Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Wallahi duk wani mai imani sai ya tausaya, kowa ya aikata haka Allah ya hana shi zaman lafiya”
Momy ta daka mata tsawa.
“Ina ruwanki shegiya yar iskar yarinya yar neman suna, ke aka sata? A gidan nan wa kika ga yana damuwa da rayuwar wani?”
“Haba Momy idan aka sace ni ya zaki ji?”
“Allah ya mayar miki da aniyarki, ni ai wanda ya sace yaron kuma ya gama da yar wajen Kaltume ya kyauta min Wallahi, daman shi Hamad ya fitini kowa, karshen mai cin amana kenan, ita kuma Ruma satarta zai hana Kaltume kwanciyar hankali”
Miwan dake saukawa ya karbawa Momy.
“Wallahi kin fadi abun da yake zuciyata, daman shen yaron nan ya isheni, saboda shi nan kwanan baya babu fadan da Appa be yi miki ba, har kuka sai da kika yi, kuma saboda shi aka mari Musib Allah yasa ma su kashe shi”
“Ato… Da ma Hurriya ce wata kila na tausaya mata, amman Hamad shegen yaro. Kaji min yarinya wai ita mai zuciyar tausayi, ke idan ke aka kama waye zai yi wannan kuka? Kuma ni bana raba dayan biyu, Wallahi Kaltume zata iya sakawa a sace yaran nan saboda muguwar mata ce, yaushe ta dawo? Ta sace kanta kudin be mata ba yanzu kuma ta koma gurin yara, balle kuma ta san Hurriya Alhaji yana ji da ita, ke ma kuma idan baki kula ba sai ta saka an dawo kanki, wannan bakar matar mutuwa kawai zata yi kowa ya huta, ni daga yau ma ba zaki sake komawa makarantar ba, canja miki makaranta zan yi, kuma direba dabam zai rika kai ki yana dawowa dake”
“Amman Momy baki ga yadda Hajiya take kuka ba, haba Momy za’ayi ta sace yarta?”
“Kukan munafurci ne, ke yarinya ce baki san kan duniya ba, ni dazun da na san Captain zai zo ai ba zan ma shiga bangarenta ba, ke kuma kika ki kirana gashi har sake zuciyar ya tafi”
“Shi yace kar na kira ki na barki sai kin kare abun da zaki yi, bayan ya tambaye ni abun da ya faru”
Miwan ya zauna yana daukar katin ya duba.
“Wallahi Momy Captain yana sonki sosai if not wulakancin nan da aka yi ta masa ba zai sake dawowa ba”
“Ai nima na san haka, shiyasa nake son zage dantse na kyautata masa a bikin, ga abu dai ya matso kusa”
Daga haka suka dauko zancen bikin kamar babu ruwansu da damuwar kowa. Appa sai da ya biya unguwar Gidan Dawa ya dauko Hajiya Binta sannan ya nufi gidan Gwaggo, a mota Hurriya na kara fadawa Amma abun da ya faru tana kuka. Appa be shiga ciki ba, daga Hajiya Binta sai Hurriya suka shiga, Hajiya ta hadu ita da Gwaggo suka yi ta bata magana suna kwantar mata da hankali. Sannan taja ma Hurriya kunne kan fita waje duk kuwa da ta san Hurriya ba ma’abociyar yawo bace, daman kuma Appa yayi mata nasa jan kunne a mota.
*** *** ***
Wasa wasa aka kwashe kwana uku shiru babu Hamad da Ruma babu labarinsu, police din da aka damkawa case din kuma ba su samu wani bayani ba, sai dai suna ta kokarin zafafa bincike iya yinsu. Tun daga ranar kuma Amma bata iya bachi, dare take rayawa tana fadawa Allah bukatarka ya kare mata danta ya dawo mata da shi cikin aminci. Abinci ma Amma bata iya ci sai Gwaggo ta yi da gaske. Hurriya kuma tun daga ranar bata sake zuwa makaranta ba saboda tsoron fita da take ko kofar gidan bata yarda ta tafi, daman kuma Appa ya daukarwa yaransa hutun sati daya a school dinsu har zuwa lokacin da abun zai dan sake su. Appa ma ya yarda Hurriya ta zauna a gurin Amma ne kawai saboda Hurriyar ta zaki haka, kuma ya san hankalin Amma zai dan kwanta idan Hurriya tana kusa da ita, ba dan ransa yana so ba, domin gani yake ko a can za a iya tafi a dauki Hurriya ko Amma.
