VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Hajiya Kaltume ta yi kamar bata ji ba ta shiga wani bangaren na wayarta, kamin ta kara wayar a kunnenta.

“Yasir kana kusa?”

Yasir ya amsa a dayan bangaren.

“Eh ina nan waje, muna tare da Kamal ne”

“Asibiti nake son mu tafi idan ka gama”

“Waye ba lafiya”

“Ni ce, amman dai da sauki, ka bari sai ka gama ni ma akwai abun da zan yi yanzu”

“Toh”

Ta sauke wayar ta kalli Kulu, sai a lokacin take amsa mata maganar da ta yi.

“Ai kara da kika yi haka, saboda kaucewa ido”

“Duk wani abun da zai saka Momy ta ji ko ta gane akwai alaka a tsakaninmu ina kokarin ganin na gujewa haka”

“Kin kyauta, dabam na ce a kira min ke ne, saboda mu yi wata magana da ke, kamin nan tashi ki tura kofar dakin”

Kulu ta kike tsaye ta nufi kofa da ta bari a bude ta rufe, sannan ta dawo ta zauna ta natsu sosai tana sauraren matar da ta fi tsoronta a yanzu fiye da uwar dakinta.

“Aminci ne ya saka na nake tambayarki abu ko na saka ki yi, na san ba dan kin dauki sarka da kudi ba, wata kila ba zamu san juna ba, amman bana son kina kallon wannan a yanzu, ni daman tuni na tattara wannan abun na aje a gefe daya”

“Hajiya ai ba dan karki ce na yi karya ba, nikam da nace satar nan ta zame min alheri domin sanadinta na hadu dake”

Hajiya Kaltume ta sauke ajiyar zuciya ta marairaice fuska.

“Kulu ke da yar’uwata duk daya a yanzu, shiyasa har na kira ki nake son na fada miki damuwata, kuma neman samun mafita a gareki”

“Hajiya tafi kanki tsaye, duk wani abun da kike so zan miki shi, yadda kika rufa min ba ni da kamar ke a duniyar nan”

Dogon numfashi Hajiya Kaltume taja ta sauke sannan ta furta.

“Kulu ina cikin damuwa da matsala kala kala, amman wanda ta fi min yawa, ita ce ciwon kafar nan dake damuna, yanzu haka kiran da kika ga nayi ma Yasir ita zan kai asibiti, na dade ina ciwon nan amman har yanzu babu sauki babu alamarsa, tun ina barin ciwon a cikina abun ya fara min yawa, to yanzu kuma sai abin da biyo har da mafarkai da ba su dace ba, kuma ciwon nan sai cigaba yake, abun ya ba ni tsoro, ga maganin asibitin nan yi ake amman a banza”

Kulu ta dukufa a tunani har wani kada ido take tana jinjina kai.

“Hajiya ba zaki gwada na hausa ba? Ko Allah zai saka a dace?”

Kamar an yi ma Hajiya Kaltume albishir haka ta ji, saboda Kulu ta sosa mata gurin dake mata kaikaiyi.

“Shiyasa na kiraki ai, kin san ku ne mutanen kauye, kun fi sanin irin abubuwan nan, wata kila ba zaki rasa sanin masu irin aikin ba”

“Akwai su Hajiya kala kala, akwai wata mai aljannu tana bada taimako sosai, kuma akwai namiji ma yana yi”

“Yauwa namijin dai zai fi, ni ban cika son mata masu aljanu ba, na fi son inda zan tafi a fada min ko minene, jifa ce ko kuma ciwo ne ko iska ne”

“Aiko kina tafi gurin Malam na gangare zai fada miki ko menene, domin shi baya son ma ka fada masa abin da ya kawo ka shi zai baki labarin komai, har abun da baki sani ba, da madubi yake aikinsa yana kallo madubi ya fadi magana ta tabbata, kuma ko minene a take zai rabaki da shi, idan jifa aka yi miki ko turbuda a take ma zai ciro shi”

Hajiya Kaltume ta dauki filo ta dora a cinyarta ta kwantar da hannayenta akai tana gyada kai.

“Yauwa irin su nake so masu aiki kamar yankan wuka masu zafi”

“To idan kika kai gareshi magana ta kare, domin shi ko mutum kika ce ya kashe miki zai kashe”

“Irinsa ya dace, kin ga ko minene a take zai fada maka kuma ya karya shi, a ina hake Kulu?”

“A kauye uku yake, dake nan cikin bunguɗu”

“Babu nisa sai dai ban san yanayin hanyar ba?”

