Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
Hurriya ta sauke ajiyar zuciya, daman ta raya a zuciyarta cewar kawarta ba zata aikata mata wani abun da zai jefata a damuwa ba da ganganci.
“Amman Hurriya ke da kika samu komawa gidan Hajiya meyasa kika dawo nan?”
Nan ma sai da Hurriya ta fada mata abun da ya faru, ciki kuwa har da rumgumar da Khairy ta yi mata a yau.
“Eh gaskiya kara da kika dawo, kuma ko yanzu ki yi taka tsantsan, saboda su ya saka bana son yawaita shigowa gidan nan, yanzu kuma gashi kin fada min abun da ake kallonki da shi kuma na san ni za a kalla a matsayin mai tayaki”
“Su suka sani, ai Allah yana shaidata”
“Haka ne, kin ma san abun da ya kawo ni wai?”
Hurriya ta girgiza kai tana kallon Husna.
“Wani abokin yaya ne yace kin san shi sunansa Salim ya ce min har kun yi magana amman ya rasa ya zai shawo kanki, shi ne ya zo jiya saboda ya gan mu tare lokacin da kika je gidan kuma ya tambayi Yayana ya fada masa ni kawarki ce sosai, tare da Yaya ma suka saka ni a gaba wai yana son na lallabaki na karkarto da hankalinki ki fahimce shi, shi ba da yaudara ya zo ba…”
Hurriya ta mike tsaye ta dafe kanta tana yawuta a dakin.
“Ni kam na shiga uku, mutumen so yake ya ballo min wasu ruwan kuma? Yaushe na samu na rabu da Adam shi kuma ya kuso yana son haddasa min fitina, na yi magana da shi na fada masa cewar ni bana sonsa kuma fa ma Yaya Namra yake so daga baya ne ya dawo guna”
“Duk ya fada min, amman yace ke ce baki fahimta ba, ko kuma yayarki ce take son bata lamarin amman shi tun farko ke yake so, kuma Hurriya ni fa ina ganin idan da gaske yake kuma aka bincika yana da halin kwarai sannan aka dace kina sonsa kawai ki aure shi ki huta da wannan gidan, albashi idan zaku yi aure sai ya miki alkawarin zai barki ki yi karatu”
Hurriya ta dawo ta zauna.
“Ni be min ba, kuma na fada masa gaskiya wata kila ma saboda shi ne na ga Yaya Namra ta canja min, sai ta yi zaton ko ina kokarin kwace mata saurayi ne, kuma fa tana son shi, ni gaskiya bana sonsa ni babu ma wanda nake so yanzu”
“Shi kuma yana sonki sosai Hurriya da ace zaki ba shi dama dai zaki saurareshi, ya ce min ma zai zo gobe”
“Dan Allah kar ya zo kar ya hada ni da mutane, ki fada masa kar ya zo dan Allah, Husna kin san halin da nake ciki ki fahimtar da shi mana”
Ta karasa tana cikin son yin kuka idonta na tara ruwan hawaye.
“Zan yi magana da shi, zan fada masa yadda zai fahimta, yanzu ya maganar karatunki”
“Ni dai yanzu ki tashi ki tafi kar ace na shigo da ke a daki muna gulma”
Husna bata da wani aiki a yanzu da ya wuce ta taimaki kawarta dan haka ta mike tsaye ta yi mata sallama, cikin tsoro Hurriya ta raka falo, hankalinta be kwanta ba har sai da Husna ta fice. Sannan ta dafa zuciyarta kamin ta sauke hannun ta koma dakinta, sallah ta yi ta fito falon ta zuba abincin rana ta ci.
**** **** ****
Karamin filo ne a hannunta ta rumgume shi sosai a kirjinta, kalaman da Momy ta fada mata dazun take tunanin, suna kokarin dorata a wani tsani da bata taba hawa ba, zancen ana son su fahimci juna ita da Captain ta tsaya mata a rai. Yana da kyau da za a so shi, yana da cikar halitta da duk wani abu da ake so a jikin namiji, sai dai ganin yadda tsarin rayuwarsa yake ya saka bata taba ayyana ma kanta kaunarsa ko sau daya a zuciyarta ba. Ta dago ta kalli wayarta dake ringing ganin sunan Salim ya saka ta dan yamutsa fuska kamar ba zata daga ba, can kuma ta kai hannu ta dauka.
“Hello”
“Namra ya gida, ko da yake yayarmu ya kamata na ce”
“Haka fa, lafiya kalau ya aiki?”
“Alhamdulillah, alfarma na kira na roka kamar yadda na saba yi, kanwar nan taki dai na kasa hakura da ita, na gwada ko zan iya amman na kasa”
“Toh yanzu kuma me zan yi?”
