Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Aa ko kadan, karin aure al’adarta ce, kamar yadda take al’adar Malam Bahaushe kuma Sunna, ko da iyami tana cikin gidan nan zan kara aure, shiyasa na yi bangare hudu ba biyu ko uku ba, ko Iyami na nan ko bata nan wannan abu ne da zan yi kuma ba dan kun gaza a komai ba”
Ta saka kuka.
“Amman Fisabilillahi ka rasa wa zaka aura sai karamar yarinyar sa’ar Salma? Ko kunya ba zaka shi ai sai mutane su ce maka mai budurwar zuciya, haka ka yi min daga kawo Iyami aiki a gidan nan ka yalla ido ka aureta, ka saka a unguwa da dangi sai labarina ake yi”
“A cikin mutanen da zasu zage ni, akwai mai ba ni naira biyar na kara gurin aikin? Ko akwai wanda na tafi neman abun da zan ciyar da Iyalina a gurinsa? Kaltume wannan kishin fa ba naki ba ne, ina ce idan za’ayi ta uku ta biyu aka yi ma, idan za’ayi ta hudu ta uku aka yi ma, ki bar Nafisa ta yi wannan fadan, kuma aure fa ba zan fasa ba, burina ne aurin mace hudu kuma sai na cija wannan burin da yardar Allah”
“Alhaji dawo zaka yi da Iyami kenan? Kuma ka kara aure?”
A take Appa ya fusata a yanzu kam ta kai shi kul.
“Idan zan dawo da ita akwai wanda zai hana ne? Me ye matsalarki da Iyami ne wai? Ta bar gidan amman bata fita a bakinki ba? Ban san wani abun da ta yi miki ba bayan alheri, amman kin dauki karan tsana kin dora mata, matar da lafiyar jikinta ma bata wadace ta ba, ba a aure aka haife mu? Ko kuma ba a aure ni na aureki? Kina da yaya shekararmu nawa tare da ke, to miye matsalarki da karin aure, idan mata dari zan aura miye matsalarki da hakan? Akwai abun da na rage ki da shi? Ko kuma da kudinki zan kara auren? Ke ce babba amman kullum ke ce mai fitina ta, na fara gajiya da hallayenki nan Kaltume na fara gajiya, daga ke har Nafisa idan ba zaku gyara ba to ko tabbas abun da ya ci Iyami zai ci ku, ita din ma da bata min komai ba balle ku da kuke neman haddasa min fitina”
Ya sauke kafafuwansa ya saka talkaminsa cikin bacin rai ya nufi bandakinsa. Kallonsa ma Hajiya Kaltume bata yarda ta sake yi ba, balle ta furta masa wani abu, gaba daya jikinta yayi la’sar, a take ta shiga sake-saken zuci tana neman bakin zaren lamarin.
‘Yau ni Alhaji yake fadawa haka? An samu matsala kenan, wata kila Malam ya fara karya aikinsa ne shiyasa Iyami ta fara tashi? Kuma Alhaji ya fara son wata bayan ya min alkawarin babu waa a zuciyarsa da yake so yake jin tsoron bacin ransa fiye da na uwarsa kamar ni? Saboda yana somu yi min milkin mallaka irin na Hajiya fatee, ni ko ba zan yarda ba, wata kila kuma Iyamin ce ta dukufa a wasu safgogin tun da gashi har yana tunanin dawowa da ita, ko kuma dai wannan fitinannniyar yarinyar ce da zai aura ce ta fi ni iya shiga da fita? Shiyasa har Malam ya ce ta gagareshi sai an tafi gurin Malaminsa? Zata iya mallake Alhaji ta karya duk wani abu da na yi? Waya ni m ko ita take aiko min da faduwa so take na fadi na mutu, ko ma Iyami? Kai Nafisa ma zata iya shiga nata tsabgar fa? Gaskiya zama be gan ni ba, idan ban motsa da wuri ba, za a min Zagon Kasa a lalata min tsari’
Haka ta raya dare da tunani kala kala, idan ta yi wannan sashen ta fado wani, ta rasa wa zata zarga da karya mata aiki ko kuma kokarin rabata da mijinta, kamin safiya ta waye har ta tsuma saboda burin da take da shi na tafiya kai kukenta ga wanin Allah. Da asubar fari ta baro bangare Appa sallah ma a bangarenta ta yi, kana ganin idonta ka san bachin da ta yi kadan ne, ga ciwon kafa na damunta. Tana sallame Allah ta dauki wayarta ta kira Khairy bata daga ba, ta kira Salma bata daga ba, ta kira wayar Ruma ita ma duk daya. Bata aje wayar ba ta kira Yasir shi kadai ya dauka
“Yasir”
“Hajiya ina kwana?”
“Lafiya Kalau dan Allah ka tashi yan’uwanka su shirya mana abun karyawa ina son na fita da wuri”
“Okay”
Ta aje wayar a kusa da ita ta cigaba da jan carbinta abubuwan da suka gudana tsakaninta da Appa na musayar yawu suna dawo mata yau da asubar nan, har yanzu mamaki take waya saka ta gaba. Ta aje carbin ta rafka uban tagumi kusan bata taba shiga damuwa irin yau ba, ga aure Appa zai kara gashi yana kokarin juya mata baya har yana ikirarin abun da ya sami Iyami zai iya samunta.
“Sallamu Alaiku Hajiya”
Ya juya ta kalli kofar dakin tana samawa Yasir
“Ya jikin Hajiya?”
“Alhamdulillah”
“Zan shirya da wuri sai mu tafi asibitin”
“Aa na hutar da kai tare da Khairy zan tafi”
“Hajiya saboda abun da ya faru jiya ne?”
“Ke nan dai kasan abun da kake kokarin aikatawa ba abu ne mai kyau ba”
“Miye abun rashin kyau a ciki Hajiya? Idan ma akwai wani abu tsakaninki da Amma ita Rukayya meye nata a ciki?”
“Ai tun da sonta kake yi ba zaka gani ba, ni dai ko tsumma ne wannan tsumma na Iyami ba zan taba sonshi ba, daga Iyami har yayanta har wani abun da yake da alaka da ita ba zan taba son shi ba”
Ya mike tsaye ba tare da ya sake cewa komai ba ya fice daga dakin.
HURRIYA POV.
Bata yi irin saka ci da ta yi jiya ba, sai yau ta hana kanta bachi ta fito da wuri ta zauna falo, kusan ita da masu aikon gidan duk daya, domin sai da Momy ta gama karyawa sannan ta nufi dinning ta zauna ta zuba nata abincin ta fara ci, sosai ta cika cikinta sanin cewar da rana ba lallai ne ta samu na damar ci kamar haka ba. Ta dawo falo ta zauna a nan bachi yayi gaba da ita bata farka ba sai sha daya da rabi, shi ma sanadin tashinta da Namra ta yi ne.
“Idan bachi zaki yi ki shiga dakinki mana, kin fi kowa sanin Momy bata son ana nata bachi a falo”
Mika ta yi ta mike tsaye tana hamma, tukuna ta fara tafiya, har ta haye stairs din bata juyo ba, kai tsaye ta zarce bandakinta ta yi wanka ta fito daure da tawul ta tsaya gaban madubi tana kallon yadda kashin wuya ke mata ado kamar sarka, ta cikin madubin ta hango Hajiya Binta dake sanye da onion Hijab dinta hakoranta na makka guda suna kyalli a tsakanin hakoranta na gaba. Hurriya ta juya tare da zubawa da gudu ta rumgume Hajiya Binta.
“Hajiya yanzu kika zo”
Har Hajiya Binta ta zauna Hurriya bata sake ta ba, tana rike da ita kamar zata shige jikinki.
“Hurriya yanzu nake tafe Hurriya kuma tafiyar taki ce ke kadai”
Ta dafa kirjinta dake bugawa saboda murnar ganin Hajiya da ta yi.
“Ni kuma Hajiya? Allah yasa ba fada kika zo yi ba, ki ja min wata rigimar kuma”
“Sarkin tsoro tashi ki tura kofar ni ba shi ya kawo kawo ni ba”
Sai a lokacin Hurriya ta saki Hajiya ta nufi kofar dakin ta rufe ta dawo ta zauna dafe da Hajiya dake bude hand bag dinta, gorar ruwan sai dai wannan ba ruwa ne a ciki ba rubutu ne cike da gorar ta mikawa Hurriya.
“Hajiya menene?”
“Sha zaki yi, ki kasa uku a rana, kuma na kwana uku ne, wannan kuma da nono zaki sha, idan zaki sha safe da maraice, kuma idan zaki sha ki hau kan gadonki ki tsaya a tsaye sannan ki sha tare da bismillah”
Ta mika mata dayan maganin da yake kulle a bakar leda, sannan ta dauko mata nono.
“Na san samun nonon zai miki wahala shiyasa na nemo miki tun a can, ki rika amfani da shi kina sha”
Ta saka hannu ta karba ta dora maganin a bedside drawer dinta ban da corar nono da ta bari a hannunta ta fara budewa.
“Kuma ban da wasa, ban ce kuma ki aje shi a fili idan aka zo aka gani ki ce ni na baki ba, addu’o’i ma mi rike Hurriya, kana idan kika yi sallah ki roki Allah bawa mahaifiyarki lafiya, ya karkato da hankalin mahaifinki a gareku”