VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

“Gwaggo karki gayan magana, to faduwa zan yi na yi birgima? Ko kuma an fada miki ni din kamar yarki ce Iyami da bata yarda da kaddara ba? Ai ma dai da kunya Wallahi ku tako gidan nan da sunan ganin Alhaji shi be nemu ba ku za su neme sa, abu dai kamar ba Fulani ba”

“Ba rokonsa muka zo akan ya ba mu wani abu ba, kuma ba zuwa muka yi akan ya maida Iyami ba, shi ne abun kunya, mun zo ne saboda Hamad, ai kin san ko an rabu idan akwai yaya kamar ba a rabu ba ne, sai hakuri Hajiya Kaltume Iyami dai ta zama murucin kan dutse, ta zama kadangaren bakin tulu, kuma ta zama ƙashin wuya bata haɗuwa bata amayuwa”

Maama ta juyo tare da tasowa daga dinning din zata fadawa Gwaggo magana Hajiya Kaltume ta yi saurin daga mata hannu.

“Babu ruwanki Maama je ki cigaba da cin abincinki, Allah dai baya baci zalinci da kuka min sai ya saka min macuta kawai masu abun kunya”

Hankali kwance Gwaggo ta ce.

“Ba mu da abun kunya, da muna da abun kunya mijinki ba zan lallaba ya nemi hada iri da mu ba, kuma Alhamdulillah ko yanzu kasuwa ta watse ɗan koli mai rabo ya ci riba, tun da ga ƴaƴa nan Allah ha raya su ya saka musu albarka”

Gwaggo na kaiwa nan ta kabe Hijabinta ta fice daga falon ta bar Hajiya Kaltume da ciwon rai. Ko da Gwaggo ta iso gurin Bappa na nasa masifar Yasir na bashi hakuri.

“Bappa ka yi hakuri Wata kila ransa ne a bace”

“Idan ransa ne a bace be san waye ni ba da zai fada min maganar banza?”

Gwaggo ta dubi Yasir ta dubi Bappa.

“Malam lafiya?”

“Yasir ya shiga ya kira min Alhaji Haruna, daker mutumen ya fito, kuma abun da yake fada min shi be da miliyan dari biyu da zai bada yanzu, kuma ina damunsa da kira ban san damuwarsa ba, ai ba Hamad kadai aka dauka ba har da yarsa amman mun daga masa hankali kamar Hamad ne kadai ďa, idan muna da kudin mu ba su mu karbo Hamad din har da rubuto min number mutanen ya turo min, wai shi ba zai bada kudi ba police sun ce za su karbo su”

“Hmmm Allah ya kyauta, tun da ya baka Number mu tafi Malam”

Yasir ya nufi Gwaggo cikin rashin jindadin abun da ya faru yana bata hakuri

“Gwaggo dan Allah ku yi hakuri, maybe damuwa ce ta yi ma Appa yawa, dan Allah ku yi hakuri ba halinsa ba ne Wallahi”

“Karka damu Yasir babu komai”

Gwaggo ta fada sannan ta bude motar ta shiga, Bappa yaja motar sai masifa yake ta yi domin yau Alhaji Haruna yayi masa abun da be taba masa ba.

“Har yana cewa muje mu biya kudin ganin yake kamar ba zamu iya ba ko? Har yaushe za a bata lokaci gurin jiran abun da baka san faruwarsa ba? Ko bayan haka ni bana je akan ya bada kudi ba, naje ne mu yi magana ta fahimta da shi na ji halin da ake ciki, amman mutumen ko kallona baya son yi, sai fada yake kamar shi ne uban ni ne dan, na fada masa ni ba zan dauki wannan rainin wayon ba, kuma ni da gidansa har abada, wato saboda ya saki Iyami shiyasa yanzu baya ganin kimarmu ko?”

“Allah kadai ya san abun da yake nan Malam, Allah dai ya isarwa Iyami da yaranta Allah ya saka mata da gaggawa”

Gwaggo tana addu’a tana kuka daman idan ranta ya bace bata da wuyar kuka.

 

_________________

Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo…

@

Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660

4️⃣

“Gaba daya an juye kan Alhaji Haruna, kuma ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba, ba zai wuce Kaltume ba, domin bata hada hanya da imani ba, kai ko gurin da ya bi ya wuce bata bi ba”

Amma ta share hawayenta bayan ta gama sauraren Gwaggo dake fada mata abun da ya faru.

“Ni yanzu ba ta Kaltume nake ba ko Alhaji, ta dana nake burina ma ga ya fito, kuma tun da har ya kai ga furta cewar ba zai bada kudin ba, ni zan bada albashi shi sai ya bada na Ruma”

“Ko daukar yaron nan da aka yi bana raba dayan biyu, Kaltume ce ta saka aka sace shi, yadda na ga ta sha ado ta sauko hankali kwance har tana neman fada min magana ya isa ya tabbatar da cewar da sa hannunta aka sace yaron nan, tasan yarta tana cikin kwanciyar hankali shiyasa hakan be daga mata hankali ba, kuma yanzu na kara tabbatar da ita ce ta aiko Maama gidan nan saboda ta rabaki da dan abun da kike da shi, ni dai da zaki yarda da shawarata da kin saurara karki kira su ki kyale su da yaron ki gani shi za a karbo Ruma ba a karbo Hamad ba?”

Amma ta daga kai ta kalli Hurriya dake zaune a waje tana cin indomie da Gwaggo ta dafa mata kamin ta fita.

“Gwaggo shin idan wani yayi garkuwa da ni yace sai an bashi kudi alhalin kina da hanyar za ki bi ku bada kudin nan zaki bada ko kuma zaki tsaya jiran sai ranar da wani ya bada ne?”

“Zan fada”

“Toh ki saka kani a matsayinki, ni ma fa uwa ce tun daga lokacin da na baro gidan uban yaran nan kullum da kalar tunanin da nake kwana a raina balle kuma yanzu da yarona yake hannun wasu mutane da ba mutanen kirki ba, marasa tsoron Allah, duk abun da nake da shi a duniyar nan be kai ran Hamad ba, Gwaggo ko rayuwata suke ce sai na basu sannan za su sako Hamad Wallahi zan ba su”

Tana maganar hawaye masu zafi na sauko mata, ita kadai take iya jin abun da ko wace uwa take iya ji idan danta ya shiga mugun hannu.

“Kana ina dana? Ka ci abinci baka ci ba? Wane kalar abinci suke baka, ina kake kwanciya? Suna azabtar da kai ko basa yi? Ka yi marmarin gida?”

Amma ta gargiza kai tana kara jin ba zata iya jure har lokacin da Appa zai ga dama ya biya kudin ba. Haka kuwa aka yi, Bappa ma ya bata goyon baya domim ransa ya bace sosai akan abun da Alhaji Haruna yayi masa, Amma da kanta ta kira number da aka bata sai suka tararda line a kashe, sai dai mai neman baya fitar da rai, jajircewa suka yi ta yi suna kiran line kullum ba dare ba rana ba safiya, har suka yi sa’a a rana ta uku kiran ya shiga da misalin karfe goma sha daya na dare. Abun da baka saba ba zuciyar Amma ta hau zillo tsoro ya kamata kamar suna gabanta, duk kokarin da Bappa yayi na ba su Hamad su yi magana da shi sai mutanen suka ki, Bappa ya tambaye ina za a kai musu kudin suka fadi gurin da za akai musu kudin a aje, wani kasurgumim daji ne dake tsakanin mafara da Gusau.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected