Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Ku bincika min ko’ina na dakin nan, ku duba min sarkar Namra da tawa da kuma kudin”
Hurriya ta mike tsaye da sauri irin mikewar nan kamar wanda aka lakawa wutar nepa.
“Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un, ni kuma? Momy ni…? Momy ban taba ba, Wallahi ban dauka ba, Momy ban zan miki haka ba”
“To waya aikata? Da zan fita waye na bari a bangaren? Waya shigo ya dauka?”
Hawaye ya fara mata zuba.
“Ban sani ba Wallahi amman ban dauka ba, ban taba sata ba Momy ko tsintuwa ban taba yi ba, balle har na shiga dakinki na dauki kudi ko sarkar zinari, dan Allah karku min haka, idan baku son zama na a gidan nan ku kure ni amman dan Allah karku laka min abun da ban yi ba”
Namra ta ta yi saurin rika Hurriya dake kuka kamar zata narke.
“Momy da dai an zafafa bincike Hurriya bata taba daukar abu ba, kuma a jininmu babu barawo”
“To waya dauka? Shekarata nawa da masu aikin nan balle har ace su suka yi”
“Haba Momy taya zaki shaidi bari ki bar na gida, Wallahi Hurriya ba zata dauka ba”
“Ke fice ki ba ni guri, ba ke da bakinki kika fada min Hurriya ta tambaye ki kudi ba? Kuma su ma sai na saka an duba dakunansu ai sai an bincika ko’ina na gidan nan”
“Eh amman bana jin Hurriya zata aikata haka Wallahi, kuma wannan ai na dabam ne, a maganar da na yi miki na ni na fi zaton ko zata siye anko ne ko wani abu dabam”
Momy ta watsawa Namra wata kalar harara da ke karantar da ita ranta yayi kololuwar baci, ita kuma zata iya bata nata rai a take. Ganin haka ya saka Namra sauka ta kira masu aikin, Momy na tsaye aka fara binciken dakin Hurriya tana ta kuka, sai da aka daga komai aka bincike har kwalin da Adam ya kawo mata sai da aka bude ba aga kudi ko sarka ba.
“Wato har da soyayya kike da wani a boye ko?”
“Aa aa aa sako ya kawo min, na je bangaren Hajiya na karbo kuma ban san zai aiko da sakon ba”
Ta amsa daker tana kuka sosai.
“Oh to ke kika bar min kofar daki a bude kenan aka dauka min sata, ko kuma kika sata”
“Na ga kofar a bude lokacin da na dawo kuma ban ga kowa a falon ba, amman Wallahi ban dauka ba”
Still Momy bata yarda da ita ba saboda tana ganin ita ma ai talaka ce kuma mabukaciya saboda halin da Amma take ciki, kuma gashi Appa ya daina kula da ita.
*I know littafin nan zai fito, i know zai yi yawo har ya iso gareki. Na fada kuma zan saki repeating Wallahi duk wanda ya karanta min littafi ba tare da ya biya ba, na barshi da mai mafaɗar rana da fitowarta. Daga masu sharing har masu karantawa ba tare da biya ba na barku da Allah…!*
Yadda Momy ta saka aka bincike dakin Hurriya haka ta saka aka bincike, dakunan masu aikinta, a nan ma ba a samu sarka ba, ba a samu kudi ba. Daga nan kuma sai labari ya canja Momy ta fara zargi ko Hajiya Kaltume ce ta aiko aka shigar mata daki saboda ta aiko kiran Hurriya, a karfin hali da nuna isa irin na Momy ta aika da masu aikinta kai tsaye a bangaren Hajiya Kaltume wai su bincike mata komai na bangaren saboda an dauke mata sarkar zinari mai tsada da kudi mai kauri, a nan Hajiya Kaltume ta fara nata masifar ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, ita da Khairi, har Yasir abun be masa dadi ba ganin an lakawa mahaifiyarsa sata. All this while kuma Hurriya na dakinta tana rusar kuka abun ya zame mata biyu ta rasa gurin jin sanyi, domin ta san a yadda mahaifinsa ya tsane ta yanzu zai iya yarda ta dauki kudin, gashi bata san yadda zata yi ta fidda kanta ba, secondly ga gift din da Adam ya aiko mata ta san Khairi sai ta fadawa Appanta. Kuka take sosai kamar ranta zai fita gaba daya ta gama fita daga hayyacinta tunani ma ta rasa wanne zata yi.
9:30pm Appa ya aiko kiranta bayan kowa ya hallara a falonsa, cikin matukar tsoro da firgici ta fito daga bangaren Momy tana tafiya kafafuwanta na yin kamar za su zameta. Hankalinta be kara tashi ba sai da ta shiga falon ta ga kowa yana nan ciki har da Yayanta da Hajiya Kaltume mai karawa miya gishiri, ga kuma Momy da ta rumgume hannaye ta hakimce babu alamar sassauci a tare da ita, sanin kanta ne a yanzu babu wanda zai wanketa domin babu mai kaunarta a gidan, kuma bata da tabbacin za su shaideta, dan haka ta bi shawarar dake karya mata zuciya. Idonta yana a gurin mahaifinta tana kallonsa zuciyarta na rawa kalaman da za su fito daga bakinsa kawai take saurare. Sai da ta zauna kusa da Ruma sannan Appa ya dubeta duba na tsanaki ya ce.
“Hurriya ina son ki fada min gaskiya, na san baki taba min karya ba, kin shiga dakin Nafisa a lokacin da ta fita ko dakin Namra”
“App…”
Ta kasa karasa furta sunansa ma saboda kukan da ya ci karfinta, hawaye kam ko kai waye sai ka tausaya mata yadda take zubar da su.
“Kin shiga”
“Ta girgiza kai”
Sai Hajiya Kaltume ta kada baki ta ce.
“Ai fa akwai iya kukan kamar yar drama, ba a dai taba sata a gidan nan ba sai yanzu, kuma babu wanda yake bangaren nan sai ke, sai dai kuwa masu aiki, ko da yake bari na rufe bakina ai ita wannan yar karuna ba a mata gwaninta, ni ma bata raga min ba ni din ma da na fi karfin shekara biyu rabona da kofar falonta”
Momy ta dago tana harar Hajiya Kaltume ta ce.
“Kwarai kuwa, a gidan nan ba a shaidar kowa, domin kowa shegen kansa ne, rufin asirin da Allah yayi min na san ai tsonewa wasu ido”
Hajiya Kaltume ta nunata da hannu.
“Ina arziki yake? Me kike da shi Nafisa? Babu abun da Allah ya baki wanda be bani ba, zan iya siye abun da kike siye to miye zai saka ma na aika a dauko min wani abu dakinki saboda gaki diyar Bill Gates ko?”
“Karya kike yi Wallahi, ki ce me nake da shi, ai ke kin san na fi karfinki sai gani sai hange, ni ba irin Iyami ba ce, ahe”
Appa ya daka musu tsawa rai a bace.
“Miye haka wai? Na taraku a nan ne saboda ku fara sa’insa? Musamman ma ke Nafisa kin fi kowa fitina a gidan nan, na fara gajiya da matsalalolinki”
“Allah ya raba ni da matsala, ka ga Matsala can”
Ta nuna Hajiya Kaltume sannan ta cigaba.
“Kuma daman ai dole ka ce ni ce mai fitina saboda ita wa’eh ta mallakeka baka ganin kowa sai bakar kaza, daman idan ta shiga akurki bata barin kowa ya shiga, idan ka gaji da matsalolina sai ka san yadda zaka yi da ni, amman ina mai tabbatar maka zama daram dam dam dam, domin babu inda zan tafi na barwa wata makira yar kasan wuta ta samin hannu a yaya”
Khairi ce ta yi karaf ta ce.
“Momy ba dai Hajiyarmu ce yar kasan wuta ba Wallahi sai idan ke”
Tana rufe baki Namra ta mayar mata da martanin.
“Ba dai Momy ba, sai dai ke Khairi yar shaye shaye kawai mai banzayen abokai”
Appa step on his feet ya sake daka musu tsawa sai da falon yayi tsif.
“Ku tashi gaba daya ku fice min daga falo, saboda kun raina ni, ku yi sa’insa a gabana yaranku ma su yi ko? Toh wannan ya zama na karshe, kuma daga yau sai yau kar wanda ya sake dorawa yata sata, ni na haifi Hurriya ko mahaifiyarta bata fini sanin halinta ba, Hurriya ba zata yi sata ba, Nafisa ki tafi can ki nemi wanda ya shiga dakinki ya dauki sarka da kudi, ki bincike masu aikinki amman Hurriya ba zata aikata haka ba, duk abun da nake yi ma Hurriya ina mata ne ba dan bana kaunarta ba, kuma haka ba yana nufin kowa ya kwaso shararsa ya watsa mata ba”
Ya kalli Hurriyya With Angry face.
“Hurriya tashi ki yi tafiyarki”
Hurriya bata san lokacin da wani sanyi ya ziyarci zuciyarta ba, hawayen da suka banbanta da na dazun suka zubo mata. A nan kam ta samu courage din yin magana.