VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Ta girgiza kai alamar aa. Sai ya fara fada mata yadda komai yayi kyau a jikinta yana tana hancinta da bakinta har sai da ta yi dariya.

“Taso mu yi alwala”

“Na yi a gida”

“Shi ne baki fada min ba na yi?”

Ya ja lebenta a hankali sannan ya sake ta ta tashi ta cire babbar rigarsa Falo ya fara fita ta rufe musu kofar gidan sannan ya dawo ya shiga bandaki yayi alwala ya fito ya shimfida musu carpet ya daga matarsa yana rike da ita ita ya tsayar sa ita daga baya shi kuma ya matsa gaba kadan ya tsaya kabbatar sallar. Cikin natsuwa suka yi sallah Nafisa yayi musu addu’a ya juyo ya kama goshinsa ya karanta addu’a sannan ya kwanto da ita jikinsa.

“Yan mata na…”

Ta yi shiru tana jin wani bakon al’amari da bata saba ji ba, wani yanayi take ji na dabam a tare da ita. Hannunsa ya saka aljihun rigarsa ya ciro dabinon da Daddy ya damka masa ranar da aka daura aurensu ya saka a bakinsa ya tauna dabinon da yawunsa sai da yayi taushi sannan ya saka hannunsa ya ciro ya kai mata saitin bakinta.

“Dabinon daurin aurenmu ne, ranar da Daddy ya ba ni a raina na ce zan aje sai kin tare mu ci a tare”

Ta bude bakin da tunin yawunsa da ya tauna dabinon da su suka jika mata lebe, ya saka mata a baki sannan ya lashe hannunsa, ya sake tauna wani har yayi taushi sannan ya dago fuskarta ya hade bakinsu suka ci dabino a tare. Kamin ya cire bakinsa ya kalli fuskarta yatsansa ya saka ya matsa hancinta har sai ta ta fara masa kukan shagwaba.

“Da zafi”

“Uhmmm wannan kawai tukuna ma”

Ya tsakani idonta yana murmushi, kamin ya tashi ya dauko musu abun tabawa, sai da ya fara ciyar da ita ta koshi sannan ya ci, daga bisani ya kawar da komai ya dauki Amaryarsa cak sai kan gado. Wardrobe ya dauko musu kayan bachi, sai da ya saka nasa sannan ya fara kokarin rabata da lifayar dake jikinta.

“Ke me yake zuciyarki? Hummm me kike tunani?”

Ya rada mata a kunnen kamin ya dago ya kalli fuskarta. Sai ta yi shiru domin bata da abun fada, tun da ba wani abu yayi mata ko yace mata ba.

“Kayan bachi zan saka miki”

Ta kanne kafada.

“Aa da wannan zan kwanta”

“Hey don’t try to act smart here”

Ta fara rare masa kuka a hankali, sai yayi murmushi yaje kayan bachin ya zauna kusa da ita ya rumgumeta. A dole ya hakura ya kyaleta ta yi bachi da lifayar har safe.

 

HAJIYA KALTUME POV.

“Kin ba ni kunya Khairy ban yi zaton zaki iya haka a gaban mutane ba, idan ma neman yafiyarta zaki yi ai sai ki yi daga ke sai ita a cikin mutane ba, yanzu ai ta ji dadi ita da Iyami sai su ce gashi nan kina kuka kina neman yafiyarta”

“Hajiya wanda aka yada video shi a duniya kamar ni da yana da sauran jin kunya ne? Ni fa yanzu rayuwata ta kare, da ina tunanin auren Fadeel zai rufe abubuwa da yawa akaina kuma ya saka ni jin sanyi amman haka ya gagara, shi ma ya juya min baya”

Ruma ta kalli Hajiya cike da damuwa ta ce.

“Hakan da ta yi ba laifi ba ne Hajiya, idan ba irin yau ba yaushe zata roki yafiyarta?”

