Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
Zuciyar Amma ta fi aminta da fada suka yi da Hamad shi yasa har ta furta hakan, ganin Hurriya ta fashe fa kuka a lokacin da ta ambace shi.
“Kai Hamad yana da matsala Wallahi sai ace baka iya zaman lafiya fa yan’uwarka, ko tausayinta baya ji”
Rukayya ta fada. Sai Gwaggo ta ce.
“Kusan duk mabiyi da mabiyi haka ake, ba kowa ke shiri da juna ba”
“Amman dai shi nashi yayi yawa”
Amma dai ta yi shiru tana ta saurare numfashin Hurriyya dake fita da karfi..
FAMILY HOUSE…
A rikice Appa ya fito motar tun kamin direban sa ya gama fakin, ya nufi hanyar Falon Hajiya Kaltume cikin tashin hankali, hausawa suka ce ba a saka masa rana. Gaba daya kuka suke cikin falon har Namra da ta shigo. Hajiya Kaltume na ganin Appa ta kara mulmulawa a kasa tana dafa kai ta tashi zaune ta koma ta kwanta kamar wata bayarba…
“Eyyyy Eyyyy Eyyyy ni Kaltume yau na shiga uku yata, wayyo Umm Ruman, Alhaji ina cikin matsala da bala’i sun sace min yar auta, wai ni mi na yi ma mutane ne ne? Wayyo Allah na”
“Haba Hajiya ki yi hakuri mana, idan ke kina haka su kuma yara waye zai rarrashensu? Dan Allah ki tashi”
“Alhaji wasu sun tare mota sun tafi da Ruma”
“Hamad ma yana can hannunsu ai, ba ita kadai ba, kuma In Shaa Allahu zaku dawo lafiya”
“Mutanen nan ba su da imani shi Hamad ai namiji ne, ita kuma mace ce yarinyar yar shawalwala”
Appa ya zauna a kujera ya cire hular kansa duk sanyin ac falon gumi ne ke keto masa ta ko’ina. Salma da Khairi suka fara fada masa abun da ya faru suna kuka ba tare da ya tambaya ba, Kamin ya dago ya bi kowa da kallo.
“Ku daina mana kuka tun da ba mutuwa aka yi ba, ku yi ta addu’a, idan ma wani abun suke so ai dole za su kira. Ina Hurriya?”
Appa na rufe baki Yasir da shigowar falon kenan ya amsa masa.
“Yanzu na kaita gida?”
Appa ya masa wani kallo.
“Gida ina?”
“Gurin Amma tana ta kuka ta ce a kaita can, shiyasa na kaita amman ban shiga gidan ba”
Appa ya dafe kai cike da takaici kamin ya dago ya kalli Yasir yana jin kamar ya mareshi.
“Ban taba sanin baka da hankali ba, sai yau Yasir ka kaita ta fadawa Iyami abun da ya faru kamar baka san halin da Iyami take ciki ba? Ciki ne fa a jikinta kuma tsohon ciki idan ta fadi ta rikice wani abu ya same ta ko ya samu abun da ke cikinta kai zaka mata magani? Wani irin shashanci ne wannan?”
Yasir yayi shiru sai a lokacin shi ma yake ganin abun da yayi na kai Hurriya a irin wannan lokacin be dace ba. Hajiya Kaltume ta fashe da kuka.
“Haba Alhaji wake da Iyami yanzu an dauke min yar shawalwalar yarinyar, mace ce fa, al kara ma Hamad namiji ne”
Appa ya tashi ya fice, Yasir ya bi bayansa, daga gidan station suka nufa daman kamin su isa Appa ya kira CP ya fada masa abun da ya faru, suna isa ya saka aka shigar da report kamin yan sanda da suke sashen kidnapping su tafi gidan aka kwaso duka yaran, ana tambayarsu yadda abun ya faru suna fada. Babban cikin su dake tambayar ya kalli Namra da ta kare nata bayanin ya ce.
“Wacece Hurriya? Ina ita Huriyyar take?”
“Tana gidansu”
“Okay ita ba yar’uwarku ba ce?”
Appa yayi gyaran murya dan ya san Namra zata iya wata kwabar.
“Yata ce, ni na haifeta amma yanzu tana gurin mahaifiyarta da ta koma gida haihuwa”
“To zamu iya ganin ita Huriyyar? Domin ga dukan alama ita aka zo dauka, ita da Ruma din a yadda na fahimta Hamad din tsautsayi ne ya rutsa da shi, rashin samun Hurriyya sai suka dauke Hamad din, dole akwai tambayoyin da nake son yi mata”
“Ni ma na yi wannan tunanin duba da irin labarin da suka ba ni, zan je na zo da ita”
Appa ya fada sannan ya kalli Yasir.
“Idan an gama ka maida su gida, ni zan je na taho da Huriyya”
“To Appa”
Yasir ya amsa cikin ladabi da biyayya, Appa ya ma Officer sallama ya fice. Tare da direbansa suka isa gidan Gwaggo, a waje suka faka motar direban ya fito ya bude masa mota ya fito. A ransa yana son shiga amman jin hake kamar ana tsikara masa allura a zuciya saboda ya doso gurin da Amma take.
“Bala, ka sallamo Hurriyya”
“Toh ranka ya dade”
Malam Bala ya wuce cikin gidan, Appa kuma ya jingina da mota, Malam Bala be dade ba ya dawo yana sanar masa Gwaggo tace ya shigo tana son magana da shi. Rasa yayi me zai ce, shi dai be isa ya juya yayi tafiyarsa ba, kuma yana jin kunyar hada ido da iyayenta ita kanta Amma a yanzu kunyarta yake ji. Haka dai ya daure ya danne duk wani abun azabar da yake ji ya shiga cikin gidan, sai da ya hada da addu’a sannan ya samu courage din shiga har cikin falon Gwaggo. Be zauna ba sai da ya risina ya gaishe da ita kamar yadda ya saba, ba dan ta girme shi ba, sai dai ma shi ya girme ta, yana bata girmata ne tun a lokacin da ta zama sukurukarsa a yanzu ma be yada girmanawarba, domin har a yanzu sun din suna da kima da daraja a idonsa.
“Hurriya ta shigo tana ta kuka, amman bata yi magana ba har yanzu ta kasa fadar abun da ya faru, a baki Rukayya muka ji cewar Yasir ne ya kawo ta ma, kuma da kayan makaranta ta shigo, babu gilashi a idonta, yanzu kuma sai ga Malam Bala ya shigo wai kana kiran Hurriya shiyasa na ce ya shigo da kai ciki mu ji abun da ya faru domin mu ma hankalinmu duk a tashe yake”
“Gwaggo, ni ma kaina ban san abun da ya faru ba. Shiyasa na kira Hurriyar na ji ta bakinta”
“Can gida ba su fada maka komai ba.?”
Appa ya ki yarda su hada ido.
“Ba su fada min ba, Hurriya tana kusa?”
“Eh tana dakin mahaifiyarta, bari a kirata”
Gwaggo ta tashi ta fita. Bata jima ba Iyami ta shigo falo tana sanye da digon Hijab har kasa Hurriya na rike da hannunta. Appa na kallonsa sai gashi ya mike tsaye yana kallon cikin dake jikinta cikin wani yanayi na rashin jindadi.
“Na fada maka babu uwar da zata so yayan wasu kamar nata, yanzu wannan tashin hankali duk na minene? Ba komawa gidanka nake bukata ba kwanciyar hankalin yayana kawai nake bukata a yanzu…”
“Iyami zauna”
Amma har ta yi kamar ta ce masa ba zata zauna ba, domin niyarta ta kawo Hurriya kuma ta jadda masa amanar yayanta ta koma, sai kuma ta zauna domin bata saba musa masa a komai ba. Sai da ta zauna sannan shi ma ya zauna.
“Ba wani abu aka yi mata ba, ki daina saka kishi da son cusa kiyayyar Kaltume ko Nafisa a zuciyar yayanki, ba dukan Hurriya aka yi ba, ba wata bakar magana aka fada mata ba, babu wanda ya mata komai, ba mutuwa aka yi ba”
“To miyasa ta zo tana min kuka? Kuma Yasir da ya kawo ta be shigo gidan ba ya fita?”
“Ni ma shi na zo tambayarta”
Amma ta kalli Hurriya har lokacin hawaye take sai dai ba kamar dazun ba. Ta kalli Appa
“Ina Hamad…!”
Appa ya ji tambayar kamar saukar aradu. Appa ya kalleta ya kasa cewa komai.
“Ina Hamad Appan Hurriya?”
“Dan Allah kin kwantar da hankalinki”
“Kamar ya na kwantar da hankalina? Miye abun tashin hankali a tambayar Hamad? Ko kuma shi ya aikata wani laifin?”
“be aikata laifin komai ba Wallahi, ki ba mu guri zamu yi magana da Hurriya”
Amma ta kalli Hurriya kamin ta mike tsaye ya fice daga falon. Appa ya tashi daga inda yake zaune ya koma kusa da Hurriya ya zauna ya rika yarsa.
“Hurriya”
“Na’am Appa”
“Ki kwantar da hankalinki kin ji, Hamad zai dawo soon da yardar Allah, babu abun da zai same shi, kuma na ji dadin da baki fadawa Iyami abun da ya faru ba, kin ga tana da ciki zata iya daga hankalinta,”
Ta daga kai ta kama hannun Appa ta jimke da karfi.