VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

CAPTAIN POV.

Ammy ta aje tea cup din dake hannunta tana kallon danta.

“To waye kuma da wannan aiki?”

“Za mu gane,  kuma ko waye sai ya dandana kudarsa”

“Ko yar’uwarta ce?”

“Bana tunanin haka, saboda asirinta ya tonu, kuma bana jin Adam ne domin  ya fada cewar ba shi ba ne ko a yanzu!”

“Ko ma dai waye ya kamata a hukunta shi a yanzu, domin ya wuce gona da iri kuma ba kai kadai ne da fadan ba har da na mu domin idan hotunan suka sake yaduwa har da mu za a taba”

“Mutum daya nake zargi.”

“Waye”

“Bana son fada, amman gaskiya zata yi halinta, and if i find out shi din ne, zan masa ba dadi”

“Zan yi magana da aka daddynka san fada masa a zafafa bincike ta bangarensa ma ko zamu samu wani abu, and ka kula da gidanka domin  wanda zai iya yi ma Iyalinka haka zai iya neman rayuwarka ko ta matarka ko ma ya sake yin wani abun da zai zubar da kimarka, gashi yarinyar ba gani take ba be ma kamata a barta ita kadai a gidan ba”

“Na barta ne just for today and tomorrow saboda masu zuwa, amman bayan nan idan zan fita nan zan kawo ta sai idan na dawo sai na dauke ta mu wuce”

“A madadin haka ka rika kaita a gidansu mana ko kuma ka dauki mai kula da ita tun da ka ji ka gani zaka iya”

Ya dan yi murmushi.

“Nan din ma gidansu ne ai saboda gidanmu ne, Ammy kina son yarinyar nan fa ki daina boyewa”

“Au boyewa nake ma?”

“Idan ba shi ba, miye na danka mata key mota? Duk soyayya ta dake fa baki taba siye min mota ba, amman ita gashi kin siya mata sabuwa, sannan kika bada kayan bikonta”

“To ya zan yi? Na yi abun da ya kamata uwa ta yi ne, ba ni da wani zabin ne”

Yayi dariya sosai yana kallon mahaifiyarsa cike da farinciki.

“Ni dai tarewar ne a haka be min dadi ba, da dai ka hakura har idon ya bude da abun ya fi armashi gaskiya”

“A yanzu din ma babu abun da ya ragu Ammy, ina farinciki da matata kuma ba wai bana son duba idonta din ne a yanzu ba, akwai planning din da nake, ina son nan da two years….”

“What…! Baka da hankali ashe..!”

Ya dan bata fuska.

“Ammy ni?”

“Taya zaka auro yar mutane ka ajeta har nan da two yrs sannan a duba idonta? Wane irin plan ne wannan? Hummm uhmm you better not, karka kuskura gwada wannan, iyayenta ba za su yarda ba ai”

“Karkashin ikona take yanzu”

“Haka ake aure a garinku? Dan tana karkashin ikonka iyayenta ba za su yi mata abun da ya dace ba, gaskiya be kyauta ka ajeta a haka har two yrs ba ai sai ta wahala kara dai a gwada idan ma ba a dace ba ansa ba a dace ba ne amman ba wai haka nan kawai ba”

Yayi murmushi ya taso daga inda yake zaune ya zauna kusa da uwarsa.

“Kin gani ko Ammy kina son yarinyar nan Wallahi gashi kin damu da ita…”

“Ni shawara ce kawai nake baka, idan ta ni ne ka barta har sai nan da shekara goma ma babu abun da ya dame ni”

Side hug yayi mata yana dariya.

“Ammyna i love you so much…”

Ta yi murmushi kadan tana tabe baki.

“Ka ji da shi, ku yaran zamani sai dai abi yadda kuke so ba yadda iyaye suke so ba”

Ya sake yin dariya ya mike tsaye ya fice daga dakin, haka ya fito harabar gidan ya gaisa da mutane cousin dinsa mata suna ta tsokanarsa. Sai da ya shiga motarsa sannan ya kira Nafi’u ya aika masa da wata number.