Hajiya Kaltume ta ja tsaki, bakinciki ya zame mata kashi kashi. Khairy ta mike tsaye tana kuka ta haura sama ta shiga dakinta sai ta kife akan gado ta fashe da kuka.

“Ka cutar da ni Adam.. Ka gama da rayuwata ka ruguza shiri ka tarwatsa duniyata wayyo Allah na…”

Kuka take sosai tana jin kamar ace adam din yana kusa da ita ta kashe shi ko ta rage zafi, can kuma ta dago ta nufi wayarta ta dauka ta kama number Adam ta aika masa da sako.

 

Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo…

*Shafin nan sadaukarwa ce gareki  UMMU FAISAK my albasa my tomato my pepper, jikar Iya kawar Amo da Hajiya Kaltume. Alherin Allah ya kai miki har a gadon baccinki*

***    ***    ***

_Wallahi baka taba yin farinciki a rayuwarka ba Adam kamar yadda ni ma ba zan yi ba, ba zaka taba ganin haske ba, sai na bayyanama duniya abun da kake boyewa sai na hana ko wace mace aurenka, baka da zabin rayuwa daga yanzu har zuwa mutuwarka, idan ban auru ba ba zaka auru ba Adam…_

Yana gama karanta sakon ya dan dago ya kalli mutanen dake falon sannan ya maida kansa yayi mata reply.

_Mu zuba zuwa Khairy, ni da za a ga shege, kuma ni sai na auri macen da nake so nake ra’ayi amman ke ba zaki taba auren mijin da kike so ba, saboda kowa ya san me na yi miki kuma idan kika matsa asirin ba nawa kadai zai bayyana ba har da naki domin ke ma yanzu ya shafe ki kin ga sai mu yi jinya tare_

Yana bata amsa ya aje wayar ya cigaba da kallon tv rai a bace, Salim ya taso daga inda yake zaune ya nufo Adam.

“Ara min wayarka zan sauke app wayata ya ki sauke shi”

Without second though Adam ya mikawa Salim wayar ya tashi ya hanyar dakinsa. Salim ya zauna a gurin da Adam ya tashi yana.

“Akwai pin a jiki”

Adam ya dawo ya cire masa pin sin sannan ya shige dakinsa. Kai tsaye a Salim ya shiga whatsapp dinsa yana duba recent chat ne ga wani abun daga hankali ko bata rai ba, yana kokarin fitowa daga whatsapp din sakon Khairy ya sake shigo ta SMS.

“Mu zuba zuwa ni da kai shege ka fasa Adam”

Ya haka ya samu bin sakon ya karanta har wadda ta aiko masa da farko. Salim ya dan dago da mamaki kamin ya sake maida kansa, wannan ne karo na biyu da ya sake ganin wani abu da ya daga masa hankali a wayar Adam. Da kansa ya shiga dakinsa ya mika masa wayarsa sannan ya fito harabar gidan zuciyarsa na zafi. Domin ganin yakw yanzu ya zama loser shi ya fara son Hurriya amman abokinsa yayi masa overtaking duk kuwa da irin yadda aka bata sunan Hurriya,  it pain him yadda abokinsa yayi betrayed dinsa. Number Namra ya kira domin sauke mata haushin dake ransa.

Namra ta share hawayenta sannan ta kalli wayar dake gefenta ta dauka.

“Hello”

“Burinku ya cika? Kun nani Hurriya kun bawa wani?”

“Wane irin magana ne wannan? Wa yake murna da wannan auren ne? Kai kanka ka san Hurriya bata dace da Captain”

“Bata dace da shi ba ta aure shi? Na yi zaton ma kina can gurin raka amarya ai”

“Zan aje wayar idan baka da wata magana mai muhimmanci, ina cikin damuwa ba zan yarda ka kara min wata ba”

“Baki da matsala daman saboda ba ke kika rasa ba”

“Idan har da gaske kake kana kaunarta me ya hana ka fitowa ka aureta kamar yadda Captain yayi?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected