VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

“Ku kira su Hajiya Fanna da Mama Zainab ku fada musu halin da ake ciki, idan asibiti za a kai ta sai mu tafi…”

Maama ta juya ta kalleshi tana hawaye

“Haka Jarabawar ta zo mana Yaya? Ni gidan aure babu dadi Hajiya kuma nata auren ya kare, Khairy an fasa yanzu kuma wannan ya biyo baya?”

Yasir ya daka mata tsawa kamar zai daketa.

“Laifi duk na waye ba naku ba? Idan ta kauce ko zata aikata wani abun da ba daidai ba kun fi kowa sani, me yasa ba zaku nuna mata illar hakan ba? Amman ke kuke zugata kuna tayata kishi ku nuna abunda take daidai ne, ke Khairy lokacin da kika aikatawa Hurriya haka bata ma sani ba, saboda zuciyarku babu kyau, ke kuma idan abun kwarai ne gashi yanzu kin yi aure kin girba, kar wanda ya sake saka min baki akan lamarin uwata kar wanda ya sake wata magana ku bar ni na ji da zafi daya”

Ya share hawayensa ya fice daga dakin, ya sauko kasa wayarsa tana ringing da ya duba sai yayi arba da number Appa, and for the first time sai ya ji ba zai iya amsa kiran ba, a yayinda wayar yake rike a hannunsa tana ringing. Ya jingina da kofar falon ya cije bakinsa ya buga ginin ya girgiza kai. A karo na biyu wayarsa ta sake yin ringing ya dago ya duba wayar Appa ya sake kira wannan ya dauka sai dai yana kara wayar a kunnesa sai ya fashewa Appa da kuka kamar mace.

“Subhanallahi… Yasir.. Lafiya kana ina?”

“Ina gida Appa.. Amman ba lafiya, ji nake kamar na bar garin nan kamar na tafi a inda babu kowa na rayu a yau, duk na ji duniya ta isheni”

“Toh gani nan zuwa gidan”

Appa ya sauke wayar yana jin karin wata damuwar, daman ya kira ya fada masa yadda suka yi daman ya kira ne ya fada masa yadda suka yi da Amma da kuma Captain sai dai jin halin da dansa yake cike har yana kuka ya saka shi jin babu dadi domin be san Yasir da bayyana damuwa idan ma akwai.
Yasir ya share hawayensa yana kokarin ganin yayi halin maza wajen hana kansa kuka da jin tsanar duniya da halin da yake ciki, ya nufi bangaren Appa, a Balcony ya zauna kamar dai dazun yana jiran Appa, sai dai Yayyun Hajiya Kaltume da Maama ta kira ta fada musu halin da ake ciki sun riga Appa zuwa, hakan kuma be saka Yasir tashi ya koma bangaren ba, domin baya son ya sake kallon mahaifiyarsa a cikin wannan halin. Direban Appa ya fakawa Yasir ya mike tsaye Appa kuma ya fito mota da sauri yana kallon Yasir.

“Mu shiga ciki”

Yasir ya wuce gaba sannan Appa ya bi bayansa, a babban falonsa suka fara zaunawa Appa ya dubi ďansa cike da damuwarsa ya ce.

“Lafiya Yasir? Me ya faru..?”

Nauyin furucin da kunyar abun da mahaifiyarsa ta aikata sai ya saka shi kasa furta komai a gaban Appa.

“Yasir daga kanka ka kalleni mana fada min damuwarka ni kaina da nake mahaifinki wani abun ai kai nake samu mu tattauna balle kuma kai da kake ďana me yake faruwa?”

“Appa a game da Hamad ne… Dazun ban mun gama magana da kai na shiga cikin gida na fadawa Hajiya abun da ya faru…”

Ya kwashe abun da ya faru ya fadawa Appansa domin be san a inda zai bude damuwarsa bayan nan ba. Appa ya mike tsaye yana ambaton Allah yana jin kamar duniya zata rikito ta fado masa tsabar tsorata da abun da Hajiya Kaltume ta aikata.

“Yanzu da saka hannun Kaltume aka dauke ďana? Da sa hannunta a rabuwata da Iyami? Me na… Me.. Mena rage ta da shi? Akwai ta inda na canja mata ne bayan auren nan? Ba Iyami da yayanta kadai ba har da Sapna? Ita me ta yi mata? Wace irin mata ce Kaltume? Me yake damunta? Innalillahi Wa’inna ilaihirraji’un”

Duk yadda Yasir yake tunanin abun ya gigita shi sai ya tarar ya gigita Appa fiye da shi domin sai da ya tsorata da yadda Appa ya rike kirjinsa ya dafe saitin da zuciyarsa take, tsoron rasa mahaifinsa ya saka shi nadamar sanar masa abun da yake faruwa.