“Lallaba min ita zaki yi, yau ma zan shigo gidan kuma tare da dan’uwanki In Sha Allah”
Har zata tambaya ta ce wani dan’uwanta sai kuma ta ji bata bukatar hakan, domin ya nuna ba ita yake ra’ayi ba, dan haka be kamata ace ta shiga hancinsa ba.
“Okay zan yi kokari, amman daga wannan ba zan sake ba gaskiya, baka fada min ya kuka kare ba a wacan karon”
“Idan na zo zamu yi maganar”
“Okay”
“Thanks”
Ta cire wayar kunnenta tana hautsina fuska, kamar zata ji haushinsa kuma sai take ganin babu dalilin haka. Aje fillon tayi ta sauko saman gadon,
‘Babu wani lalaba ta da zan yi, yarinya ta nuna vata yinka dole ne, ai maganin namiji mai shegen ruwan ido kenan da son mata’
Ta fada a ranta kamin wasu zantunka su fara zagayar kwakwalwarta, yanzu da Momy ta fada mata kudirin da suke da shi akansu ita da Captain sai take ganin wata kila canja mata ne Allah zai yi da son Salim da ta fara, ya bata wanda ya fi shi komai, dan murmushi mai kyau ne ya kawata fuskarta, ta mike tsaye ta nufi kofar dakinta ta bude sai da ta shiga dakin Momy ta duba bata ciki sannan ta sauko kasa domin ta san idan bata dakinta to tana kasa ko bangaren mahaifinsu ko kuma ta fita daga gidan. Tun kamin ta karasa saukowa stairs ta ji fadan da Momy take yi ma Hurriya har da rantse rantsen abun da zata mata idan ta sake zuwa kai tsaye ta bude mata kuloli ta zuba abinci.
“An gama abinci ban zubawa mijina ba, ni ban zuba ba sai ke ki zuba ke gaki issashiya ko? To ba zan daukar miki wannan ba, daga yau sai yau karki sake bude min kula ki zuba abinci ki jira sai na diba, ai na fada miki nan ba bangaren Iyami ne ba, wannan rashin tarbiyar da kuke ni ba zan dauke shi ba”
“Ki yi hakuri Momy, hakan ba zai sake faruwa ba”
Hurriya ta fada cikin muryarta mai sanyi, dake nuna tsantsar nadamarta. Momy ta sake daka mata tsawa.
“Idan ma ya faru ke ce a matsala domin kanki zaki jawa bala’i”
Hurriya ta ji kamar ace zata iya gyara komai kamar bata taba ba, amman ba dama domin mai afkuwa ta afku, cikin tsananin damuwa ta nufi stairs tana tambayar kanta.
‘Wai haka ko wace ya take fuskarta matsala a gurin kishiyoyin uwa, ko kuma ita ce ta fita dabam?’
Bata da mai amsa mata tambayarta kamar yadda ita ma bata san amsar ta ba. Namra ta bita da kallo har ta haye sannan ta sauko.
“Abinci ta zuba?”
“Eh saboda iskanci da rainin wayo, ni kaina ban zuba ba amman ta zo ta bude warmers ta zuba abinci”
“Wani sabon iskanci ne ta kirkiro kuma yanzu?”
“Oho mata ita zata sha wahala ai”
Momy taja kujera ta zauna, Namra ma ta ja nata kujerar ta zauna, sannan Momy ta fara zuba abincin.
A bangaren Hajiya Kaltume kuwa tana shiga dakinta ta dauki wayarta ta kira, Malam rashin samun wayarsa ya saka ta kira kawarta.
“Ikon Allah, hausawa suka ce dan halak kaki ambato, yanzu fa nake son kiranki na tambaya size din Khairy na talkami”
Hajiya Fatee ta fada daga dayan bangaren bayan ta amsa wayar kawarta Hajiya Kaltume.
“Hmmm ai ni wani abun ne na ji da ya so daga min hankali, kuma dai be daga ba shiyasa na kiraki”
“Me ya faru?”
“Wai anya baki tunanin Malamin nan yana tayar da aikin da muke ba shi ne saboda ya bukaci wani abu?”
“Ah touh Hajiya na ga cikin nan naki fa an kwantar kuma ya kwanta daga baya abu ya tashi, har kika ce ya bukaci wani abu agareki, ni na ma manta ban tambayeki me ya bukata ba”
“Hmmm wannan maganar kuma ai ta wuce Hajiya Kaltume ciki kuma ya koma ya kwanta yadda ake bukata, ke dai yanzu me sa kika kira ni kuma me ya daga miki hankali tukuna bari mu ji na ki”
“Salma ce ta dawo dazun, bayan ta huta take min hirar wai mahaifinta yana son kawarta”