Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Alhamdulillah Allah ya kawo mana su lafiya”
Shi ne abun da Gwaggo da Hindu ke Fada, direban da ya dauko su kuma yana kara basu labarin yadda aka sace wani shi ma suka karbi kudi mai yawa.
“Kasar ce ta lalace Allah ka kawo mana sauki”
Amma ta amsa addu’ar da Hindu ta yi da Ameen daman bata cewa komai sai murmushi take tana ta daukin arba da ďanta. Sai da ta isa gidan sai kuma ta soma tambayar kanta me yasa ta zo? Wani bakinciki ya rufeta ta kasa shiga bangarenta da babu komai ta tsaya, kuma ta ki yarda ta shiga bangaren Hajiya Kaltume daga ita har Gwaggo a babbar harabar gidan da direba ya faka motarsa a nan suka tsaya suna jiran isowar su Hamad.
**** **** ****
“Iyami kuma?”
Namra ta daga kai.
“Me ta zo yi?”
“Tarbon su Hamad mana Momy, kin manta yau za su dawo? Ya Yasir ma sun tafi gurin dauko su”
“Au haka ne fa, kin san badan da babu ruwanka dadin kallo gareshi, ni na manta ma”
“Toh ina take”
“Tana can babbar haraba tsaye ita da wadanda suka zo har da Gwaggo da Hurriya”
Momy ta dan yi jimm kamin ta girgiza kai.
“Wallahi har ta bani tausayi, ta yi going though alot shekarar nan, ga ciki ga saki ga sace ďa, da dai Appanku zai tausaya mata ya dawo da ita, ta rike yayanta ni na huta ma, daman bana son rikon yayan wasu, dan na san yanzu Alhaji zai ce su dawo gidan nan da zarar sun dawo kuwa ba su da gurin zama sai bangarenna.”
“Ni tausayi suke ba ni”
“To sarkin tausayi je ki ce su shigo cikin falon nan mana su zauna”
Namra ta wara ido with surprise.
“Su shigo Momy? Ko bakar mana kike min?”
“Toh ya za’ayi, ai da anyi haihu kuma zance ya kare, ba dan tana da yaya a gidan ba ai ba zata zo ba, da zarar an haihu ai kuma shi ke nan sai hakuri, kuma dai an girma kishi na miye ina zan tsaya kishi da karamar yarinya kamar Iyami? Level dina kuma ba zai taba haduwa da nata ba, har abada dukansu na fi karfinsu sai dai ta kara da Kaltume bakar akuya”
Namra ta tashi da kuzarinta ta fice daga dakin ta sauri ta sauko downstairs ta bude kofar falon ta fita. Sai da ta fara gaishe su bayan ta isa gurin da suke a lokacin Amma har ta kai zaune a cikin mota domin bata yarda ta zauna ko da a kujerun baki da ake ajewa a gidan ba.
“Amma Momy ta ci ku shigo ciki ku zauna kamin su iso”
Amma ta kalli Namra tana murmushi.
“Ki ce mun gode zamu tsaya a nan”
“Ai tun da ita tace mu shiga, mu shiga kawai zai fi mana tsayuwa a nan”
Hindu na rufe baki, masu gadi suka bude gate motar da aka je dauko su Hamad da ita ta kunno kai cikin gidan, gaba daya sai hankali ya koma can Hajiya Kaltume, Salma, Maama Khairi suka fito daga bangaren Hajiya Kaltume da gudunsu har Hajiyar da jiki ya hana ta walawa yadda take so, Namra ta shiga bangarensu da gudu kiran Momy. Appa ma ya fito da waya a kunne sai dai fuskarsa babu annuri ko kadan, ba irin da wanda ransa ya bace ba, rashin annuri ne irin na wanda ya rasa wani abu fuskarsa ma gaba daya launinta ya canja. Amma ta fito daga cikin motar ta nufi motar da Yasir ya sauko yana hawaye Ruma kuma na rutsar kuka.
“Ina Hamad? Ina Hamad?”
Amma ta tambaya domin yaronta ne kadai bata ga ya fito daga cikin motar ba. Aka rasa mai ce mata komai har ta isa gurin ta tsaya tana kallonsu murmushin dake fuskarta na kokarin gushewa.
“Yasir ina Hamad? Dan Allah ku amsa min…!”
“Amma sun kashe shi, sun kashe Hamad…!!!!!!”
Ruma ta fada da karfi tana kuka. Momy ta dora hannu saman kai tana fadin Innalillahi. Amma kuma ta yi baya baya kamar mai tafiyar baya sai Hindu ta rike ta, runtse ido ta yi ta kai hannunta ta dafa cikinta dake zillo ta durkusa a kasan guiwoyinta ta dafa kasa. Hajiya Kaltume ma kuka take ta nufi yarta ta rika hannunta da niyar rumgume sai Ruma ta buge hannun Hajiya Kaltume ta nufi mahaifinta tana kuka ta rumgume shi yana hawaye, kusan kowa a gurin sai da yayi hawaye.
“Su ba mu gawarsa mana to mu gani, idan da gaske ya mutu su ba mu gawarsa mu gani Wallahi be mutu ba, boye shi suka yi Hamad yana nan da ransa”
Hurriya ce take maganar tana kuka, Gwaggo ta rikota ta rumgume tana kuka.
Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.
Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo…
@
Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya kin daukar kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660
5️⃣
Hurriya first lost her sight a jikin Gwaggon, before ta yi going blank aka kwasheta ita da Amma sai Asibiti. Amma aka wuce da ita dakin haihuwa Hurriya kuma aka kaita Emergency. After 49hours of labor Amma ta haihu tagwayenta biyu duka maza. A madadin ta yi murnar ta haihu ta samu yan biyu sai murnar ta koma mata ciki saboda tunanin Hamad bata da wani kuka sai na Hamad. The following day aka sallamo ta daga asibitin bayan sun mata dinki kuma sun dorata akan maganin da zata rika sha na hawan jini sannan suka hana ta wankan ruwan zafi domin jinin nata ya hau sosai irin hawan da ba dan Allah ya kawo sauki ba, da abu ne mai wahala ta fita lafiya.
Har lokacin Hurriya tana asibitin Hajiya Binta na jinyar tare da taimakon Rukayya, kwananta biyu bata san inda kanta yake ba a asibitin, kamin ta farfado sai kuma ta zama so weak sai da ta sha drip da manyan allurar sannan ta samu sauki, the following day ita ma aka sallame ta two days after an sallami Amma. Wani abun da ya bawa kowa mamaki ciki har da Momy kuma ya daurewa Amma da Hajiya Binta kai shi ne, kin lekawar Alhaji Haruna a asibiti ko gida da sunan duba Amma ko kuma duba yaran da ta haifa masa, yan’uwansa na nesa da na kusa duk sun je duba twins din kuma sun je duba Hurriya wasu ma ba su samu labarin abun da ya faru ba sai a da suka je barkar twins. Sai dai Appa be bar rashin zuwa duba yaran da kowa ke musu lale da zuwa duniya, ya hana shi kyautata musu ba, duk wata hidima ta ya kamata uba yayi ma yayansa Appa yayi tun daga kan tufafin mai jego Amma har na jaririnsa, sai dai Amma bata yi taron suna ba, duk kuwa da kasancewar ba ayi taron gaisuwa a gidanta ba, an yi zaman makoki a gidan Appa kuma an masa sallatul ga’if wato sallar da ake yi ma gawar da bata kusa. Ta ko’ina Appa ya karbi gaisuwar mutane ana ta jajanta masa. All those days, hour’s Hurriya a daki take rayuwa, domin bata son ganin kowa, idan zata yi alwala sai ta shiga bathroom ta yi idan ta yi sallah ta kwanta, bata son ayi mata gaisuwar Hamad, bata fitowa idan mutane suka tambayi ina take, idan kuma aka shigo sai ta rufe kunnuwanta bata sauraren kowa, she’s the only one da ta kasa yardar Hamad ya mutu, ranar sunan yaran ma sai da ta saka kowa kuka, domin ihu take ta yi me yasa Amma ta sakawa little one din Hamad yayan kuma Hamid.