“Hanya lafiya kalau take, ai garin mu babu irin bata gari, su kansu suna tsoron mutanen yankin”

“Maa Sha Allahu, sai dai kuma tafiyarmu kamar ba zata yi a tare ba, saboda uwar dakinki Nafisa ba zata bari ba nake gani”

“Wannan ba matsala ba ne Hajiya, kina shiga garin Bunguďu ki dauke hanyar kauye uku, da kin isa ki ce gidan Malam Ashiru mai Yasin da Allon karfe kike nema, ko karamin yaron zai kai ki, idan kuma kina jin ba zaki iya haka ba ke nemi gidan su Kulu taroro kina shiga gidan ki ce ni na aiko ki gurin Malam Ashiru za a kai ki, zaki iya ma kira na yi magana da su”

“Allah dai ya saka miki da alheri Kulu, ina ganin ma ba zan tafi asibitin nan ba, gobe ina gama karyawa zan kama hanyar garin, zan iya tafiya da direba na ma ya kai ni garin”

“Daman Hajiya tafiya da daren ba ai ya fi sirrin da sauki”

“Haka zan yi, zan fara zuwa gidan na ku sai na kira na ba su ku gaisa idan ya so sai kun iso gurin Malamin zai fi sauki”

“Toh Hajiya, Allah ya bada lafiya”

“Amin”

Hajiya Kaltume ta mike tsaye daker tana cige baki kafar kuma kamar zata yi gurmanta da ita haka ta taka ta isa gurin kayanta ta bude wardrobe ta dauko wani lace da ba a dinka ba ta jefawa Kulu.

“Ahhhhh Kai Hajiya duk ni kadai? Alhamdulillah Hajiya na gode na gode, Allah ya kara rufa asiri ya biya bukata, Allah ya kara lafiya ya tsare ki daga duk wani sheri”

“Amin, wani abun kulu ai sai na samu lafiya ma, da yardar Allah idan bukata ta biya zan kyautata miki, ta shi ki tafi kamin Yasir ya shigo”

“Toh Hajiya, amman zan bar leshin a nan saboda idon mutane, sai idan na ga sarari zan zo na karba”

“Dadina da ke wayo Kulu kin iya sirri”

“Gidan na mu ne Hajiya sai da haka, kamin a fara fadar ana ganina bangarenki ”

Hajiya Kaltume ta yi murmushi. Ita kuma ta mike tsaye ta yi mata sallama.

“Mu kwana lafiya”

Kamin ta isa kofar dakin ta bude Yasir ya bude sai dai be shigo ba ya bata hanya ta fita yana amsa gaisuwar da take masa.

“Me ta zo yi nan?”

Hajiya ta nuna masa lace din dake kasa

“Nafisa ta aiko min da lace?”

“Ke kuma?”

Ya tambaya kamar mai shakku, Hajiya dai bata sake ce masa komai ba ta nufi gurin da ta tashi ta zauna da tafiyar nan nata kamar zata yi dingishi.

“A kafa kike jin ciwon ne?”

“Eh gurin da na taba jin ciwo kwanan baya, a nan na sake jin ciwo haka nan kawai sai na ji kamar an tureni na fadi kasa”

“Ko santsin gurinki ne ke janki”

Ya soma duba kafar da ta dan dago masa tana jin kamar ana yanka gurin sai sululi yake mata kamar an watsa ruwan zafi.

“Aa ba wani tsantsi shekara nawa ina gidan nan da can tsantsin be ja ni ba sai yanzu? Turo ni ake yi fa”

“To wa yake turoki Hajiya”

“Yo ina zan sani tun da abu ne na aljanu, amman tabbas ba faduwa ce zallar faduwa ba, turo ni aka yi”

Yasir yayi murmushi tare da kai hannu ya latsa gurin.

“Ban san me yasa ku mata kuke yarda da irin abubuwan nan ba, haka Last week Rukayya take ce min wai ance aljannu ne a jikin Amma, ku dai komai kun fi son ace aljannu ne, wani abun fa daga Allah yake kai tsaye idan ana na asibiti zaki ga an dace, ita kanta Amma da za a fitar da ita waje a dubata duba mai kyau za a gane Matsalarta”

Hajiya ta janye kafarta da sauri saboda lasa gurin da Yasir yake yi.

“Ku kuma ba ku yarda da aljannu ba ko?”

“Mun yarda da su mana, amman ba lallai komai ace su ba, kin ga kafar nan take da zaki iya daurewa mu bari sai da safe mu tafi asibitin, hoto za su miki su duba matsalar”

“Eh haka zan yi, mu hakura da tafiya asibitin nan sai gobe da safe”

“Ba sosai kafar take damunki ba”

“Yanzu dai ta min sauki ba kamaf dazun ba, kai Allah sarki na tausaya wa Iyami gaskiya, a kafa kawai ina jin ciwon nan kamar zan mutu balle ita da ta ke kwance bata iya komai shekara da shekaru, wai har yanzu bata iya tashi da kanta?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected