Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Ni abun nan ya ba ni mamaki, wai waye yayi wannan aika-aikar”
“Zai wuce Kaltume? Ai bata son kowa da alheri a gidan nan kuma ta ga mota mai tsada ina za so haka, ballantana fitowar nan da ta yi dan uwa ko daya be je ya mata barka da fitowa ba”
“Amman Momy Yasir dai ba zai yi haka ba kin san ko da ta saka shi”
“Su matan fa? Kuma shi ma ba munafurci ba ne da nuna soyayyar ido, ai ta ciki na ciki dan’uwa be taba son dan’uba ba har abada”
“Ko kuma ta aiko wani yayi ba”
Ta juyo tare da Musib suka shigo falon, ko zama ba su yi ba motar Appa ta faka a harabar ya bude ya fito ya shigo cikin falon fuska a dauke.
“Ku ba mu guri zan yi magana da mahaifiyarku”
Appa ya fada immediately after ya rufe kofar falon, Musib ya dubi Miwan sannan suka tashi suka haura sama, Momy kuma ta zauna ita ma nata ran a bace tana sauraren da wacce Appa ya zo.
“Nafisa ina son na tambaye ki, akwai laifin da Hurriya ta yi miki ko kuma Hamad?”
“Wani abun aka fada kuma?”
“Akan wani dalili zaki nemi banbanta su da sauran yayanki? Fada min banbanci dake tsakinsu da Namra ko Miwan, dukansu ba Yayana ba ne? Akan wane dalili zaki ce Hurriya sai dai ta share dakinta da kanta kuma idan zata hau stairs ko ta sauka ba ta hau kamar yadda Namra ko Musib suke yi ba?”
Momy ta rike baki.
“Oh Allah na ni Nafisa, yaushe aka yi haka? Kuma shi kenan daga fada maka zance karya da gaskiya sai ka hau ka zauna har da zuwa gurin fada ba tare da ka tsaya ka bincika ba? Shiyasa ka dauko su ka kawo min? Me yasa ba a kaiwa Kaltume ba? Ita da yake tsoronta kake sai Nafisa da aka raina itace mai dadi hawa, gashi sai mulki take mana ciki gidan ita da yaranta”
“Daga ke har ita karkashin kulawata kuke kuma karkashin ikona, dan haka duk gurin da nake ra’ayi a can yarana za su zauna, kuma ina gargadinki wannan ya zama na karshe da zan sake jin wani abu marar dadi akan Hurriya da Hamad, zan iya canja mata ban zanja yaya ba, gaba daya yarana babu na yarwa kuma bana son a batawa kowa”
“Eh amman ai ka ware wadanda kake so kake kauna, na tabbatar da nawa yayan Kaltume ko Iyami take yi ma wani abu ba zaka yi magana ba, amman da yake yayan mowa ne ai gashi nan ka shigo falo cikin bacin rai saboda an taba yan gold, ni da zaka nuna musu kauna ka dawo da uwarsu ai da duk yafi wannan nema musu yanci da kake, idan ya so sai ta rike yayanta na rike nawa”
“Abun da na ga damar aiwatarwa shi zan aiwatar, babu mai fada min gabas, na san Allah, daman ke haka kike banta zuwa da wata magana ba ki musa min ba, ban taba fada kin yi shiru kin saurareni ba sai kin fada, sa’insa da ni ba yau kika fara ba, daga ke har Kaltume babu wadda nake jin sanyinta kowacce ku da lagon da take matsawa ta bata min rai”
Momy ta fashe da kuka domin kalaman Appa sun mata zafi, ta san abun da Appa ya fada akam Iyami gaskiya ne, domin ya saba yi mata fada ko a gabansu kamar yadda su ma zai iya musu a gabanta ko kuma ya tara su gaba daya yayi musu fadan idan wani abu ya faru, su kan tanka shi su kare kansu ko maida martani amman Iyami bata cewa idan yana fada har yayi ya gama, ko daga kai ba zata yi ta kalleshi ba, wannan ta saka suke yawan yi mata kallon munafuka, hawaye shar Momy take yi daman kuma bata gama hucewa daga bacin ran abun da aka yi ma Captain ba.
“Eh sai Iyami, abar kaunarka, yanzu gashi nan ka rufe da fada akan yayanta, matarka Kaltume kuma ta takura min ta takurawa bakina, yanzu Captain ne ya zo, ka san dai yadda nake da Captain amman haka matar nan ta saka aka fasa mata tayun mota saboda bakin ciki, ban gama huce wannan haushin ba gashi nan kai kuma ka zo ka rufe ni da wani, toh Wallahi ka jawa yayanka kunne su daina munafurci, kuma ka jawa matarka matarka kunne ta fita safgata da ta bakina babu ruwanta da ni idan ba haka ba Wallahi za ‘ayi tashin hankali da ba taba yi ba ko a lokacin da ka auro karamar yarinyar can Iyami”
“Ni dai na fada miki, karki sake banbanta min to ƴaƴa duk daya suke a gurina, babu wanda ya fi wani, zan iya canja mata ban canja ƴaƴa ba bana ni da kamar ƴaƴana!”
