VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

“Amma da baki saka Hamad din ba, Wallahi Hamad be mutu ba, karya suke yi Amma dan Allah ki cire, ki saka masa wani sunan ba Hamad ba”

Tana kuka tana rokon Amma a canjawa jaririn suna, Amma ta aje Little Hamad ta kama Hurriya ta rumgume.

“Hurriya dole mu karbi wannan gaskiyar, tana da daci amman dole ne mu karbi kaddara, duk yadda kike son Hamad na fi ki sonsa domin ni na yi nakudarsa na haife shi, una jin fiye da yadda kike ji”

“To me yasa kika sama Amma? Why? Why?”

Amma ta girgita da karfi tana kuka.

“Saboda ya mutu Hurriya, baki daya Allah ya karba ya bamu biyu ba? Toh sai mu gode masa, yadda ya so haka yake aikatawa, Hamad ya tafi tafiya ta har abada ya kamata ki karbi wannan, wannan shekarar haka ta zo mana”

Hurriya ta saki jikinta sai ta lankwasa ta yi baya Amma ta sake ta ta fadi kasan carpet din. Ita kam ta kasa yarda dan’uwanta ya tafi ya barta, fadan da suke yawan yi yake damunta a yanzu, why take ramawa idan yayi mata abun? Ko wane motsi yana tuna mata da dan’uwanta ne, bata taba sanin tana kaunarsa ba sai a yanzu da baya kusa da ita, ina ma ita aka dauka ba shi ba haka take yawan ayyana a ranta. Kusan kowa a gidan sai da yayi kuka kuma aka kasa wanda zai rarrasheta sai Yayanta Yasir, domin shi kadai ya fahimci manufarta kuma ya mara mata baya cewar Hamad be mutu ba, domin karbar gaskiyar cewar ya mutum shi ne ƙarya a zuciyarta.

****   ****     ****    ****

“Hajiya ki yi haƙuri dan Allah, bana son ina musa miki akan abubuwa, amman yaran nan da Iyami ta haifa nawa ne, idan ina buƙatar ganinsu ba sai na jira wani ya ba ni shawara ba, ayukan ne sun min yawa a yanzu amman da zarar na samu lokaci zan je na duba su, idan suka yi ƙwari ma aka yayensu ɗauko su zan yi na dawo da su gidana domin zuciyata ta fi amintuwa da haka”

Hajiya Binta ta kalleshi tana mamakin yadda yake ita bude baki ya musa mata a duk lokacin da ta yi masa maganar zuwa duba Twins din da Amma ta haifa.

“Tsoho me yake damunka? Wani lokaci ne baka da shi akan iyalinka?”

“Hajiya kin san kasuwanci ba daya ba, kuma idan ina son ganin yaran nan ni zan je da kai na, ina cw dai na sauke duk wani hakki na uba?”

“Toh baka bukatar ganinsu kenan? Haka kake nufi? Toh ni da nake bukatar ganinsu zan tafi, ko miye ya rufe maka ido ka kasa taka kafarka gidan Iyami Allah ya yaye maka shi tsoho, yau sati daya da haifa maka yan biyu kyautar Allah amman ka kasa taka kafarka ka duba yayanka”

“A gaishe su, Hajiya zan leko in Shaa Allah, kuma idan kin tafi ki fada mata next week Hurriya zata dawo zan aiko da mota a dauke ta saboda makaranta”

Yana maganar yana mikewa tsaye abun da be saba yi ba, ko magana Hajiya Binta take masa baya iya daga kai ya kalleta tsabar biyaya amman a yanzu duk ya canja mata, abun da be yi mata da kurciya ba a yanzu da girma ya kama shi yake canjawa. Baki saki Hajiya Binta ta fi danta da kallo har ya fice sannan ta girgiza kai hawaye na cika idonta.

“Allah ka shirya bawan nan naka, Allah ka karya duk wani abu da aka yi masa Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un”

Ta rafka uban tagumi tana kokarim ganin bata bar hawayenta sun zubo ba, domin ta san illar zubar hawayen uwa ga ďanta. Appa har ya isa gida bw daina ganin laifin Hajiya ba, ganin yake tana kusa masa cikin al’amurran da be kamata ta saka kanta ba, shi dai aka haifawa yara to damuwa kuma na me tun da har be ce ba yayansa ba ne, kuma yayi musu duk wata hidima da ya dace uba yayi ma ƴaƴansa. Ba ta inda ya ji sayin kamar ta gurin da Hajiya Kaltume take taba masa ita ma tana dorawa Hajiya Binta laifi, tana bashi gaskiya na kin son zuwan da yake.

“Gaskiya Hajiya ba a haka, ai sai ta saka maka ido ta gani, ina laifin bayan duk wata hidima, kuma yara idan suka yi wayo ai sai ka dawo da su nan gurin Momy ta cigaba da kula da su, tun da tana da masu aiki ba daya ba za su rika musu komai”

“Ni ma haka na gani, amman ta kasa fahimtata sai laifina take gani, gaba daya ta rufe ni da fada”

“Toh ya ka ayi, sai hakuri ka san bata hada Iyami da kowa ba a gidan nan, duk dai abun da yayi dalili ya raba amman dai Hajiya bata dauki kowa sukarta ba sai Iyami, wai ni yaushe Hurriya zata dawo ne Alhaji”

Tana maganar ya aje kofin ruwan dake hannunsa ya amsa mata.

“Next week, na fadawa Hajiya idan ta je ta fadawa Iyami zan aiko da mota a daukota saboda makaranta”

Hajiya Kaltume ta dan tabe baki tana shafa zanen atamfar dake jikinta.

“Makaranta ma ai bata jira Alhaji, yanzu kan sai dai a canja mata makaranta a maida ita Government School, ko ba komai ta dan rage kewar Hamad dan na san abun zai yi da damunta, amman idan ta koma wata makarantar sai ta samu sabin kawaye kewar zata dan ragu, kuma ka ga yanzu private school ai duk an yi nisa da karatu sai dai ta Gwafnati ita ce za su karbe ta ko dan lalurarta”

Appa yayi shiru kamar mai nazari, idea Hajiya Kaltume na cewa a saka ta wata makarantar ta government be masa ba, sai dai ba zai iya nuna mata haka ba.

“Ko kuma a kaita wata makaranta, amman makaranta government bata cika kyau ba, bayan kuma ga duka yan’uwanta a private suke, kuma kudin biya makaranta ai akwai shi ba babu ba”

“Ba shi zaka duba ba, yadda Hurriya take da kokari a makaranta ko’ina zata iya karantu, kuma zata gane kamar sauran yan’uwanta daman kuma ta fi su basira, ni dai gaskiya shawarar da nake baka Alhaji a kaita government schools kuma bana son ka musa min akan haka, kai fa ka san Hurriya kamar ƴa take a gurina, yadda ba zan so abun da zai cutar da Ruma ko Khairi ba ita ma ba zan so abun da zai cutar da ita ba”

“Shi ke nan, tun da haka kike so, za’ayi, Allah ya tabbatar mana da alheri”

Fuskar Hajiya Kaltume ta fadada da murmushi.

“Amin Alhaji na, Allah dai ya kara rufa asiri, ya kara wadata”

“Ameen”

Ya amsa cikin rashin dadin rai da be isa ya nuna a fili ba. Abun ku da makirar mace haka ta rika jan sa da hira tana tabo bangagori da dama na kasuwanci, sai dai be yarda ya fada mata abubuwan da take son sani ba, sai dai ta fahimci wasu bangarorin da kuma har ta nuna masa sha’awar na son fara kasuwanci. Appa ya saka dariya.

“Kaltume ina zaki iya kasuwanci crude oil? Kina mace? Wannan kuma ai sai mu maza”

“Hmmm Alhaji ka manta karin maganar da hausawa suke cewa duk abun da namiji zai iya mace ma zata iya? Ai mata ma kansu ya waye yanzu ana damawa da su sosai akan crude oil a yanzu”

“Amman yan boko Kaltume ke da ko primary ba ki yi ba ina ke ina wannan kasuwanci? Da ma dai Nafisa ce tace zata yi ba zan musa mata ba, domin ita tana kasuwanci sosai ta san kan kasuwanci domin shi ta karanta kuma mahaifinta ma kin san waye shi ba sai na fada miki ba, amman ke Kaltume ina ke ina wannan kasuwanci?”

A take fuskarta ta canja domin ya tabo mata inda bata so, dauko zancen Momy ya ce ta fita wani abu, bayan kuma ya gama yaga fuskarta cewar ko primary bata yi ba. Alhalin kuma gaskiya ya fada haka ta yi rayuwa rayuwar kauye ba arabi ba boko sai talla kamin ya aurota.

“Alhaji na ga dai kai ma ba kasuwanci ka karanta ba, amman kake kasuwancin nan gashi nan kuma yanzu ka koma dam bokon har turanci kana ji”

Appa ya cire gilashin idonsa yana dariya.

“Kaltume ni fa na yi boko kuma na yi zurfi kawai dai rayuwa ce ta yi tsanani kuma kasuwancin ya fi tsaya min a rai shiyasa na watsar, na fara kasuwanci kuma da yake arzikin a nan yake kin ga a yan bokon ne a karkashina, amman ke Kaltume da ko sunaki ba zaki iya dubutawa ba Allah cutarki za ayi”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected