VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

“Ranka ya dade kana bukatar wani abu?”

Inna Shatu ta tambaya tana mikewa tsaye.

“Aa na gode”

Ya amsa ba tare da ya kalleta ba.

“Toh”

Ta nufi kitchen domin ba zata iya fita cikin ruwa ba balle ta tafi gurin da suke zama, kuma ta san Momy tana hana su zama a falonta idan tana ciki ko bakinta suna nan. System din ya bude ya fara tabawa, yana tsaka da typing kofar falon da yi kara alamar da mutum a waje. Inna Shatu ta fito daga kitchen da saurin da nufin zata tafi ta bude.

“Lemme Handel it bari na bude”

“Tou”

Ta juya ta koma. Dauke hannunsa yayi daga typing din ya mike tsaye ya nufi kofar ya bude. He thought Hurriya zai gani domin ita ya san da shigowarta gidan, sai kuma yayi arba da Momy da Namra rike da umbrella suna mamakin ganinsa.

“Captain kai ne kuma?”

“Eh na zo baku nan ai”

Ya matsa jikin kofar suka shigo.

“Ka dade a nan?”

“Aa ban jima ba, Momy sannu da zuwa”

“Yauwa, ya aikin?”

“Alhamdulillah shi na zo na yi a nan ai”

“Captain sannu”

“Sannu Namra”

“Bari naje na canja”

“Okay”

Ya amsa mata ta siga biyu amfani da kai, da kuma furtawa. Momy ma ta bi bayanta tana fadin.

“Ai da na san zaka zo ba zan fita ba ma, gashi nan ruwa duk ya jika mu”

“Be kamata ai ka ki fita saboda ni ba”

“Babu wani abun da ya fi uwa ta saka danta a gaban ta yi ta kallo, da ka san irin dadin da nake ji idan ka zo gidan nan wata kila da kullum sai ka zo”

Murmushi kawai yayi ya bi su da kallo har suka haye stairs din. A madadin ya rufe kofar falon ya samu kansa ta takawa ya fita tare da janyo kofar ya rufe daga waje, balcony ya tsaya yana kallon yadda ni’imar Allah ke sauka ko’ina a gidan tana jika gidan. Dan matsawa yayi kadan yana takawa a hankali har ya isa gurin da ruwan yake zuba ya tara jikinsa ya saka hannunsa aljihu ya lumshe ido yana maida numfashi a hankali, sanyin ruwan saman dake sauka a kansa suna ratsa zuciyarsa da ilahirin jikinsa, da abun ya masa dadi sai ya daga kansa sama daga tsayen da yake ruwan na sauka a fuskarsa and the thing is so funny kana jin ruwa na sauka a fuskarka kamar an watsa maka wani abu. Haka ya jike kansa shakaf da ruwan saman hannayensa biyu duka cikin zube cikin aljihu daga ipod din dake kunnesa da wristwatch da wallet dinsa babu abun da be jike ba, shi ma ba wai ya shirya hakan ba ne, zuciyarsa ce ta ingiza shi har ya samun kansa da bukatar aikata abun da ya ga wata ta yi. Is he a teenager like her ya tambayi kansa kamin ya juyo ya kalli Namra dake masa magana…

 

Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar  MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne  cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai  shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo…

 

HURRIYA POV.

“Assalamu Alaikum Warahamatullah
Assalamu Alaikum Warahamatullah”

Ta sallame sallah magariba ta karo da azkar din sallah, sannan ta daga hannunta ta yi addu’a kusan rabin kowace addu’arta Amma ce, burinta Allah ya bata lafiya ta tare kamar da, sauran addu’o’in bukatu na rayuwa suna biyo baya ne bayan ta yi ma mahaifinta. Daf da zata shafa addu’ar Namra ta shigo dakin, saman gadonta ta jefa mata ledar dake hannunta kana ganinta kasan Hurriya ta shigar mata hanci da yawa.

“Na gaji da ajiyar wayar nan, idan ma baki bukata ki jefar ko ki kyautar, bana bukatar wani abu naki ko na Salim”

Ta juya tana jan kofar dakin da karfe Kamar zata ballata. Hurriya ta juya ta kalli ledar sannan ta mike tsaye ta nade carpet din ta zauna a bakin gadonta ta dauki ledar tana dubawa. Babbar waya ce har da sabon line da chocolate sai turare mai kamshi. Komai sai da ta bude ta gani musamman ma wayar da take jin kamar ta yi amfani da ita, sai dai tana tsoron kar Yayanta yayi magana domin bata taba rike waya ba, kuma kowa zai tambaye ta ina ta samu, idan ta amsa da cewar Salim ya bata za a tambaye ta miye alakarta da shi, to me zata ce? Wannan tunanin ne ya saka ta maida wayar a ledar ta cire chocolate din da turare ta janyo kwalin da Adam ya bata ta saka wayar a ciki, turaren kuma ta dora a mirror tare da sauran turarukanta da suke gurin. Sannan ta hau gado ta dauki chocolate ta fasa ta fara ci tana lumshe ido, daman ta san dadinsa domin Appa na siya mata lokacin da Amma take gidan, Amma ma da kanta takan siya mata ko ta bata kudi ta siya wani lokacin amman ban da wannan lokacin da komai ya canja. Knocked din kofar dakin aka yi, ta tashi da sauri tana cin chocolate din, kamar zata tambaya ta ce waye sai kuma wata zuciyar tace tashi ki duba mana, ta sauka saman gadon ta nufi kofar ta bude, Khairy ce tsaye tana lasa wayarta suna hada ido ta sakar mata murmushi ta kunno kai cikin dakin.

“Hurriya ruwa be saka ki zazzabi ba?”

“Aa”

Ta juyo tana amsa mata. Khairy ta kalli bakinta da hannunta.

“Me kike ci?”

“Chocolate”

“Eyyyy yar gayu, wannan mutumen da na gani a falo ya kawo miki?”

Tambayarta take irin tambayar nan mai halshen damo, tana wani murmushi ta kalailaye ido ita ga mai wayo. Ita kam Hurriya sai ta ji cewar ta samu mafita ai daman bata san ya amsawa mata ga wanda ya bata ba dan haka ta amsa mata da.

“Eh shi ya ba ni”

Khairy ta kama hannunta suka zauna bakin gado.

“Ba ni labari shi ma sonki yake?”

“Aa ni aa”

“To ai kin san ke din mai kyau ce ga farinjini, tsaraba ce?”

“Haka nan dai ya ba mu”

Hurriya ta amsa tana jin kanta guilty saboda ta yi karya, abun da ba halinta ba.

“Dan’uwan Momy ne ko, ina yawan ganinshi ai ance dan yayanta ne”

“Eh”

Ta amsa tana daukar dayan chocolate din ta mika mata, a nan Khairy ta juya ta kalli bayanta, Chocolate ta gani ba daya ba ba biyu ba uku ba zai kai 12 kala dabam dabam kuma duk masu tsada.

“Kin ce ba sonki yake ba, amman ya kawo miki chocolate haka, maybe dai baki son na sani ne ko? Haba Hurriya ki dauke ni kamar kawarki mana, ko da yake dai be kamata na takuraki ba”

Ta mike tsaye.

“Daman Hajiya ce ta ce na kiraki”

“Ni kuma? Me na yi to?”

“Sai kin yi laifi za a kiraki? Haba Hurriya karki ma Hajiya wannan kallon mana”

Hurriya ta hade yawu tare da sauran chocolate din dake makoshinta, gabanta ya shiga faduwa ita dai ta san alheri baya sakawa Hajiya Kaltume ta kirata, sai da ta wuce gaba sannan Hurriya ta bi bayanta gaba daya ta saka mata tunani cewar Hajiya Kaltume tana nemanta sai ta fara tunanin ko fitar da suka yi ne a dazun, ko dai wani abun aka shirya mata? Ko Hajiya Binta ta sake yi ma Hajiya Kaltume wata maganar ne? Da tambayoyi kala kala ta sauko stairs din, a daidai lokacin da Captain yake hada takardunsa Namra na saka masa laptop din a jakarta. Sai da ta fara kallon Khairy kamin ya kalli Hurriya dake biye da ita a baya, a shi da alaka ta Hurriya dan haka ba shi da hurumin tambayar ta ina zata je ko kuma da waye take tare. Sai da suka fice sannan ya kalli Namra ya ce.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected