Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Ina wuni”
“Lafiya…”
Ta amsa tana binta da kallo tare da dan yamutsa fuska.
“Ita ce …..”
“Hurriya”
Namra ta karasa mata, sai ta watsawa Hurriya wani kallo daga sama har kasa ta yamutsa fuska kamar wadda ta yi arba da wani abun kyama. Hurriya ta kalli jikinta sannan ta kalli matar da tuni ta kama hanyar stairs gurin Momy dake saukowa da saurinta tana mata lale marhabun. Da alama Namra bata ji dadin abun da matar da take bakuwa a idon Hurriya ta yi ba, sai ta kama hannun Hurriya ta nufi kitchen da ita suna shiga ta rufe kofar kitchen din ta kalli Hurriya da har lokacin mamakin yadda matar ta yi mata kallon wulakanci take, bayan kuma bata da wani abun wulakantawa a jikinta ko suturarta, gashi alama ya nuna ta santa ita kuma bata wayanci wacece matar da Izza ta cikawa ciki har ta bayyana a kamaninta ba.
“Hurriya dan Allah kar abun da ake miki a gidan nan ya dame ki, kin san dai matsayinki a gidan nan, dan haka karki kula komai kin ji?”
Hurriya ta amsawa yar’uwar tata da kai.
“Wacece wannan Matar Yaya Namra?”
“Big Brother din su Momy to natarsa ce wannan, ba a nan suke ba, a Kaduna suke zaune ta zo duba mahaifiyar mijinta ne da bata jindadi maybe shiyasa ta biyo ta nan saboda suna good time da Momy sosai”
Nan ma da kai ta amsa mata sannan ta juya zata fice daga kitchen din.
“Kin ci abinci?”
“Aa Hamad ya ce Hajiyar Appa zata zo, ina jiram ta zo ne sai mu ci abinci tare”
“Yayi yar gidan Hajiyar Appa”
Hurriya ta yi murmushi ta bude kitchen din ta fito tana rike da hannayenta ta nufi upstairs, Miwan ya wurga mata harara yana jin haushin yadda Namra take mata sanyi ko a lokacin da Amma take nan balle kuma yanzu, hakan ya saka suke mata kallon munafukar cikinsu, domin ita halinta dabam da na su, kishi da ya kamata ace tana taya Momy bata yi ta bar musu sai dai su yi. Hurriya na shiga dakinta ta maida kofar dakin ta rufe ta nufi gadonta ta kwanta ta takure gurin daya kamar wanda aka tsare sai hawaye ya fara saukowa a idonta, tunanin barin gidan da Amma ta yi ya dawo mata sabo.
**** **** ****
Cikin annashuwa da ďaukin gani Momy take kallonta.
“Ai har ina cewa maybe ba zaki biyo ba, na ga Yamma ta yi”
Matar dake kawar da kai daga barin kallon aikin Momy dake jera mata kayan da aka shirya mata ta kalli Momy.
“Ai kin san halin Captain shi ya fi son tafiyar dare”
“Tare da shi kuka zo kenan? Amman be shigo ba?”
“Yana waje, waya yake”
“Oh Soyyayar da bata karewa, ai dai an kusa auren nan a huta, ke ma ki samu hutawa Ammy”
“Toh sai a taya mu da Addu’a Allah ya daidaita tsakaninsu”
Tana maganar tare da kai hannu ta dauko plate din grapes din da aka rolling ta cire ledar ta fara ci.
“Tsabani suka samu ne?”
Cikin mamaki Momy ta bukaci sani. Kamin ta bata amsa sai da ta juya ta kalli kofar dakin Momy da daya daga cikin masu aikinta taja.
“Wai har cikin daki kike barin masu aikinki suna shigowa?”
“Toh ya zan yi Hajiya Turai? Kin san dai ba zan yi aiki da kaina ba, dole su zan saka”
“Ai ni iyakacina da mai aiki falo sai kitchen da haraba, har yaushe mai aiki ta yi matsayin shigo min bedroom? Kina gani ai idan kika je gidana, su Larai ke kula min da daki”
“Toh ni wa zan saka? Ke ai kina rikon su Larai da Aliya”
“Wannan yar mijin na ki da kika fada min ta dawo nan hutu ta zo yi? Idan ma baki sonta sai ki duba a cikin dangi ki dauko wadda zata iya kula miki da daki, amman ba dai masu aiki ba”
“Zan duba a dangi, yar miji ina sakata za ace bana kaunarta”
Hajiya Turai ta yi murmushi mai sauti tana mamakin sakarcin Momy domin a gurinta abun da Momy take fada ko take gi sakarci ne.
“Ke ma dai ban da abun ki Hajiya Nafisa waya taba son ɗa ko ƴar kishiya? Ai ba wani boye boye, ba zan hana ka aure ba amman fa ba zan so matarka da ƴaƴanta ba”
“Ai Wallahi Hajiya Turai ba karamin sa’a kike yi ba, da yayana baya sha’awar aure-aure, ba kamar nawa mijin ba, domin ni ko a yanzu da ya saki Iyami tunani nake ko dai ta dawo ko kuma ya auro wata”
“Shi ne banbancin tashi a gidan arziki da kuma cintar arzikin, da ace mijinki ma kamar tashin Engr ne, da ba zai yi wannan aure-aurenba, ai talauci mugun abu ne, da zarar sun ga sun yi kudi sai su ga babu abun da ya dace da su kamar aure, amman Engr kam ai rayuwarta turawace da shi, babu ruwansa da wannan hange-hange”
“Wallahi ya huta, da alama ma ďana halinsa zai gado”
Hajiya Turai ta tabe tana girgiza kai cike da kasaita.
“Hmmm Captain? Ai idan ba Allah ya sauya masa hali ba, da wahala ma ya iya zaman da mata, yanzu ma addu’a muke kar ya ce ya fasa auren, shiyasa na ce ban yarda ya zauna ko’ina ba sai a kusa da ni”
Momy ta kasa dariya.
“Haba dai Hajiya Turai”
“Hajiya Nafisa kin manta halin ďan naki? Wannan mugun fushi da bakar zuciyar ta Captain tsoro take ba ni, komai aka yi masa a duniya ba a masa daidai, ko kallonsa kika yi zai iya cewa kallon ya wuce kima ya fara masifa ko ma ya ce hararasa kika yi, yadda kika san shaidan aka nade aka saka masa a zuciya haka, abu kadan sai masifa sai fushi baya iya controlling kansa, ga zafin hannu a family babu wanda be san halinsa ba, ita kanta yarinyar da zai aura yanzu, ba dan tana hakuri da shi ba da yanzu rabu da ita, da inda abun ya zo da sauki ita mai sanyi hali ce kuma tana gudun zuciyarsa”
“Toh ai sai a kiyaye, haka Allah yake son ganin kayansa, Captain murdaden mutum ne iya masa sai Allah”
“Ina ta addu’a dai Allah ya sauke masa wannan mugun fushi da bakar zuciyar, idan ba haka ba zaman auren ba zai jima ba, kuma ya fada min idan yayi wannan auren ba zai sake yi ba har abada, wai ko matarsa mutuwa ta yi ko suka rabu a haka zai zauna har karshen rayuwarsa, ni kuwa ba fatan haka nake ba, ni da nake son na yi ta ganin jikoki a makwafin ƴaƴan da Allah be ba ni ba”
“Gaskiya kam, muma muna son gani ai balle kuma ke da shi kadai kika haifa…”
Hajiya Turai na taba kayan marmarin suna hira da Momy har time ya fara ja, hakan kuma be saka sun yanke hirar ba har sai da Namra ta shigo turo kofar dakin ta shigo.
“Momy Hajiya ta iso”
Momy ta yatsina fuska domin ta san wace
Hajiyar ake magana, wato Hajiyar Binta surukarta uwar da ta haifi mijinta.
“Toh shi ne kuma sai an fada min? Kin san ai ba nan take fara zuwa ba sai ta gama da ko’ina take lekowa nan, to miye damuwata da ita, je ki fadawa masu aiki su kai mata abinci”
“Okay”
Ta juya ta fita. Momy ta yi tsargi da fuska.
“Idan ban je na gaisheta ba, sai ki ga ya shigo yana ta bala’i, alhalin ba so take ba, idan ta zo bata sauka bangaren kowa sai na Iyami, kuma sai ta fara shiga bangaren Kaltume sannan take leko nan”
“ikon Allah haka take ita kuma! Allah kyauta rayuwarku sai ku Hajiya Nafisa”
Cewar Hajiya Turai da kamar gatse tana jin ita duk ba zata iya daukar wannan ba, domin kowa yana da yancinsa. Namra na fitowa bedroom din Momy ta nufi dakin Hurriya ta tura kofar dakin, Hurriya na ji an taba kofar ta yi saurin juya fuskarsa ta boye kukanta.
“Hurriya Hajiyarki ta iso, Appa ya aiko Ya Musib ya fadawa Momy”
Hurriya ta share hawayenta da sauri ta juyo, sai gata ta sauko daga saman gadon bata ko kula Namra ba ta ratsa gefenta ta fice da gudu, duk wata dokar sauka ko hawa stairs na Momy manta su Hurriya ta yi a lokacin saboda zumudin zuwan Kakarta Hajiya Binta a gidan, kamar yau ne zata fara ganinta a gidan haka Hurriya ta ji. Da sauri ta bude kofar fita falon Momy bata kula komai ba ta saka kai zata fice, da mugun karfi ta ji kanta ya daki wani abu mai karfi har sai da ta yi baya kamar zata fadi. Dagowar da zata yi ta duba me ta buga domin be yi mata kama da karfe ko icce ba, ta ji an wanke mata fuska da lafiyayen marin da ya haddasa mata ganin wadansu kananan taurari, gilashin da yake mafaka ne a idonta ya fadi kasa, sai hudu da buji suka mamaye ilahirin idanuwanta. Sai ta tsaya cak irin tsayin da ta saba yi a duk lokacin da wani bakon al’amari ya ziyarceta.