Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Haba Hajiya yanzu duk hakurin da muka yi ta baki baki hakura ba, ita dai Hurriya na san bata da matsalar komai kuma ko yanzu zata so komawa gidan ubanta domin babu kamar gidan uba a duniyar nan”
“Nan da take ai daji ne, da bata da alaka da kowa, ke ni kar nake ganinki, halinki babu wanda ban sani ba Kaltume, tun kina da kurciyarki har yanzu da kika yi yaya, saboda na aika muku da shi ne kika taso mijinki gaba kuka ta so wai azo a kalailaye ni da dadin baki a tafi da Hurriya ku karasa kasheta a can ko?”
“Wallahi ba manufata kenan ba, ni taya zan ce na kashe rai balle kuma Hurriya haba Hajiyaba zan iya aikata haka ba, kawai maganar da kika fada mana ne, na lura da haka ya kamata na yi kasancewa uwa, a wacan lokacin idona ya rufe ne ni da Alhaji shiyasa har ya koreta, ni kuma na kasa dakatar da abin amman na bashi hakuri Hajiya, ita kanta da zata fadi gaskiya ta sani”
Cikin kuka Hajiya Kaltume take maganar da hawaye shabe shabe a fuskarta. Kukanta ya bata ran Appa har yayi sanadin da ya watsawa Hurriya wani kallo daya saka ta sauke idonta kasa da sauri.
“Hajiya, ki yi hakuri haka ba zai sake faruwa ba”
“Ba fa zata koma ba, daman can ni bana son zamanta a gidan nan, ba za a kula da ita ba yadda ya dace, gashi ba iya magana take ba fa ma Hamad ne shi ne mai iya magana da fadar abun da aka yi har ma ya rama, amman ita ba zata fadi komai ba, ko a lokacin da aka ce taje ta yi gulmarka a wani guri ai be kamata ka yarda ba, domin idan akwai wanda ya san halin Hurriya ciki da waje a duniyar nan kai ne, yadda ta shaku da kai bata shaku da mahaifiyarta haka ba”
Appa ya sauke kansa kasa har lokacin hakuri yake badawa yana neman yafiyar Hajiya.
“Ni na yafe maka amman tabbas da baka zo ba kam, ina nan rike da wannan abun a raina kuma ba zai maka dadi ba saboda ni uwa ce, ko ban fada ba idan raina ya bace zaka iya gani a al’amurranka ko a jikinka ma”
“Toh a yafe min Hajiya hakan ba zai sake faruwa ba, kuma dan Allah ki bar mu mu tafi da Hurriya”
“Ba za a tafi da Hurriya ba, idan ka ga ta bar gidan nan to a dayan biyu ko dai ta yi aure ko kuma na mutu”
Hajiya ta sake fashewa da kuka, ita kanta Hurriya ta tsorata da yadda Hajiya take son komawarta a gidan har da hawayenta. Cikin kukan Hajiya Kaltume ta kalli Hurriya data kasa tashi a gurin da take zaune ta ce.
“Subhanallahi, ki yi hakuri dan Allah, kuma ki sak baki Hajiya ta hakura ita ma, wannan maida magana baya da ake ba shi da dadi, takas mahaifinki ya zo saboda ya tafi da ke, dan Allah ki yi hakuri Hurriya”
Hajiya Binta ta yamutse baki.
“Hurriya bata da ikon kanta, ikonta yana gurin mahaifinta da mahaifiyarta sai kuma ni, dan haka ki daina saka Hurriya a cikin maganar nan”
Hajiya na fadar haka Appa yayi karaf ya kalli Hurriya ya ce.
“To idan haka ne, Hurriya ina baki umarni a matsayina na mahaifinki ki koma gida cikin yan’uwanki, idan ba haka ba zaki yi mamakin abun da zai biyo baya…”
Appa na gama fadar hakan ya kalli Hajiya Kaltume ya ce.
“Tashi mu tafi”
Sannan ya mike tsaye, Hurriya ma ta mike tsaye da sauri, cikin karfin hali na tsufa Hajiya Binta ma ta mike tsaye ta rike hannun Hurriya.
“Hurriya ba zata koma ba, gaba daya ka canja tsoho ta ya zan yi umarni kuma ka yi kokarin karya wannan umarni? Anya kana cikin hayyacin Tsoho?”
Ya kada kansa kasa.
“Hajiya ba umarninki nake kokarin karyawa ba, bana son zaman Hurriya a ko’ina sai a gida, sanin kanki ne tun kamin yau kin ce na baki ita ban baki ba, saboda bana son kowa ya rika min da”
Hajiya Binta ta masa wani kallo na tsanaki, shi kuma ya ki yarda ya daga kansa ya kalleta sai yawo yake da idon a kasa. Tun tashinsa har girmansa bata ba shi umarni ya tsaba sai a yanzu, ba kuma yanzu ta yau ba, yanzu da girma ya cin masa ita kuma take gangarawa. Ko a lokacin da ya saki Iyami babu yadda bata so ya dawo da ita ba yaki, yanzu kuma saboda Hajiya Kaltume ta sako shi a gaba ya zo a maida Hurriya yake wannan bubutan.
“Kai ma haihuwarka aka yi, kamar yadda ka haifi Hurriya idan baka yi hankali ba, kai ma sai na baka umarnin da idan ka saba ba zaka ga da kyau ba”
Hajiya Kaltume ta kama gafen mayafinta tana share hawaye tare da mikewa tsaye domin ta lura ran Appa ya bace kamar yadda na Hajiya Binta ma ya bace har ta fusata.
“Ba za’ayi haka ba, ba ta kai ga haka ba, Alhaji mu tafi, tun da Hajiya na zon zaman Hurriya a nan ka barta ta zauna Allah ya bada hakurin zama”
Appa ya kalli Hurriya sai da hantar cikinta ta kada ta fara kokarin zare hannun Hajiya Binta a hannunta, ba kuma dan komai ba sai dan saboda Hajiya Kaltume, sannan ya dan risina ya ce.
“A tashi lafiya Hajiya”
Hajiya bata amsa masa ba bata ce masa komai ba har ya fice, kana ita ma Kaltume ta yi ma Hajiya sai da safe ka roki gafararta sannan ta fice. Sai a lokacin Hajiya Binta ta zauna ranta a jagule.
“Hajiya dan Allah ki yi hakuri ki bar na tafi, kar na kawo rudani tsakaninki da Appa, ko kuma Appa yayi fushi da ni kamar yadda ya fada”
Hajiya bata kula hawayen Hurriya dake saukowa ba ta daka mata tsawa.
“Ke rufe min baki nemi guri ki zauna babu inda zaki je, gaba daya sun canja masa kwakwalwarsa, idan yace ya yafe ke ni ma sai na yafe ki, idan takamar yana da kudi yana kula da ni, ai ai ba haka ya tashi yana ciyar da ni ba, Allah ke min komai”
Hurriya ta duka tana kallon Hajiya bi ta data koma ta zauna.
“Idan kika samu tsabani da Appa saboda ni, zai kara wutar kiyayyata a zuciyarsa ne, kuma zai tsine min domin baya a cikin hayyacinsa a yanzu, da ba ke ma ba zai tsaba umarninki ba, idan kika yi fushi da shi ba zai ga da kyau ba, idan kuma hakan ta faru da shi, ke da mu abun zai shafa, domin ke uwarsa ce babu yadda zaki da danki sai hakuri, mu kuma yayansa har kasa ta hade bamu da wanda ya fi shi, amman matansa za su iya gina kansu har su manta da shi, wuya bata kisa Hajiya, kuma duk yadda suke nufina da sheri Allah zai kareni, ina jin tsoron fushin iyayena akaina, yardar Allah tana tare da yardar iyaye, mahaifiyata bata da lafiya kuma bana kusa da ita, ki fahimta Hajiya su suke su raba ni da Appa, dan Allah karki bari haka ta faru, ki yafe mishi ki sauko daga fushin ki yi hakuri na koma…”
Hawaye ya zubo a idon Hajiya Binta, kalaman Hurriya na hankali sun ratsa kwakwalwarta, sai ta saka hannunta biyu da tsufa ya canja musu halittar fata ta rike fuskar Hurriya.
“Ke yata ce ta gari Hurriya, kuma kamar kore kamar kumbonsa, barewabata gudu danta yayi rarrafe, kin fi duka Yaya da Tsoho ya haifa hankali da hangen nesa, karamar yarinya mai kwakwalwar manya, Allah ya miki albarka, na barki na barki ki koma gidan ki zauna, zalinci baya dorewa kuma da yardar Allah sai kin fi su albarka, sai sun koma karkashinki sai rayuwarki ta dawo tana burgesu, ki shirya gobe zan saka direba ya kai ki, kuma zan biki da addu’a, zan rika zuwa ina dubaki”
Hurriya ta lumshe ido tana kwantar da kanta a hannun Hajiya binta hawayenta na sauka a tafin hannun kakarta. Ita kanta bata son komawarma amman ta lura kamar wani abu suke shirya mata kuma suke son hada mata ita da mahaifinta shiyasa suka har Hajiya Kaltume ta nace sai an koma da ita.
“Kin fadi gaskiya, Tsoho be taba musa ba sai a yanzu ta aka cire masa kowa a zuciyarsa, yau a gaban matarsa nake cewa ba za’ayi ba yace za’ayi Allah mai girma”