“So nake ka yi min hacking din account din da yake jikin number nan, ka duba duk wani abu da ke cikin chat din maybe zamu samu wani abu da muke nema, ka yi duk yadda zak iya ka duba komai na account din”

“Okay ranka ya dade”

****     ****     ****

A WEEK da bikin auren Hurriya Amma da Gwaggo suka tafi Ummara tafiyarsu da kwana biyu Momy ta tafi tare da babbar ƴar Appa wato Sapna Momy kuma ta biyawa yarta Namra suka tafi tare duk kuwa da kasancewar ta taba zuwa ba sau daya ko biyu ba. Hakan kuma ba karamin taba ran Hajiya Kaltume yayi ba, a nan ta fara shige shigenta ko zata samu kamin Momy da Amma su dawo Appa ya daura aure da ita kuma ya juyawa Momy da Amma baya, amman yi take kamar tana shuka dusa, ga ciwon kafa ya sakata gaba amman ta kasa tsayawa ta maida hankali gurin neman lafiyarta kokarinta na yadda zata koma karkashin inuwar mijinta ne a yanzu.  Bata da wani buri da ya wuce wannan kuma duk inda zata saka kafa ta gabatar da bukatarta za su karbi kudinta su ce za a mata aiki mai kyau kuma Appa zai juyo ya nemata haka ma aurensa da Amma ba za a maida ba. Babu abun da ke daga mata hankali a ciwon kafarta nan kamar yadda idan an bincika ake ce mata babu wani rauni ko wani ciwo a gurin amman kuma ita tana jin azabar ciwon da ko tafiya bata iya yi daidai yanzu. Tana shan wahala sosai gurin hawa da saukowa a stairs har bata son yin ko daya sai idan ya zame mata dole. Yau ma kamar kullum ta sauko tana ta wai wai wai da kafar har ta zauna. Yasir yayi saurin yanke wayar da yake ganin Hajiya ya aje wayar gefe ya maida hankalinsa gurin tv.

“Me kake ayi nan? Yau baka da aiki ne?”

“Ina da aiki sosai ma Hajiya, gyaran gidan da Appa yace za’ayi ne mutanen nake jira su iso”

Wani kallo Hajiya Kaltume ta yi masa na rashin zato balle tsammani.

“Gyaran gida za’ayi? Ba mu da labari”

“Ni ma ban sani ba, kawai ya kira ni yace min na jira kar na fita da wuri so that idan sun zo na nuna musu lungu da sako na gidan”

“Ikon Allah to gyaran gida na minene? Na ga dai ko auren Hurriya ba’ayi gyaran gidan nan ba, baka fada min shi yasa aka gyara gidansu Iyami ba? Amman ba a gyara nan ba, to yanzu kuma gyara me za’ayi”

“Wallahi ban sani ba Hajiya, kin san ba komai ne Appa yake shawara da ni ko ya sanar min ba, amman dai ko minene ai zamu ji”

Hajiya Kaltume ta sauke wani dogon numfashi tana jin wani sabo na tukare mata a kahon zuciya.

“Ya kafar taki?”

“Da sauki”

Ta amsa irin amsawar dake nuna hankalinta baya gurinsa.

“Da dai kin daure kin fita a duba kafar nan kar abu ya zame miki babba fa, Appa ma na ji yana zancen yana son fita a duba lafiyarsa shi da yake lafiya ma kenan balle ke da ciwon kafa ya matsawa ya kamata a bincika ko minene”

“Zan yi Yasir akwai abun da yake gabana yanzu, ina son na gama da shi ne tukuna”

“Minene Hajiya?”

“Be shafe ka ba”

Ta mike tsaye cikin jan kafa da dingishi ta sake haurawa sama ta shiga dakinta zuciyarta har rawa take kamar zata fado. Ta zauna bakin gadonta ta rasa me zata yi kuka ba mafita ba ne, to miye mafita, yanzu tana ji tana gani Amma zata dawo gidan nan?  Ko kuma dai sabon aure Appa zai daura.

“Na shiga uku na lalace..”

Ta fashe da kuka. Ta lalabo wayarta ta kira Number sabuwar kawarta Hajiya Larai dake ke karata gurin masu magani a yanzu.

“Subhanallahi Hajiya kamar fa kuka kike yi..”

“Ba dole na yi kuka ba, ciwo ya dame ni ga kuma auren nan Alhaji jin sa zai yi ko kuma ya maida iyami abun duniya ya isheni Hajiya Larai, kullum sai ramewa nake ga ciwo ga bakinciki”

“Komai zai warware Hajiya Kaltume karki damu kanki, kin ga duka malaman nan da na kaiki gurinsu sun iya aiki babu wasa babu kama hannun yaro kuma tun da aka yi musu biya mai kyau ki saka ido zaki ga yadda komai zai tafi daidai”

“To ai abun ne kullum shiru Hajiya Larai abu sai kara gaba yake, yanzu fa har Alhaji ya saka ayi masa gyaran gida, ni dai ina tunanin ko zan bo ta bangaren Hajiya Binta ne idan na je yi mata barka da dawo na bata hakuri ko abubuwa za su daidaita, wani abun fa dole sai ana saka baki”

“Karki kuskura zubar da kimarki Hajiya Kaltume da yardar Allah sai Alhaji ya zo yana kuka yana neman yafiyarki”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected