Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Yes but you’re not a baby, wasu guraren ma wadda bata kai ki ba za a iya mata aure, and zan jira ki Hurriya har zuwa lokacin da kika tashi ko iyayenki suka tashi”
“Aa ka rushe duk wani gini na soyayyata da ka yi a zuciyarka, ka gina na yar’uwata don’t break her heart, Hurriya babu kowa yanzu a gabanta, bata taba son kowa ba, kuma ba ta shirya son kowa ba, kai ba ma zata taba son kowa ba har abada… Sai an jima”
Ta raba gefensa ta wuce ta bar shi a gurin tsaye speechless… Tana isa gate din ta tura ta shiga, a yayinda Namra kuma ta fito falon Hajiya Binta ranta a bace har wani halkalo take, a tsakiyar harabar gidan suka hadu da Hurriya, Hurriya ta tsaya ita ma ta tsaya suka kalli juna, Hurriya ta dan yi murmushi kadan zata yi magana Namra ta tari numfashinta.
“Zaki yi dariya mana, tun da kin zama munafuka munafurcin da kike yi a gidansu Husna har yayi sanadin Appa ya koreki shi kika zo kina yi a nan ko? Kina son hada Hajiya da Momy kuma kina son Hajiya ta yi fushi da Appa, kin kyauta idan halin da kike yi abun kwarai ne ki cigaba, Hajiya ta fada min baki, ja, da yello na sakon da zan fadawa Momy da Hajiya, kuma zan fada musu…”
Ta dauke kai ta nufi gate.. Mamaki da fargaba ya hana Hurriya cewa komai sai binta da ta yi da kallo har ta fice. Tsaye Namra ta samu Salim a gurin da Hurriya ta bar shi
“Lafiya?”
Ta tambaya ganin yanayin dake nuna kamar ba su rabu da dadi ba. Ya juyo ya kalleta
“Ba komai, zagaya ki shiga mu tafi”
Ya shiga side din da Hurriya ta zauna wanda shi ne side din mai tukin mota, Namra kuma ta zagaya ta shiga front seat, tun da suka kama hanya bata ce masa komai ba, shi ma kuma be ce mata ba, be kuma kalli inda take ba gaba daya yanayinsa ya sauya, ta lura da hakan ta hanyar satar kallonsa da take time to time har suka isa. A gurin da ya faka dazun ya sake fakawa ba tare da ya ce da ita komai ba.
“Anya dai lafiya ko wani abun ta yi maka ne?”
“Zamu yi waya”
Ya fada a takaice, sai ta bude motar ta fita ta rufe kuma ta tsaya a gurin tana kallon motar har yayi reverse ya isa babban gate aka bude masa ya fita. Ita dai mamaki da tunani ya hana ta tsinkayo abun da ya faru, bata amsa masa ba ne ta biyo shi da bakar magana ko kuma dai wani abun ya faru, to amman ai ta ga Hurriya ta shigo normal har tana mata murmushi, ita har tana zaton murmushin jindadi ne. Tana tafiya tana tunani kamin ta waiga, to amman me yasa ta ganshi a wannan yanayin? Idonta ya sauka a wata sabuwar motar da zata iya shaidar ta waye ba. Ta isa kofar dakin ta murda ta tura ta shiga, tana yin arba da Captain dake zaune a cushion hannunsa rike da takardu ta sake fuska ta karasa gurinsa da far’a.
“Captain sannu da zuwa”
Ya dago ya dubeta cikin wani yanayi da ba na wasa ba ya nuna ta da yatsa ya ce.
“Idan kika sake kai yaron nan gurin Hurriya sai na ci ubanki….”
Namra ta tsaya a gurin kamar hoto ta kalli Momy da ita ma kallonta take tana kuma kallon Captain ta gafen ido.
“Momy zan samu?”
Momy ta kalleshi.
“Yanzu na fada maka duk abun da ya faru fa Captain!”
Ya kalli Momy ya ce.
“Ko zina take yi be kamata a koreta daga gidan ubanta ba, kuma yanzu kika gama fada min cewar mahaifiyarta bata da lafiya ko magana bata iya yi, to yanzu waye zai kula da ita idan bata gidan nan?”
“Gurin da ka ganta hannun kakarta ne mahaifiyart Appanta”
“Ba zata iya riketa yadda ya kamata ba, tarbiyarta zata iya tabuwa, dan Allah Momy dan ni ki bawa mahaifinta hakuri ki yi duk yadda zaki iya yarinyar nan ta dawo gidan nan.. ”
Namra ta yi katsalanta ta ce.
“Momy ta fada maka abun da ta yi…”
Captain ya mike tsaye ya daka mata tsawa, har sai da matsa baya da sauri gabanta na bugawa da karfi.
“One word from your mouth sai na cika miki baki da jini, baki ji kunya ba kina gidan ubanki zaune yar’uwarki jininki tana wani gurin da sunan mahaifinta ya koreta? Baku san darajar jini ba saboda kina da yan’uwa da yawa, ni da aka haifa ni kadai a cikin uwata, kuma ni kadai a gurin ubana na fi ki sanin darajar yan’uwa, dan’uwa da kuka hada uba ko uwa shi ne ďan’uwa na jini makusanci, the rest are red oil”
Ya wuce yana taka kasa da karfi kamar wata giwa, Momy da Namra suka bishi da kallo har ya fice.
“Yaushe ya dawo?”
Namra ta tambaya, Momy ta kalleta ta ce.
“Ni ma yanzu ya shigo min, ina kika je? Da waye ya ganki?”
Namra ta nufi gurin da ya tashi ta zauna yana yawo da idonta tunani kala kala a ranta.
“Gidan Hajiya na je, amman ni be gan ni ba sai dai idan Hurriya ce ta yi wani munafurci, shiyasa na ga ran Salim ya bace, ita kuma ta shigo tana murmushi… To me ma ya kai shi gurin ina ta san shi, shi ina ya san Salim?”
“Ni ba gane wannan shabbatun baki zan yi ba, ki yi min bayani kawai na fahimta”
Sai a lokacin Namra ta kalli Momy ta fara fada mata dalilin zuwanta gidan Kakarta Hajiya Binta daga karshe ta rufe da sakon da Hajiya Binta ta bata ta fada musu.
Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.
Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo…
Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence of payment to 08036126660
@
2⃣0⃣
“A haka Captain yake cewa na bada hakuri na dawo da ita, be san halin yarinyar nan ba makira ce”
Namra ta ce.
“Ni ma sai yanzu nake gane halinta Momy, kuma na yarda ita taje ta yo munafurcin a gidan su Husna wata kila tana yin haka ne saboda a tausaya mata”
“Bata daukarwa kanta hanya mai bullewa ba kuwa, kuma ni ba zan bada Appanku hakuri akan dawowarta ba, ni ko kaunar ganinta ma bana yi a yanzu”
“Ni ma shi ne, gata da fuskar tausayi da iya makirci, ban san me ta fadawa Captain na har yake son a dawo da ita, ko cewa ta yi mu muka koreta kuma? Har da wani cewa idan na sake kai Salim gidan sai na ci ubana, waya sani ko cewa ta yi na kawo mata dan’iska kuma”
Momy ta sauke ajiyar zuciya.
“Shiyasa tun farko ban so zaunawarta a bangarena ba, saboda bana son ganin dan kowa a nan sai nawa, gashi nan kuma ta zo tana neman hanani zaman lafiya”