Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Ga yayana zasu min komai”
“Matan dai ai kin san aure za su yi, Yasir kuma abu ne mai wahala ya rike kasuwanci domin na lura hankalinsa ya fi karkarta a bangaren aiki, bayan nan ma kasuwancin Crude oil yana bukatar kudi mai yawa sai mutum ya tsaya da kafarsa”
“Zan dan hada abun da yake hannuna na ga zai kai nawa, sai ka kara min da wani haba Alhaji ina matar Alhaji Haruna Mai Yadi ai wannan kasuwancin ba zai gagara ba”
Tana maganar har da wani daga masa gira kamar wata tsohuwar kasuwa. Appa dai yayi murmushi ya girgiza kai. Sai da aka kira sallah azahar sannan ya fita gidan ita kuma ta fito daga bangarensa ta nufo nata tana tunanin yadda zata zama daya daga cikin attijiran matan jihar Zamfara idan ta fara kasuwancin, bayan kasancewarta matar Alhaji Haruna Mai Yadi, so take ta mamaye ko’ina ta sha gaban Momy a yanzu, ta yadda ita kanta Momy sai ta yarda Hajiya Kaltume ta fita komai. Ta shigo falonta cikin yanayi na farinciki da jindadi ta tararda duka yaranta suna zaune falon suna hira ban da Ruma da tun da ta dawo ta ware kanta daban take rayuwarta ita kadai ba tare da sauran yan’uwanta ba, haka ma ba ta sake kusantar mahaifiyarta ba, a baya kuma ba haka take ba ita ce yar autar Hajiya Kaltume kuma ita ce shagwababbiyar yar rikon jakar Hajiya.
“Hirar me kuke yi?”
“Yadda zamu tashin garin nan idan Allah ya nuna mana bikin Maama”
Hajiya Kaltume ta yi murmushi.
“Gaskiya ne, za ayi biki na ban mamaki daman wasu daga cikin abokan mahaifinku ba su san ma ya taba aurar ba”
Maama ta saka dariya
“Hajiya wake maganar auren Sapna auren kauye kuma tun kamin Appa yayi suna, aurena dai za’ayi aure na ji da fada da zai tashi hankali media ya zama topic of discussion a Gusau”
Hajiya Kaltume ta yi murmushi kamin ta bi kowa da kallon.
“Toh Allah ya nuna mana, shi ma angon na ki na lura ai dan son riya ne”
“Wallahi haka yake, yace aurensa na farko auren hadi ne shi kuma baya son matar aka masa dole shiyasa be wani bada jiki ba, amman aurena ko hmmmm”
Duk suka dariya. Khairi ta ce
“Yaya Maama yana sonki Wallahi da alama kan waccan matar tasa zata sha wahala a hannunki”
“Kar ma ki ji yadda yake zaginta ni har tausayi take ba ni”
“Ba a tausayin mata ai Maama raba kanki, kina shiga gidan nan idan ta samu sa’arki waje za ayi da ke, wai ina Ruma?”
Hajiya ta karasa tana tambayarsu yar autarta domin ta zagaye falon da kallo bata ga Ruma ba. Salma ta ce.
“Hajiya kin san Ruma tana dakinta fa, yanzu ta mai da kanta aljanna bata son mutane ko kadan”
“Oh ni wannan yarinyar”
Hajiya ta nufi hanyar stairs, sai da ta yi kamar ta shiga dakinta sai kuma ta nufi dakin Ruma ta tura kofar dakin ta leka, zaune ta hangowa akan studied table dinta tana rike da wani textbook tana karantawa.
“Ke…!”
Ta juyo ta kalli Hajiya Kaltume. Sai ta shigo cikin dakin ta maida kofa ta rufe ta nufeta tana fadin
“Wai ke wani sabon iskanci kika kirkira yanzu da rainin wayo? Sai ki ware kanki dabam kina rayuwa kamar wata mayya?”
A take idonta ya cika da ruwan hawaye.
“Bana son gidan nan Hajiya, na fada miki ina son na koma gurin Hajiya Binta da zama ko Anty Farisa”
“Babu inda zaki je, babu gidan uban da zaki zauna idan ba zaki iya rayuwa a nan ba sai ki hadaye zuciya ki mutu”
Hajiya ta fada cikin bacin rai sannan ta juya daf da zata kai hannu ta bude kofar dakin Ruma ta mike tsaye ta ce.
“Har yanzu Hajiya gani nake kamar ba ke bace, na san baki son Amma amman kisan kai Hajiya kisan kai? Baki ga yadda suka fasa masa kai ba, ko’ina jini yake, still kuma suka karbi kudin nan gurin Appa, Hajiya mamaki nake yadda zuciyarki zata iya aikata haka, kullum sai na yi mafarkin Hamad abun da na gani ya kasa fita a idona ni kam ina ma ba ke ce uwata ba…”
Hajiya Kaltume ta juyo a fusace ta nufo Ruma gadangadan, tana isa gurin da Ruma take tsaye tana hawaye Hajiya Kaltume ta dauke ta da mari ta rufe ta da duka.
“Yaushe wuyanki yayi tsauri haka har bakinki ya iya furta kalamai irin haka? Dan ubanki fuskata kika gani tare da mutanen ko kuma gurin kika gan ni?”
Cikin kuka Ruma ta soma bata amsa.
“Amman sun yi magana dake lokacin da suka dauko mu, Hamad ma ya ji muryarki shiyasa kika ce a kashe shi”
Hajiya Kaltume ta yi saurin rufewa Ruma baki tana juyata ta kalli kofar dakin, sannan ta juyo ta kalli Ruma tana kuka.
“Wallahi ban ce a kashe shi ba, Yaushe zan ce a kashe shi? Wallahi ban ce a kashe shi ba, kuma Wallahi idan wani ya ji maganar nan Ummu Rumana sai kin yi bakincikin zuwa duniya”
Hajiya Kaltume ta sake ta fice daga dakin da sauri tana share hawayenta, da hakki ta isa nata dakin ta zauna bakin gado kamar wadda ta yi gasar tsere hakki ne na mai jin tsoro da fargaba faruwa wani ba, ba na wanda yayi wani aiki ba. Da sauri ta lalabi wayarta ta kira macen da ke share mata kukanta…
“Hajiya Fatee ke kadai kike?”
“Ni kadai nake Hajiya Kaltume Lafiya?”
Hajiya Kaltume ta fashe da kuka tana fada mata abun da Ruma ta yi mata.
“Ah toh ita kuma duk saboda wa kike abun?”
“Ita wannan bata gani ai, da ma Khairi ce ita ce mai irin zuciyata, kuma ni Wallahi ban dauki yaron nan dan a kashe shi ba, kaddara ce kawai ni ba ma shi na so a dauka ba, yar makauniyar na so a dauka, amman abu ya zo a haka”
“To yanzu me ye abun yi?”
“Abun yi kawai a rufe mata baki, domin na lura tona min asiri zata yi, tun da ta dawo gaba daya ta bi ta canja, sai zancen barin gidan take nan gaba kadan zata iya cewa zata fadawa wani idan abu ya cika”
“Lallai da maganarki, haka ya kamata, daman ita bata san kan duniya ba shekara goma sha bakwai miye ta sani, ai da gaskiyarki da baki saka ta a lamurranki duk da shige miki da take da sabon da kuka yi, wannan ai sai ta fadawa duniya mun je gurin kaza da kaza”
“Ina zan yarda? Ai duk yarana bana zuwa da ko daya, sai dai na fada musu”
“Haka ya kamata gaskiya ki kirashi ki fada masa komai idan akwai yadda za ayi a danne bakinta nan dan kar ta fada”
“Zan kira shi, daman ban gama fita bakincikin Iyami ba yanzu kuma ita zata tsirar min wani sabon shafi”
“Wallahi kuwa shegiyar dagar ta sake jefo masa yan biyu haihu kamar karya kuma duk maza, ta dai rantsa sai ta ci gadon Alhaji daman shi ne take ta yi ma wannan haife haifen, ai Wallahi an rage mugun iri ma, yaron nan ba fadar kike yana damunku”
“Wallahi ya addabi kowa, kuma ni ba shi na ce a dauka ba, iya yar macijiyar na ce a dauka, su kuma sai suka bata aikin suka kira wayata a gabansu yaro ya ji muryata, shi ne duk sila ni kaina kullum tunanin yaron nan nake nake Wallahi abun ya hana ni sukuni sam”
“Allah dai ya rufe asiri kar wannan yar autar taki ta janyo mana jagwal”
“Ameen, ai maganinta zan yi”
Daga haka suka yi sallama, babu bata lokaci Hajiya Kaltume ta lalabo number Malaminta a wayar ta kira shi domin kai masa kukanta, daman kiran Hajiya Fatee da ta yi na neman jin shawarar abun da zata ce ne domin bata yanke hukunci sai ta shawarci aminiyarta.
Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.