Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un, mutanen nan ba su da imani ko kadan, kai yaushe aka gama wannan kuma ace sun kama wani? Wai anya ana son mu cigaba da rayuwa a kasar nan kuwa? Wannan wane irin bala’i ne?”
Haka yayi ta fada, Hajiya fatee tsabar tsoro ji take kamar ta rufe masa baki, domin ta ga tashin hankali da bata taba mafarki ba.
“Ka rufawa kanka asiri da zagin mutanen nan, ba au da imani ko kadan, su hanyar da imani ya bi ma ba su santa ba”
Fadeel ya juyo ya kalleta a daidai lokacin da ya faka motarsa a harabar gidan, yan’uwa da abokan arziki suka fito da gudu suka yo gurin motar domin taron Hajiya Fatee ciki har da Afrah da Hajiya Fatee take zagi wato matar Fadeel da kuma yaranta masu aure.
“Wallahi Hajiya Kaltume ce taja min, ita na raka a kauyen”
“Toh me kuka je yi kauyen?”
Bata samu amsa masa ba sakamakon bude gambun motar da aka yi ana murna da zuwanta, daman kuma tana neman dalili da zai hanata yi masa wani bayani dan bata shirya tonawa kawarta asiri ba. Ta bangaren Hajiya Kaltume after ta samu ganawa da mutane ta huta zuwa dare danta Yasir ya dauketa zuwa asibiti kamar yadda mijinta ya umarta. Sun dubata suka mata duk wani gwaje gwajen da ya dace sannan suka bata maganin zafi domin kafarta na ciwo sosai saboda tafiya, sai kuma na ciwon jiki da ciwon kai da na ido saboda kukan da suka sha har kammaninta sun sauya.
BAYAN KWANA BIYU….
Hajiya Kaltume ce zaune kan kujera Maama na matsa mata kafafuwan da har yanzu ba su daina mata zafi ba, domin bata taba gwada yin tafiyar da ta yi daga inda yan fashin dajin suka kamata ba zuwa sansaninsu, ko a lokacin da take da kurciya balle yanzu da girma ya fara kamata. Momy ce ta yi sallama ta shigo falon tana sanye da wada tsadadiyar shadda yar mali sai sheki take kamar an watsa mata ruwa, kana kallon shaddar ka san ranar ta fara sakata, wuyanta na cike da sarkar zinarin da ba ko wace matar mai kudi ce zata iya sakawa ba, gamshin da take ma na dabam ne domin Momy bata yarda ta siye turaren irin wanda Hajiya Kaltume ko Iyami za su iya siye ba ko da kuwa kudin da take da shi zai kare. Idan kana neman dake ji da kansu asalin ji da kai da nuna isa idan ka yi arba da Momy ka kai karshen aya. Maama ce ta amsa mata sallamar tana hada baki da Khairi dake fitowa daga kitchen rike da bowl din kankana. Hajiya Kaltume tun da ta kalli kofar falon ta ga Momy ce bata sake sha’awar kallon gurin ba. Tsaye Momy ta yi kusa da kujerar da Hajiya Kaltume take zaune abun ka da matan da tsibbo ya waya kuma suka wayance shi sai Hajiya Kaltume ta zame kafafuwanta daga hannun Maama ta matsa daga inda Momy take tsaye, jiki be bata banza ta kawo Momy bangaren ba, tunani take wani abun ta zo yi mata.
“Kaltume ashe an dawo”
Momy ta fada cikin izza tana Kiranta da Kaltume kai tsaye kamar yadda ta saba, tun zuwanta gidan taba taba kiranta da Hajiya ba balle kuma Yaya kamar yadda wasu matan suke yi idan za su kira uwargida ko da kuwa da sunan yaranta ne.
“Eh Allah ya nufa Nafisa”
Hajiya Kaltume ta amsa kamar an mata dole tana wani kashe ido. Momy ta tabe baki kamar wadda ta manta a falon Hajiya Kaltume take idan ma Hajiya bata ganinta kuma yaranta suna kallonta, amman tsabar raina uwarsu da ta yi da kuma rashin tsoron anyi an ce ya saka ta yin haka.
“Toh Allah kyauta gaba”
Maama da Khairi ne suka sam da Ameen, sukan tsoronta ya dade da cika musu ciki ba kamar mahaifiyarsu da take jin zata iya karawa da ita ba. Momy ta juya ta fara takawa kamar wanda bata son tafiya, haka yanayin ya ke tun tashi, sai dai lamarin ya samu promotion ne a lokacin da ta auri Alhaji Haruna Mai Yadi, saboda ta nunawa Hajiya Kaltume da Iyami ita yar sarauta ce kuma yar masu kudi ba Kamarsu.
“Mtsssss”
Hajiya Kaltume taja guntun tsaki tana bin bayanta da harara.
“Wallahi matar nan ta raina min hankali, wato na fahimci so ta yi na mutu gaba daya idan ba haka ba ace ma samu na kubuto hannun azzaluman mutanen nan da ba su san Allah ba, amman bata shigo ta min barka da dawowa sai yau da aka kwana biyu?”
Khairi ta mika mata bowl din watermelon din tare da fadar
“Hmmm Hajiya ai da baki dawi ba sai matar nan ta zuba ruwa kasa ta sha”
“Ai ni bayan Iyami bana da makiyiya irin Nafisa, kuma ita ma sai ta bar gidan nan da yardar Allah, komai sai ya dawo karkashin ikona sai na bata mamaki, ai Wallahi da ban dawo ba da sai Iyami ta ci ubanta dan sai ta gane kuskurenta, duk saboda ita na sha wannan bakar wahalar, duk dalilinta ne da bata aurar min miji ba da yanzu ban san wadannan yanta’adda da ba su da imani ba, yanzu na fito ga kanen can a daure”
“Hajiya ba su da Imani ko?”
Maama ta tambaya.
“Ina fa, ai babu imani a tare da su, abinci sa mun ji yunwa suke ba mu, idan dare yayi muna nan cikin hudu sai idan sun haska mu, sun dauremu sai kace awaki, sannan a ciyayi muke bacci, baba kalar kwaron da be cize ni ba, shi kam sauro ya samu abun nema style style yake mana na cizo, kuma duk ranar da aka yi waya ba a samu daidaituwa ba sai sun mana duka, kuma a kafa muka yi tafiyar nan har ciki daji, yara kanana na haife su amman haka suke juya ni kamar waina, Allah dai ya isar min akan Iyami kawai zan ce, kuma kiyayya yanzu na fara, dacan ina boyewa Wallahi yanzu a fili zan nuna bana sonta bana son yaranta, duk sai na ga bayansu”
“Hmmm Hajiya karki ga yadda Hurriya ta shigo falon nan tana ta zumudi ta ji dadi an kama ki har tambaya take”
Khairi ta shimfida mata fahimtarta akan Hurriya. Hajiya Kaltume ta cize baki.
“Shegya bakar dagga, daman idan bata yi murna ba ai bata cika yar kishiya ba, aiko sai ta gane shayi ruwa a gidan nan, ke shiga dakin yayanki ki kwaso min gilasan yarinyar nan gaba daya ki boye min su”
Kamar mai jiran umarni haka Khairi ta tashi da zafinta da murnarta ta nufi hanyar stairs. Maama ta tashi daga kasan da take zaune ta zauna kan kujera.
“Amman Hajiya Yaya Yasir zai iya gane dauka kika yi fa?”
“Ta ina zai gane fada masa zaki yi? Ko ma ya gane ai ba bayarwa zan yi ba, idan ya matsa min har shi ba zan ragawa ba, dan ni mai kaunar mai kaunar Iyami da yayanta ma bana kaunarsa, arzikinta daya ma dawo Wallahi da na mutu can da sai ta gane kurenta, kuma ita da Alhaji har abada”
Sosai ta hade fuska tana maganar irin hadewar da ya kara mata muni da bakin fata.
“Hajiya ai ba ita kadai ba, Hajiyar su Appa ma fa bata zo ba sai a waya ta kira, amman Wallahi da Amma ce da tun ranar zata iso gidan”
“Hmmm ita ai bata da wata power yanzu, ko ba komai a bakin rame take, kuma babu yadda zata yi da ni, bugu da kari kuma na kore matar da take so, sai na ga uban da zai dawo da ita a gidan nan”
Sun dade suna hirar Hajiya Binta da Maama kamin Khairi ta fito daga dakin Yasir da gilasan har uku ta nunawa Hajiya.
“Kin gansu Hajiya cikin closet dinsa ya saka su”
“Je ki yi musu mugun boyo idan ma bala’i yayi bala’i ki ce masa ni na dauka da kaina”
“Ba sai ance haka ba, kawai kowa yace be shiga dakin ba kuma babu wanda ya dauka”
“Shi ke nan, ya ma fi sauki”
Khairi ta fada a ganinta shawarar da yayarta Maama ta bada ta fi, sama da ta Hajiya Kaltume. Kamin Khairi ta isa stairs aka dauke wuta, a take hankali Hajiya Kaltume ya tashi domin har yanzu bata gama wartsakewa daga tashin hankali da azabar da ta sha a dajin ba.