Ranar da Ruma da Hamad suka cika kwana bakwai da sacewa su aka kira wayar Appa ana neman miliyan dari na Hamad, miliyan dari na Hurriya. A ranar hankalin Appa ya tashi sosai ya nemi su hada shi da yaransa su yi magana, sai suka ce mutum daya za su ba shi wato Ruma, suka bata wayar ta yi magana da shi tana kuka sosai tana fadar sun ce za su kashe su idan ba a kawo kudi ba. Appa ya bukaci ta ba sake ba su wayar, ta mika musu suna karba Appa yace yana neman ragi sai suka jaddada masa babu abun da za su rage masa kuma idan be biya kudin da wuri ba za su kashe su. Kamin Appa ya sake cewa wani abu suka kashe wayar a take ya sake sanar da yan sanda. Bayan ya sauke wayar Hajiya Kaltume ta share hawaye ta ce.
“Alhaji ka ba su kudin nan dan Allah su sako yaran nan kar su kashe su, kana jin sun ce za su kashe su fa, mutanen nan ba su da imani ko kadan ni na san yadda suke yi ma mutane”
“Dole ai za mu nemi sassauci ai, miliyan dari biyu wasa ne?”
“Amman ai kana da su, ba su fi karfinka ba, dan Allah ka ba su kudin nan, idan ma sun maka yawa, ni zan hada da dan abun da yake hannuna ita ma Iyami a fada mata ta bada abun da take da shi a hada a karbo yaran nan”
“Aa babu kudin da zan karba, kuma idan za a fadawa Iyami sun kira ba sai kun ce mata yace zai kashe su ba”
Hajiya Kaltume ta sake fashewa da kuka.
“Alhaji kenan kana jin matar nan kamar ranka, waya ke ta tashin hankalinta a yanzu? Ni ta yara nake ba nata ba”
Appa ya mike tsaye ya fice daga falon. Hajiya Kaltume ta dauki wayarta ta fadawa Hajiya Fatee abun da ya faru tana kuka kamar ba ita ba, Hajiya Fatee sai hakuri take bata, sai da suka gama wayar sannan ta fito bangaren Appa ta dawo nata bangaren ta fadawa yaransa abun da ya faru, haka suka yi ta juya maganar suna kuka, daga karshe ta umarci Yasir ya je ya fadawa Iyami halin da ake ciki.
“Kar naje kuma Appa ya zo yana fada”
“Amman ai tana da hakkin sani, tun da danta aka sace, shi kansa be hana a fada mata ba, yace dai kar a fada mata sunce za su kashe su, fada mata mana ta hado dan abin da take da shi ni na hada a karbo yaran nan”
“Amman kudin nan be fi karfin Appa ba, kamin ku yi wannan yunkuri da dai kun ba shi lokaci ku ga abun da zai yi”
“Ni zan iya jira ba, na san yadda mutanen nan suke ba zan so ko kwana daya Ruma ta kara hannunsu ba, idan ita ba zata yi ba ni zan bada nawa a sako min yata”
Yasir ya girgiza kai.
“Gaskiya ni ba zan iya zuwa ma Amma da wannan labarin ba”
“Ina fa zaka iya, da dai ni ce da gudu zaka zo ka fada min ai”
Ta fashe da sabon kuka, Yasir ya tashi ua fice daga dakin. Yana fita Hajiya Kaltume ta kalli Maama ta ce.
“Maama shirya direba ya kaiki tafi ki fadawa Iyami yadda suka fada”
“Sai kin masa magana Hajiya kin san tun da abun nan ya faru Appa ya saka dokokin fita masu tsauri”
“Zan masa”
Hajiya Kaltume da kanta ta fita ta yi ma masu gadin magana da kuma direban. Burinta dai a fadawa Iyami abun da mutane suka ce ko da hankalinta aka daga dadi zata ji a yanzu, domin ta san hawan jinin mai ciki yana da illa sosai balle ita da take da tsohon ciki haihuwa yau ko gobe. Sai da ta fadawa direba ya jira ta fito sannan ta fita motar Maama ta shiga gidan Gwaggo kamar a ita ba, rabon da ta je gidan ma ta manta amman a yau zata tafi ta sanar da bakin labari ga Amma. Ko da ta shiga ta samu Amma na zaune waje harabar gidan kan tabarka, hannunta yana kan Hurriya dake kwance gefenta tana bachi.
“Wa’alaikussalam”
Amma ta amsa tana kallon Maama gabanta ma faduwa, kusa da ita Maama ta zauna har da gaisheta abun da bata saba ba, domin babu mai bata girma a cikin ƴaƴan Hajiya Kaltume sai Yasir.
“Maama lafiya? Fuska ki ya nuna akwai damuwa fada min me ya faru?”
Maama ta fede mata daga biri har wutsina na abun da ya wakana tsakanin Appa da masu satar mutanen ciki har da zancen da Appa ya ce kar a fada mata cewar sun ce za su kashe su.