Yana kawai nan ya juya ya fice, cikin motarsa ya koma yaja ta zuwa bangare ya ajeta ya fito ya taka da kafa ya nufi bangaren Hajiya Kaltume yana shiga ita ma ya salllami yaranta suka haura sama ban da Yasir da baya gidan ma a lokacin ya fita gurin safgoginsa, Namra kuma ta fita zuwa bangarensu. Fada yayi mata sosai yana ja mata kunne akan abun da ta saka aka yi ma Momy.
“La’ilaha Illallahu ni Ummul Kultoon, yaushe kuma aka yi haka? Ni miye ruwana da Nafisa balle kuma bakinta, yanzu Fisabillahi na rasa me zan saka ayi mata sai fashe tayar baki? Abu dai kamar karamar yarinyar? Ni da nake ta kaina ma? Yaushe na fito daga daji? Kofar daki ma bana sha’awar fita balle kuma har na saka ayi wani abun, shigowar nan da ka yi ma hankalina sai da ya tashi”
“Ni dai na gargadeku, bana son wani tashin hankali kowa ya zauna lafiya kuma ya tsaya a iya matsayinsa, ku bar ni da abun da yake damuna, kullum ni ne cikin fitina kamar akaina aka fara mata aure da mata biyu”
“Mata uku dai Alhaji, yaushe ka saki yarinyar can Iyami da har zaka dawo kanmu nu kadai, musamman ni, taya za a ce na fasa tayar mota? Yara ma wa zan saka yayi wannan aiki? So take ta zugaka ka koreni a gidan kamar yadda ka kori Iyami, to Wallahi ni kam zama daram dam dam dam sai mutuwa, kuma Alhaji dan Allah ka rika bincike kamin ka fara fada, Wallahi sheri ne kawai na kishiya da neman hada mata da miji, abun da ba ayi ba da kurci ayi shi yanzu”
“Na dai ja muku kune, kowa ya tsaya iya matsayinsa bana son sake jin wata fitar”
Har Appa ya fice Hajiya Kaltume bata gama mamakin jin irin kagen da Momy ta yi mata ba, Salma ce ta fara saukowa sannan Khairi suna tambayar me ya faru domin sun lura da yadda mahaifinsu ya shigo cikin fushi.
“Wai munafurci matar nan ta hada, wai na tura an fashewa bakinta tayun mota, shi kuma babu tsayawa bincike da yake ta mallake shi komai ta fada masa shi yake yi kawai ya zo ya rufe ni da fada, ai bari Wallahi ita ma sai ta bar gidan nan Kamar yadda Iyami ta fitar da ni, waya sani ko gurin tsafinta ta tafi aka bata wani asirin ace ta zo ta hada mu, gaba daya ta mallake Alhaji ta juye masa kai komai ta fada sai ya hau ya zauna”
“Tab Lallai Momy ta yi nisa, wane irin fasa tayun mota kuma?”
Hajiya Kaltume ta kalli Salma dake maganar.
“Sheri ne kawai a samu yadda za a hada ni fada da Alhaji sai ya sake ni”
Haka Hajiya ta yi ta jininin maganar tana ta masifar har yamma.
*** *** ***
Hajiya Binta dake gidan baya tana shafa kan Hurriya dake kwance jikinta ta ce.
“Tsoho kamin ka kai ni gida, ina son ka biya da ni gidansu Iyami na dubata yaranta ma su ganta”
Kamar wadda aka cewa ya shiga ramen wuta haka Appa yaji, ko kadan be son abun da zai kusantashi da Iyami gashi kuma be isa ya musawa Hajiya ba.
“Toh Hajiya amman idan na aje ki Yasir zai zo ya dauke ki ya maida ke gida su kuma yara ya dawo da su”
“Toh zamu tafi gidan makiyiyarka ba, Allah ya kyauta”
“Haba Hajiya irin wannan maganar be dace ba a gaban yara ban da alheri me iyami ta yi min da zan dauki kiyaya na bita da ita”
Hajiya dai bata sake cewa komai ba har Appa ya canja hanya ya dauki hanyar gidansu Iyami. A bakin gate din ya faka, ya fito ya budewa Hajiya ta fito tare da Hurriya sannan Hamad ya bude front door ya fito.