Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Zan kiyaye Daddy amman baka san Salim ba ne ya… ”
“I don’t care what Salim did to you, ko zaginka yayi be kamata ka yi wasa da rayuwarsa ba, be kamata ka nuna rayuwarsa bata da muhimmanci a gareshi ba, hankalin mahaifiyarka ya tashi wane irin abu ne wannan?”
“Yi hakuri Daddy”
Yadda Daddy ya kashe wayar kadai ya isa ya bayyana maka har lokacin ransa a bace yake, abun da Captain yayi kokarin aikata laifi ne babba a dokar kasa kuma laifi da zai iya sakawa a hukunta mutum ko a koreshi daga aiki ma a dokar aikin soja, idan ma ace ya aikata matsalar su zata fi shafa fiye da Captain din. Kansa ya dafa ya runtse ido ya bude shi kansa yayi nisa abun da ya aikata a gaban mahaifiyarsa a yau, be taba aikatawa wani haka ba sai Salim kuma shi ne karo na biyu, haka yake jin kamar ba zai iya rike kansa ba a duk lokacin da wata magana marar dadi ta fito daga bakin Salim zuwa kunnensa akan Hurriya. Tashi yayi ya nufi hanyar dakin da mahaifiyarsa take sai ya same ta zaune ta kifa kai da guiwa tana kuka. A take hankalinsa ya tashi daman kukan uwa shi ne tashin hankalin ko wane ďa na gari, ya duka a kusa da ita yana kallonta idonsa har sun fada tsabar tsoron da ya kama shi.
“Ammy lafiya… Kuka kuma? Me ya faru?”
Ta dago ta kalleshi hawaye na zuba a idonta.
“Zuciyarka tana ba ni tsoro ni ba zuciya ba, mahaifinka ba zuciya ba kai ban san a ina ka dauko wannan rayuwar ba, ban san me zaka aikata a gaba ba, idan babu kowa wata rana zaka iya kashe wani, zuwanka garin nan ya bata abubuwa da yawa na farinciki na Jamal, soyayyarka da yarinyar nan ya lalata akala da Hajiya Nafisa a yanzu, saboda tana ganin zan iya cilasta ko kuma na yi fadi tashin hana tarewar nan amman na gaza, Namra muka so ka aura Jamal ba Hurriya ba, idan ba zaka so ta gida ba ka nemo ta waje mai mutunci mana ba wannan ba, yanzu kokarin tarewa kake da ita, ka bata da abokinka kuma nuna shi da gun miye amfanin haka? Duk akan yarinyar nan fa”
Zaunawa yayi a gurin ya nade kafafuwansa ya duba mahaifiyarsa duba na tsanaki.
“Mutum baya aure sai matarsa Ammy ya kamata ki gane wannan, Allah ya rubuta ni da Hurriya zamu yi aure ko duk duniya za su taru ba za su iya tare wannan ba, zuwan da nake a gurin Momy ban taba zuwa saboda wata rana rana na so Hurriyya ba, haduwata da ita wani abu da Allah ya kaddara domin ban san da ita a gidan ba har sai da Mahaifiyarta ta fita, na san akwai yayan mijinta amman ban rike fuskar ko daya ba, Ammy ya kamata ki duba wani daura auren da aka yi ma bada sanina aka yi ba, amman duka Allah ya rubuta faruwarsu, farkon haduwarmu da yarinyar mari ne, na mareta da hannuna saboda ta taba ni ba ta gani ba, daga lokacin da Namra ta fada min bata iya gani sai da gilashi sai ta ba ni tausayi, ban tabbatar da ina tausayin yarinyar nan ba sai ranar da na je zan shiga dakin Momy da kunne na ji yadda take magana da Hurriya akan cewa zata musgunawa yarinyar nan kuma ba tare da ta mata komai ba, su kan hana ta abinci wani lokacin sai da taimakona take samu ta ci, kamin zuwa yanzu mahaifinta ya tsane ta aka kashe dan’uwanta ta koma bata da kowa a gidan Allah, ga mahaifiyarta ba lafiya, and now aka yi mata wannan abun yanzu a haka Ammy duk bata ba ki tausayi ba?”
“Ta ba ni, amman ai bata dace da kai ba, ina magana ne akan dacewa”
“Ta ina kike ganin bata dace da ni ba?”
“Baka ga yadda hotunan suka yadu a duniya ba? Kuma bata gani”
“Rashin gani kar ya dame ki, ina da wani yakini cewar Allah ba zai kunyata bawansa ba, da yardar Allah idon Hurriya zai bude, yada hotunanta kuma ba ita ta aikata ba aikata mata aka yi saboda a bata mata suna, kuma an yi nasara tun da gashi matar da ya kamata ace ta fi kowa kaunarta ta tsane ta, abun da zai baki mamaki ma yar’uwarta ce ta aikata mata abun Ammy, hakan ya nuna yarinyar nan tana fuskantar kalulabe na rayuwa kala kala, ke kuma kina kara taya Momy kishi ne kawai shiyasa kike tsanar Hurriya da yawa, na tabbatar da Namra ce haka ta faru da ita Momy ba zata so na guje mata ba haka ne?”
Ammy ta daga kai.
“Amman saboda Hurriya ba yarta ba ce shiyasa take fushi dake ni ma take yi da ni, a gabanki ta fadi cewar laifi ba nawa ba ne ni kadai har da Daddy, saboda tana ganin ya aura min yar kishiyarta ya bar yarta”
Captain yayi shiru na dan lokaci idonsa na cika da hawaye.
“Wallahi Wallahi Wallahi Ammy ban san dalilin da ya saka nake kaunar yarinyar nan ba, ni dai kawai Allah ya saka min kaunarta, ina jin farinciki a tare da farincikinta ina jin damuwa a tare da damuwarta, idan wani ya tsane ta ina jin kamar ya tsani cigaba ne, ita kadai ce yarinyar da nake jin zan iya jure duk wani abu da ya shafe ta, zan iya daukar duk wani zagi da suka a duniyar nan, ban sani ba ko a nan gaba zan gane kuskuren hakan, amman a yanzu bana jin son kowa sai ita, shiyasa na kan kasa auna abun idan an tuna duk kaunar da kike min matsayinki na uwa kin tsani wandda nake so, to ina zan kama Ammy? Wani lokacin ina jin tsoron kar yarinyar nan ta dawo a gidana matsayin matata ki musguna mata ko ki wulankatata, kamar ni kika yi ma, na san ba zaki yi fatan danki ya wulakanta yar mutane ne balle ke kanki ki wulakanta matata Ammy ban taba tunani ba, ko da ace Hurriya tana aibu na yi tunanin zaki boye saboda kar na ji raina ya bace, amman ke da kanki Ammy kike yakar yarinyar nan? Kina fadar yadda zaki yi idan aurena ya zo yau duk kin kawar da wannan saboda Hurriya ce, a gabanki abokina yake zagin matata saboda ya samu fuska a gurinki Ammy, kina fada min irin kaunar da kike min kina gudun bacin raina amman yau babu wannan… ”
Tuni hawayen Ammy suka kafe a idonta ganin ďanta yana kuka, bakinsa na furta kalaman dake kama kwakwalwarta.
“Kuka kake yi Jamal…? Hawaye kake zubarwa?”
Ya kawar da fuskarsa gefe.
“Ammy ya yadda kika san zuciyata, tun da kika ga na shanye duk abun da aka yi ma Hurriya na kaunace ya kamata ki fahimci yadda tasirin sonta yake da karfi a zuciya, Ammy a yau zan miki rantsuwa da Allah na tabbatar miki da abun da kike da muradi… Wallahi Wallahi Wallahi Ammy idan fasa auren nan ne farincikinki, zan hakura da Hurriya Wallahi ba zata tare a gidana ba a matsayin matata zan hakura da ita! Amman tabbas zan roko Allah ya dauki rayuwata, na fi sha’awar mutuwa fiye da rayuwa babu Hurriyya a matsayin Matata…! Ko da na mutu zan tafi da tunanin wannan abun… ”
“Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un”
Ammy ta furta tashin hankali na kwance a idonta ta rika fuskar Captain da duka hannayenta sannan kamin ta tashi ta rumgume danta tilo daya tana hawaye.
“Abun be kai can ba, be kai can ba…”
Ta dago ta kalli fuskarsa ta sake rumgume danta.
“Wannan irin so da kake yi ma yarinyar Allah yasa ta zame mata ƴa, wannan son ya ba ni tsoro”
Tsoro ba a furucinta kadai yake ba har a cikin zuciyarta yake, domin Captain be taba zaunawa da ita gaba da gaba ya karabta mata soyayyar wata mace da karfi kamar yadda ya yi mata a yau ba, a yadda zuciyarsa take idan ya rasa zai iya jefa kansa a cikin wani hali wata kila fushinsa da zuciyarsa su karu har aikata abun daba shi ke nan ba, wata kila kuma idan yayi addu’ar ya amsa masa ya tafi ya barta da bakincikin rasa ďa ďaya tilo da Allah ya bata, da bakincikin kin abun da yake so, idan kuma hakan ta faru ta san ba zata yafewa kanta ba, Daddy ma ba zai daina ganin bakinta ba.