“Appa dan Allah ka zauna”

Yasir ya rika shi ya zauna yana girgiza mai shi ma abun ya daure masa kai, ya san be rage Hajiya Kaltume da komai ba, akan wane dalili zata azantar da kanka ta azabtar da shi kuma ta bi ta yayansa da matarsa? Ta wani bangaren kuma yana ganin laifin ba nata ba ne nashi ne saboda be rike addu’a ba tun farko, kuma be tsaya ya zabo mai addini ba da bata so ta masa wannan aika aikarba a gidansa. Hankalinsa be kara tashi ba sai da ya shiga da kansa ya duba halin da Hajiya Kaltume take ciki, a nan ya tabbatar da abun da dansa ya fada masa yan’uwanta kuma suka bukaci tafiya da ita gida a tare da su, Appa ua daga hannunsa sama yace ba su bukatar umarninsa domin ba aurenta yake a yanzu ba. Momy da Namra sai suka shigo suna kallonta a lokacin da labarin ya isa kunensu, Momy wani sabon tsoron Allah ya kamata daman can ta san Kaltume zata iya aikata fin haka ma, amman ba ta yi zaton da hannunta dumu dumu a satar Hamad ba, a nan ta gane ita kanta Allah ne kadai ya tsare wata kila ita din ma ta an sace mata Namra ko Miwan ko Musib.

Ta bangaren Iyami ma haka ta kasance cikin mamaki ta tashin hankali a lokacin da Appa ya sanar mata halin da Kaltume take ciki, sai ta fashe da kuka tana mamakin tsananin kiyayya da zafin kishi da zai saka mace aikata irin wadannan munanan abubuwan, daman can sun yi tsammanin da hannu a cikin lamarin saboda yadda ta nuna bata damu ba kuma yake nunawa yaran kiyaya ta zahiri. Hakan sai ya kara sanyaya guiwar Amma dake shirye shiryen tarewa a gidan Appa, duk kuwa da ta ji cewar a yanzu Hajiya Kaltume bata cikin hayyacinta, kuma ita ma ta rike addu’a da tsarin jiki ba kamar da can ba, ta wani bangaren Gwaggo da Iyami suna ganin kamar Hajiya Kaltume ta yi haukan karya ne saboda ta san asirinta yana daf da tonuwa. Faruwar hakan ya sakawa Amma yarda cewar yaron da zai baro Ethiopia tare da Hurriya da surukinta da kanwarta lallai danta ne wata kila Allah ya raya shi ne saboda zuwan wannan ranar da asirin Kaltume zai tonu, domin wani abun tun a duniya yake bayyana. Ba sai an je ba, lahira karbar sakamako ne kawai da sanin makoma.

 

HURRIYA POV.

Cikin tsoro Mama Rukayya take kallon Hamad da ke zaune a masaukinsu, Hurriya na zaune a kusa da shi tana kuka shi kuma yana hawaye.

“Taya wai za ace wanna Hamad ne ni fa ban gane ba..”

“To ke da kika san kan labarin kenan balle ni da ban san komai akai ba”

Cewar Momy Ikilima. Captain ya dan dago ya kallesu kamin ya dauke kai ya cigaba da amsa wayar Appa.

“Hakan nake tunanin zai fi, sai mu dunguma gaba daya mu dawo tare, saboda bana son karatun nasa ya samu matsala ka san su nan sai da doka suke komai ba kamar kasarmu ba”

“Shikenan za’ayi haka, zan kira ka duk yadda ake ciki”

“Na gode Appa…”

Ya sauke wayar ya kalli Hamad.

“Hawayenka su suke saka yar’uwarka kuka kuma kasan yadda idonta yake”

Hamad ya kalleta sai ya mike tsaye da sauri Hurriya ta rike hannunsa ganin take kamar idan ya fita ba zai sake dawowa ba.

“Dan Allah karka tafi..”

“Hurriyana sake ki babu inda zai je tare zamu koma nigeria, na yi magana da Appa zai yi magana da jami’an tsaron can a matsayinsa na Mahaifin Hamad sai su aiko da takarda zuwa ga Ambassador Nigeria da yake nan shi kuma zai yi magana da makaranta su ba mu aron Hamad mu tafi tare da shi a can za a warware komai”

Ta sake shi ba dan ta gamsu zai dawo ba idan ya fita sai dan babu yadda ta iya.

“Bana son ya sake tafiya ya bar ni..”

“As long as you’re with me you’re not alone, you will never be, babu sauran damuwa Hamad ba zai sake tafiya ba..”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected