Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Toh Amma”
Amma ta kalli Hamad tana jin wani yanayi na rashin jindadi.
“Hamad ba zaka ce komai ba?”
Juyawa kawai yayi ya shige cikin falon ba tare da ya ce mata komai ba. Sai ta lumshe ido hawaye suka sauko mata.
“Hurriya shiga ciki idan ina ganinku ba zan iya tafiya ba”
Ta fada still idonta na rufe, babu abun da take a zuciyarta sai ambaton Allah.
“Amma ko mu rakaki mu dawo”
Ta bude idon da sauri.
“Aa zan tafi da kaina ku kula da kanku”
“Toh Amma Allah ya baki lafiya ya dawo dake lafiya”
“Ameen”
Ta bude motar ta shiga tana share hawayenta. Hurriya ta daga mata hannu tana murmushi a tunaninta Amma na kewar rabuwa da su ne shiyasa take kuka, a kurciya da rawarkai irin nata bata damu sosai da tafiyar da Amma zata yi ba a yanzu, domin a ganinta gidan Gwaggo da gidan Appanta duk daya ne kara ma gidan Gwaggo tana musu gata tana barinsu su yi duk abun da suke so, ba kamar nan ba da wani abun Hajiya Kaltume ko Momy zata hana, wani abun kuma Amma ce da kanta zata hana. Juyawa ta yi ta koma cikin falon tana rufe kofar ta nufi dakinta ta cire uniform dinta ta dauki na islamiyarsu ta saka sannan ta sauko ta shiga Kitchen ta dauko cornflakes ta jika a two cups daya nata dayan kuma na Hamad, sai dai wanda yake na Hamad ya fi yawa domin shi baya wasa da cikinsa komai sai ya ci ya ji baya iya tashi yake bari, ita kuwa abinci be dame ta ba, bar ta ma ga kayan kwalama, ko abu mai ruwa dangin tuwo da shimkafa ba babinta ba ne shiyasa kullum gata nan kamar wadda ake diba ana miyar gidan. Jiki na rawa ta dauki cup din Hamad ta nufi dakinsa ta shiga sai ta same shi kwance ruf da ciki yana kuka.
“Hamad ga cornflakes na jika maka, ka ci mu tafi Islamiya…”
Yana jin sautin muryarta sai yayi tsif numfashi ma a hankali yake fitarwa dan kar ta ji.
“Hamad kuka kake yi?”
“Ina ruwanki bana shan ki dauke abunki ki fice daga dakina”
“Na maka kirki ne fa, Amma ta ce mu zauna lafiya amman baka ji ba, miye laifina dan na kawo maka abu”
“Ba zan sha ba bana so”
“Kar Allah yasa ka sha din, wanda baya jin maganar Mamanshi ya ji haushi ai, ko Sallah be yi ba kalleshi”
Sai a lokacin ya dago daga saman gadon ya sauko fuskarsa shabe-shabe da hawaye ya yi kanta, sanin dukanta zai yi ya saka ta saki kofin cornflakes din ta kama shi da kokawa daman sun saba, abu kadan idan ta yi masa sai ya ce zai daketa saboda ya fita girma jiki da karfi, idan ma ba wanda ya sani ba zai dauka ita ce kanwar shi ne yayan. Suna fara kokawa ya buga kanta ga kofar dakin sai kawai ta saka kuka ya fisge glashin idonta ya jefar a kasa ya saka kafarsa ya taka haka be masa ba sai da ya dauko talkaminsa ya saka ya bubbuga glass din ya fasa shi, domin zuciyarsa ta kawo idan kuma yayi fushi sai ya ji kamar ya tashi gidan, gashi baya tsoron kowa har Appa, idan za a masa dukan mutuwa sai yayi magana, sai dai yana da wata dabi’a na baya shiga safgar kowa sai idan an shiga ta shi.
“Wayyo Allah na…”
Hurriya ta fada tana kuka tana lalaba kofar fita dakin, domin ta daina ganin komai da kyau a yanzu sai dishe dishe saboda Hamad ya cire gilashin idon dake bata damar banbance fari da baki. Ta bude kofar ta fita tana lalaben hanya irin yadda makafi suke yi tana kuka har ta sauka kasa, da lalaben ta isa kofar falon ta bude ta fita tana kuka, dishe-dishe ta fita daga part din ta shiga part din Hajiya Kaltume har lokacin kuka take kuma ta san by that time Appanta baya gidan balle ta kai masa karar Hamad, idan kuma Appa baya gidan Yassar ne mai yi ma Hamad hukunci yadda take so, wani lokacin ko Appanta ta fadawa cewa yake ta fadawa Yayanta.
Da kuka ta nufi bangaren Hajiya Kaltume ta isa har bakin kofar falon ta tura ta shiga. Hannu ta kai tana kokarin lalabawa ta ji waye a tsaye jikin kofar, sai ta ji an sauke mata lafiyayyen mari a fuska. Tsaye ta yi cak kamar wanda aka daukewa wuta tana kallon kasa, ta san kowa zai iya marinta a bangaren Momy ko Hajiya Kaltume, saboda suna ganin abun da take kamar da gangan take yi, shiyasa dole kawai ke kawo ta bangaren Hajiya, bangaren Momy kuma ko shiga bata yi idan ta shiga sai da wani kwarran dalili, domin Hajiya Kaltume na sake mata fuska irin na munafurci, Momy kam bata sakewa kowa fuska a gidan, har gobe ganin take level dinta ya fi na kowa a gidan, wannan na daga cikin dalilin da ya saka komai nata ko na ƴaƴanta take banbanta shi da na sauran, komai nata is unique and Expensive, gashi bata son ganin ƴaƴan Amma da Hajiya ko kusa da ďakinta, sai dai ita Hajiya tana karbar Ƴaƴan Momy har so take suje a gurinta yanzu da suka girma.
“Haba Musib Haba Musib miye haka?”
Musib dake rike da wayarsa a hannu ya kalli Yassar da ya doso inda suke tsaye cikin bacin rai.
“Baka ga abun da ta yi min ba?”
“Amman dai ka san idan kana gani ba zata maka haka ba? So take ta gane waye a gurin, me yasa kuke kyarar yarinyar nan ne please? Ku ba ku tausayin halin da take ciki? Ba ku ganin lalura da take tare da ita?”
“Tana tare da lalura take yawo babu glass? Ni fa bana daukar wannan iskanci”
Ya amsa a fusace sannan ya saka talkaminsa ya fice daga falon, har lokacin Hurriya na tsaye bakin kofar ta kasa yin komai sai hawaye, a nan ta gane wani abun ake iya yi ma magana ko kuka, ta sani sarai tana kuka ko furta wani abun zai iya kara mata ko ya rufeta da duka, domin ba yau ya saba ba. Ko kwakkwaran motsi bata yi ba sai da ta ji ta a jikin Yassar ya rumgune yana bata hakuri sannan ta fashe da kuka.
“Yi hakuri Allah zai saka miki”
Hajiya Kaltume dake saukowa rike da plate ta soma fadin.
“Ya saka mata ga wa? Wai Yassar ba zaka daina wannan bakin shisshigin ba? Yadda kake da alaka da ita fa haka yake da alaka da ita, idan ma kwantar da ita yayi ya yanka ina ruwanka?”
Dagowa Yassar yayi ya kalleta.
“Haba Hajiya ai ko mai aikin gidan nan wani abu ba zai same ta na yi magana ki ce ina ruwana ba balle kuma Hurriya, marinta fa yayi kamar ya samu babbar mace”
Hajiya Kaltume ta yi fuskar tausayi kamar gaske yadda ta tambaya sai ka rantse bata san abun da ya faru ba, bayan kuma tana sama a tsaye stairs tana magana da Umm Khairi lokacin da Hurriya ta shigo.
“Ayya ah gaskiya be kyauta ba, me ta yi masa?”
“So take ta tantance waye a gurin kawai ya sauke mata mari”
“Oh Subhanallahi, Sannu Hurriya ina glass din naki?”
Cikin wani irin kuka mai tsarke numfashi Hurriya ta soma magana.
“Hamad…. Hamad… Hamad.. Ya fasa.. Shi..”
“Saboda me? Kai Hamad akwai mugun hali ita Iyami tana aikin me yayi miki haka?”
Line by line ta fada musu abun da ya faru tun a school har dawowarsu gida, ciki har da tafiyar Amma da hudubar da ta yi musu. Ciki wani yanayi na damuwa da rashin fahimta da kuma faduwar gaba a lokaci daya Yassar ya kalli Hajiya Kaltume, Hajiya Kaltume kuma ta juya ta kalli ƴarta Umm Khairi, suna haɗa ido fuskarsu ta soma fadada da murmushi, tunawa da Yassar na dakin ya saka Umm Khairi ta fara tarin karya, Hajiya Kaltume kuma ta daure fuska.
Yassar da ya tattara hankalinsa gaba daya gurin kanwarsa Hurriya ya ce
“Kamar ya sai ta haihu zata dawo?”
“Haka tace mana, kuma bata jima da tafiya ba, har ya fara min duka, Wallahi kashe ni zai yi idan muka zauna a can mu kadai”
Ya kalli Hajiyarsa cikin yanayin damuwa sai ta girgiza masa kai alamar bata san komai ba, hannun Hurriya ya rika.