Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
Ta yi kwafa ta girgiza kai.
“Tabbas na yi sake, da na san haka zai faru da ban tafi gurin wannan bakin bokan ba, gashi Iyami bata mutu ba yata ta mutu Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un, Allah sarki Salma”
Ta fashe da kuka mai karfi tana jin kamar ace zata iya dawowa da ita. Momy ta jero tare da matar Yayanta Hajiya Turai suka nufo bangarenta, Hajiya Turai dake murmushin kasaita ta ce.
“Sakin daya ma ta ya rage zai karasa mata shi nan kusa ki koma ke kadai, ban da rashin sanin darajar kai har yaushe namiji zai sake ka zauna a gidansa wai zaman yaya? Ba sai ta tattara ta koma gidanta ba ta tare, idan ma yana da ra’ayin maida aurensa sai ya same ta a can”
“Ah to ke ma dai kya fada, ai haka na fada ni ma yaya dai da wayonsu ta bar su a gidan ubansu ko ta tafi da su duk daya, ni dai ba zan sake yarda a dauko wahala a kawo min ba, ga Hurriya nan har yanzu ban haife cikin bakincikinta ba”
Hajiya Turai ta dafa Momy.
“Ai kin yi kokari, ni zan iya rika kowa ban da yaran miji, shiyasa kullum nake godewa Allah da ya miji ba mutum ne mai aure aure ba, kin ga da mai wannan kwashekwashen ne da yanzu ya karo aure ko dan haihuwar nan da ta tsaya mana, amman duk be kula wannan ba, gashi yanzu girma har ya kama”
“Wallahi kin huta, daman zuri’ar duk ba mu da wannan rayuwar ta son aure auren mata”
“Allah yasa yaran mu su gado mu”
“Amin, da alama kam Captain ma ba zai yi irin wannan rayuwar ba”
Hajiya Turai ta yi murmushi masu nairori.
“Captain wanda auren farko ma ya gagareshi, ina maganar kari?”
“Na farko ma yana kusa, domin yanzu na lura kamar hankalinsa ya karkata gurin Namra kuma sai dai mu saka musu ido mu ga gudun ruwansu kamin mu ga abun da Allah zai yi”
“Oh yanzu na gane dalilin da yake fada min cewar na kusa samun suruka, amman be fada min ko wacece ba, har nake ce masa ko da ka jitu da ita ai abun baya daurewa, sai ya ce min wannan kam idan har na ga be aureta ba to baya raye, amman ko naman jikinsa take yanka ba zai rabu da ita ba”
Momy ta yi murmushi zuciyarta na kara jaddada mata Namra ce.
“Toh Allah yasa, zaman da yake a garin nan yanzu gaba daya hankalinsa yana gidan nan komai aiki yayi masa yawa sai ya leko gidan nan”
“Aiko zan jidadi idan haka ta faru, daman abun da muke fata kenan, wata kila idan ya dawo daga tafiyar nan zai gabatar min da ita”
“Tafiya yayi?”
“Eh tun last week yace zai tafi Abuja?”
“Oh Allah sarki daga Kaduna ya wuce Abuja? Aikin na su ne ba zama”
“Aa be zo Kaduna ba, daga nan Gusau ya wuce yace min sati daya zai yi”
Momy ta jingina jikin Range Rover din aka tuko Hajiya Turai tana mamaki.
“Ni kuwa ce min yayi Kaduna zai tafi”
“Aa gaskiya Abuja yace min, tun last week jiya ma da muke chat da shi yake ce min ya kusa dawowa”
“Wata kila kuma ban ji daidai ba, ko kuma an canja tafiyar tasa ce daga Kaduna zuwa Abuja”
“Maybe”
Daga haka suka yi sallama da Momy, Dreban ya bude mata mota sai ta shiga ta zauna ya rufe Momy ta daga mata hannu ya ja motar. Momya ta shigo falonta ta samu masu aikinta na kwashe kayan da suka ajewa Hajiya Turai bata taba ko daya ba.
“Kar a taba komai aje su a kitchen”
Kulu ta amsa da sauri.
“Toh Hajiya”
Momy ta haura stairs ta shiga dakinta, wayarta ta dauka tana murmushi maganar da Hajiya Turai ta fada mata cewar yace ta samu suruka ya faranta mata rai. Akan haka ne ta gwada kiransa ta ji lafiyarsa a yau domin tun da ya tafi bata kira shi ba, sai dai tana magana da shi ta chat kamar yadda mahaifiyarsa ma tace. Sai da tana kiran sunan sai kiran ya yanke alamar ba za a iya samunsa ba.
“Wata kila yana gurin da babu network ne”
Ta furta kana ta bude data ta shiga whatsapp dinta ta duba last chat dinsu two days sai ta aje masa sako tana murmushi.
“My Son, ya aikin na ku? Hajiya Turai tace min Abuja aka kai ku ashe, amman baka fada min ba, Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya”
Tana kokarin aje wayar reply dinsa ya shigo bata san yana online ba sai a lokacin.
“Amin Momy na kusa dawowa jibi nan, Ammy ta zo kenan?”
“Eh kasan idan ta shigo Family House bata barin garin nan sai ta biyo gurina, ta fada min albishir din da aka yi mata muna fatan jin labari mai dadi”
Ya turo mata emoji din murmushi sannan ya aiko mata da sako.
“Za ku ji ba da jimawa ba Momy. Hurriya tana lafiya Momy?”
“Hurriya???”
“Na dauka zaka tambayi Namra ne”
Ya turo mata murmushi shi dai yana kokarin isar mata da sakon zuciyarsa cikin hikima tun da har ta fada masa Ammynsa ta tsegunta mata wani abu a kansa.
“Duka daya ne Momy”
“Aa ba daya ba ne, Namra yar ‘uwarka ce jininka zaka iya juyata yadda ka ga dama ka tambaye ta ko ka saka ta yin wani abu, amman Hurriya baka da alaka da ita”
“Alakar musulumci ta fi ta jini”
Momy ta kashe data ta aje wayar da mugun mamaki a fuskarta. Kar dai ace abun da Namra yake hasashe ya tabbata kar dai ace Hurriya yake nufi da yarinyar? Idan ba haka ba me ya kawo zancenta a yanzu. Ta sake daukar wayarta ta bude data ta masa reply.
“Haka ne, amman ina son ka sani babu wata alaka tsakaninka da Hurriya, ya kamata ka sani matsayinku ba daya ba”
Wannan karon bayan ya karanta be sake ce mata komai ba har ta gaji ta aje wayar ta mike tsaye fice daga dakinta. Dakin Namra ta shiga sai ta same ta kwance kan gado tana waya.
“Aje wayar nan ina son magana da ke Namra”
Namra ta tashi zaune tana kallon Momy da already ta zauna gefen gadonta.
“Me ya faru Momy?”
“Tafiyar da Hajiya Turai ta yi a yanzu ta fada min wata magana da Captain ya fada mata, na yi zaton da ke yake, sai dai a yanzu da na ke chat da shi sai ya ke tambayata ina Hurriya?”
Namra ta yi murmushi.
“Ai na fada miki Momy baki yarda ba”
“Ba wai yarda ne ban yi ba, ina ganin dai kamar Captain ba zai tsaya kula yarinya irin Hurriya ba”
“Saboda me? Ga alama ya bar mana kamin ya tafi? Kuma shi Captain ba irin rayuwarku ce da shi ba, be cika duba arzikin gidansu ba”
“Ba zan bar wannan ba”
“To ya zaki yi Momy? Ba ayi ma Captain dole kuma iyayensa suna son farincikinsa fiye da na su babu wani abin da zamu iya yi”
“Iyayensa sun fi ni kyamar talaka, kuma Hajiya Turai ta san yadda nake da Hurriya dan haka ba zata yarda danta ya aure ta ba, bana ma tunanin auren zai yiyu domin Captain baya iya jure komai, daga yanzu ina son ki yi duk wani abun da zaki dauki hankalinsa ki kwantar masa da hankali ita kuma zan yi maganinta na san yadda zan yi da ita”
“Momy ni fa ba zan cusa kaina a gurin namiji ba, idan har zan yi haka miye amfanin amsa suna na mace? Idan yana ra’ayi shi zai kawo akansa a gareni, ba wai na shige masa na nuna masa so ba?”
“Baki son sa ne? Ko kin manta burin da muke da shi akanku? Yanzu ma sai da mahaifiyarsa ta ce zata fi kowa farinciki idan hakan ta faru tsakaninku, haka kika yi saka har ta yi nasarar raba ki da Salim yanzu kuma haka zaki zuba mata ido ta rabaki da Captain? Karamar yarinya kamar Hurriya?”
Namra ta sauke ajiyar zuciya.
“Momy idan yana ra’ayina shi zai kusanto da kansa a gareni kamar yadda yake kusantar da kansa gurin Hurriya”
“Take dai jan hankalinsa, saboda ta fiki wayo da iya kisisina, ki zauna nan kina tunaninki na banza da shirme”
A fucewa Momy ta mike tsaye ta fice daga dakin, cikin kufula da fusata ta tura kofar dakin Hurriya ta shiga.
“Ke…!”