka ba, ni mai kaunar abun da kake so ce kawai dai ina ganin rashin dacewa ne akwai, ni mahaifiyarka ce Jamal ba makiyiyarka ba”

Captain yayi murmushi yana jin dadi a zuciyarsa, daman ya san Ammy ba zata iya zabar mutuwarsa da rayuwarsa.

“Ina son ki Ammy ina sonki sosai, shiyasa yanzu da kika ji yarinyar nan farinciki ya rage, saboda baki goyon bayana kuma babu wani annashuwa da murna da kike na auren, wata kila ma jira kawai ake na yi auren a karbi rayuwata maybe shi ne last abu da zan yi a rayuwata, wata kila zan tafi ne kawai na bar muku yarinyar nan, ko yanayin aikin da nake ma rayuwata kullum a cikin hatsari take komai zai iya faruwa….”

“Wane irin magana ne wannan?”

Ta daka mishi tsawa.

“Wane zance kake haka? Me yake damunka? Ina ce komai ya wuce ai, me kuma ya sake dawo da zancen mutuwa?, bana son wannan maganar karka sake”

Ya amsa mata kai yana murmushi.

“Ba zan sake ba Ammy”

Ya kwanta a jikinta kamar yadda yake mata a lokacin da suke cikin Kaduna idan yana gida tare da ita, babu ruwansa da girman da yayi kwantawa yake a jikinta yayi ta zuba shagwaba, kamar wani yaro. Kansa ya shafa yana kallonsa ita kam ba zata iya jurar rasa danta ba, zata haka for now domin ta san gaba ba zai dade ba, yadda yake da fushi ma wata kila da kansa zai zo ya fada mata ya saki Hurriya wata rana, domin zuciyarsa ba ko wace mace zata iya zama da shi ba, shi ma ba zai jure wani abun ba. Dan haka zata aje makamanta a gefe ta saka musu ido, gudun kar ta rasa ďanta kuma ya dauke ta a matsayin makiyiyarsa. Wannan ne abun da ta ayyana a ranta.

 

HAJIYA KALTUME POV.

“Daga min mana Ruma kafar nan ciwo fa take min amman sai ki rika dora min kanki nan kamar baki tausayina, gashi idan ina tafiya kamar zan yi dingishi haka nake yi, ina tunanin Egypt zan tafi a duba min ita, tun da nan sun gagara gane komai”

Ruma ta tashi daga kwancen da take a jikin Hajiya Kaltume ta kalli Khairy dake zaune tana gyara akafaitar.

“Yau ke da kanki kike gyara kafarki?”

“To ya zan yi? Ni tsoron fita nake yanzu, mutane za su fara kallonka saboda video nan da ya fita wata kila ma har a nuna ka ace ita ce”

Khairy ta fada kamar zata yi kuka. Hajiya Kaltume ta ce.

“Ke daina damar da kanki, abun ne dai kin riga min yi da kin yi shawara da ni da ba zaki aikata ba, ku yara ne ba ku san bandar kasa ba, sai ku rika gaggawa kuna son aikata abun da zai kaiku ya baro, gashi nan duk kin bi kin rame, kin tsallawa a madadin ita aka yi ma ta shiga damuwa gashi nan ma shirye shiyen aurenta kawai ake yi, ni damuwa ke damuwa abu ya taru yayi mana yawa, ni na rasa ina ma zan saka kaina na ji sanyi”

Hawaye ya zubo a idon Khairy.

“Da na san haka abun nan zai zama Wallahi ba zan aikata ba, kuma Wallahi ba ni na yada hotunan ba, ni dai kawai na nasa barazanar zan yada ne, shi ne yayi min shairi yace ni na aikata, gashi ya fadi zancen fyaden nan kowa ya ji, na muzanta Hajiya na ji kunyar duniya”

“Ba ke kadai ba, abun ya shafi kowa ai, da murna nake da Hurriya ce ta janyo sai gashi reshe ya juye da mujiya, ga abokiyar taya ni yakin tana can babu lafiya, ni na rasa ma ina zan kama, abubuwa sun tsaya min cak…! Ina tunanin shiryawa zan yi na tafi gurin Yaya Altine…”

Bata rufe zancen ba Alhaji Musa ya turo kofar falon ya shigo da sallamar fuska kuma babu annuri. Hajiya ta amsa Khairy ta sauke kai kasa tana jin kunyar hada ido da kanen mahaifin nata, ruma kuma ta gyara zamanta tana masa sannu da zuwa sai ya amsa yana zaunawa.

“Yauwa… Sannu dai Hajiya barka da gida”

Hajiya Kaltume dake jin kamar ya zo yayi mata albishir ne na ganin ya daidaita tsakaninta da Appa ta amsa masa tana murmushin karfin hali.

“Lafiya Kalau Alhaji Musa ya yaran?”

“Alhamdulillahi…”

“Maa Sha Allah…”

Sai kuma shiru ya biyo baya tun bayan da Hajiya Kaltume ta yi magana ta karshe. Khairy ta daga kai kadan ta kalleshi ta ga ita yake kallo sai gabanta ya fadi, ta mike tsaye zata bar falon ya katse shirunsu ta hanyar dakatar da ita.

“Zauna Ummulkhar maganar ai duk a kanki ne… Wato Hajiya dazun ni da Yaya mun tafi gidansu Hajiya Iyami, to ni ina daga waje saboda na dan ba su guri ne su gana, sai gashi ya fito yana fada min iyayen yaron nan ne suke son ganinsa….”

Daki daki Alhaji Musa ya jera musu abun da ya faru har zuwa karshe.

“A takaice dai yanzu shi yaron yace baya ciki idan ta samu wani ta yi aurenta”

Khairy ta fashe da kuka mai karfi daman ta saka ran haka, ganin yadda yaki ya daga wayarta tun daga lokacin da abun ya faru har zuwa yau da aiko musu da mummunan sako, Ruma ma kallon Khairy take cike da tausayinta domin ta san abubuwan za su mata yawa ne. Fasa auren na Khairy da aka yi ba daga hankalin Hajiya Kaltume ya jefata a tunani ba kamar jin cewar Alhaji Musa ya bawa Appa da Amma guri domin su gana sai ta ji kamar an watsa mata garwashi a zuciya.

‘Su gana kamar yaya? Daman ganawa suke a yanzu? Ko da yake ga zahiri tana ganin shirye shiyen auren Hurriya da ake sai dai ta ji labari yadda aka yi ko za’ayi a gurin ďanta Yasir idan ta shinshini gulma, be bawa Momy ta yi komai ba ita da take karkashinsa a yanzu balle kuma Ita da igiyar aure ta raba, yanzu hankalin Appa ya koma gurin Iyami kenan? Gashi har da zuwa da kanensa ko dai auren zai maida? Tun da yanzu ta samu lafiya kamar yadda ďanta ya fada mata tun kwanakin baya? Ita kam abubuwa sun ribchabe mata a yanzu komai ya shige mata hudu…’

Bata gama sakar zuci ba Alhaji Musa ya kira.

“Hajiya kin fahimce zancen nawa?”

Sai ta kalleshi kamar wata yar marainiya idonta na cika da hawaye, ta rasa laifin me ta yi abubuwa suka zo mata a haka.

“Na fahimta Alhaji Musa, to me zan ce kaddarori ne gasu nan sun rufe mu..”

“Shiyasa aka ce idan zaka gina ramen mugunta ka gina gajere, yanzu gashi garin yi ma yar’uwarki sharri kin kunyata kanki kin kunyatata kin bata sunan gidanku, ina amfanin haka?”

Hajiya Kaltume ta dafe kanta.

“Yara ne sai ka rasa gane me ke cin zuciyarsu batsa tsayawa su yi tunani”

A nan ya samu zaren zancen ya rufe ta nasa fadan yana karanta mata inda yake ganin abubuwan da yake yi ma yaran ba daidai ba ne.

“Komai dai aka yi uwa ake dorawa laifi, to na ji Allah ya yaye mana”

Ya tashi ya fice daga falon ba tare da sallama ba.

“Yanzu ni Hajiya Fatee zata yi wannan cin fuskar, ashe ko mutuwa na yi ita din ba mai rufa asirin yaya ba ne? Har zata kyale Fadeel ya aiko wai ya fasa aurenki? Ita Hurriya ba gata nan makauniya ba amman a haka da siraicinta da komai ta samu dan manya mutane ya aureta?”

Ruma ta share hawayenta ta ce

“Hajiya Saboda Hurriya bata aikata ba ne aka yi nata sheri aka ce ta yi, shiyasa Allah yayi mata wannan sakamakon, daman sakamakon masu hakuri mai girma ne, shiyasa yake da kyau mu kiyayi iyakokin Allah domin ba za mu iya jurar radadin ukubar sa ba, gashi yanzu tun ba ayi nisa ba ta fara ganin illar abun da ta aikata”

“Ke dalla can rufe mim baki, tun kamin a haife ki na san wannan! Tashi ki ba ni guri, daman ke da Yasir haka kuke kamar ba ni na haife ku ba”

Ta lalabo wayarta dake hannun kujera ta shiga kiran Hajiya Fatee….
Fadeel ya gyara mata fillon dake bayanta ta jingina da fillon tana runtse ido, ta cije baki alamar ba karamin ciwo take ji ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected