VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

 

HURRIYA POV.

“Daure ki sha tea ne kuma ba mai yawa ba”

Hajiya Binta na lalabata tana hada mata tea. Gwaggo ta ce.

“Babu yadda ban yi da ita ba amman ta ki cin komai tun safe har yanzu”

“Bana iya cin komai ne, ko na ci bana iya hadewa”

“Hurriya wannan abun duk zai wuce, wata kila an buga an buga an ga babu sa’a ne shi ne aka bullo ta nan, amman duk wanda ya sanki ya san ba zaki aikata ba, babu wanda zai yarda kawai ana son a jefaki a damuwa ne, dan haka karki bari damuwar da suke son jefaki ta tasirantu akanki karbi ki sha”

Ta mika hannu tana lalaben kofin ta karba ta kai bakinta ta kurba kadan sai ta gagara hadewa.

“Hajiya bana iya hadewa”

Hajiya ta karbi kofin ta rike tana kallon jikarta cike da damuwa sosai a fuskarta.

“Jibi zan wuce Ummara zan miki addu’a mai karfi a can, da yardar Allah wanda ya aikata miki haka ba zai sake sanin rahma a rayuwarsa ba”

“Amin Hajiya”

Gwaggo ta amsa, sannan suka daga kai gaban dayansu suka kalli kofar dakin da aka turo. Cikin wani irin yanayi kamar na kunya kamar tsoro Yasir ya shigo dakin fuskarsa a raunane.

“Yasir”

“Na’am Hajiya”

Hurriya ta sauke kanta kasa duk da kasancewar bata ganin kowa tana jin kunyar aga fuskarta saboda an yada tsiraicinta. Yasir ya tsaya daga tsaye suka gaisa da Hajiya da Gwaggo be ce da Hurriya komai ba ita ma bata iya dagowa ba balle tace masa wani ba sai hawaye take.

“Appa ya ce na zo da Hurriya”

“Ka zo da ita kuma? Be san tana asibiti ba?”

“Ya sani, yace na yi magana da likitan ya bata sallama”

“Saboda me? Be san idonta ya samu matsala ba?”

“Ya sani Namra ta fada mana komai, Hajiya idan za ayi mata aikin idon a ba nan za’ayi ba kuma abu ne da yake bukatar shiri da tantance inda ya kamata da kuma likitan da ya dace”

Hajiya zata sake magana Gwaggo ta dakatar da ita

“Je ka karbo sallamar, zamu tafi da ita mu ga iya gudun ruwansa amman ba zan bar Hurriya ta zauna a gidan nan ba har bada…!”

Yasir ya juya ya fita daga dakin ba tare da yace komai ba, Hajiya Binta kuma ta hau masifa ta daga wayarta ta kira shi kiran be shiga ba. Misalin karfe biyar da mintuna Yasir ya faka a harabar Appa, Gwaggo ta fara fita sannan ta fito da Hurriya Hajiya Binta ma ta fito tana kara shiryawa duk wani abu da ďanta zai yi. Hurriya ta kama hannun Gwaggo ta rike da karfi.

“Gwaggo tsoro yake kar Appa yace be yafe min ba”

“Ko da ya fada ba zai kama ki ba, domin ba ki aikata ba kuma Allah mai adalci ne”

Cikin karayar zuciya da duhun idanuwa Hurriya ya shiga bangaren na Appa Gwaggo tana mata jagora komai bata iya banbance komai a yanzu. Yanayin yadda ta ji numfashi na tashi ya karantar da ita falon cike da mutane da bata san su waye ba, yan gidansu ne kadai ko kuma dai duka familynsu da suke garin. Me Appa zai fada akanta shi ne abun da ya fi tsorata ta, da lalabe ta zauna a falon kusa da Gwaggo, hawaye na mata zuba, ta wani bangaren tana gode Allah da bata iya ganin komai, a yanzu da bata san da wane ido zata kalli Appanta ba.

“Hurriya…!!!”

Gabanta ta kasa amsa kiran da Appa yayi mata gabanta sai bugawa yake da karfi.

“Kina da wata hujja ta kare kanki akan abun da muka gani tsakanin jiya zuwa yau?”

Ta yi shiru, Gwaggo ta ce.

“Ka san dai ba zata aikata ba…”

“Gwaggo dan Allah ki yi hakuri ki bari ta amsa min”

Appa ya bukata cikin yanayi da ke nuna shi ma yana cikin damuwa kwatankwacin wanda Hurriya take ciki.

“Appa akai ni na yi alwala”

Tana fada ta mike tsaye tana kuka.

“Ba sai kin rantse ba abun da duk ba halinki ba ba zaki aikata shi ba”

Hurriya ta girgiza ma Hajiya Binta kai ba dan tana ganinta ba.

“Idan ban rantse ba babu wanda zai yarda da ni, ni ma kuma ba zan samu sukuni ba, dan Allah ku kai ni bandaki”

Yasir ya kalli Ruma.

“Tashi ki kaita”

Ruma ta tashi ta rika hannunta suka shiga bandakin dake cikin falon, Hurriya ta yi alwala ta fito ta bukaci a bata kur’ane.

“Bari zaka yi ta yi rantsuwar nan Tsoho?”

Appa ya kasa amsawa mahaifiyarsa, shi ma ji yake kamar Hurriya ba zai aikata hakan ba sai dai zuciyarsa ta kasa natsuwa. Yasir ya tashi da shiga bandakin da Hurriya ta fito yayi alwala ya shiga bedroom din Appa ya dauko mata alkur’ane ya kama hannu ya mika mata, shi kansa idan ta rantse zai fi jin natsuwa, domin ya shirya ui mata mummunan hukuncin idan har ta tabbata ta aikata. Hurriya ta rike qur’anen da dayan hannunta sai ta dora hannunta na dama a saman kur’ane ta dafa.

“Na rantse da littafin nan, abun da yake cikinsa da wanda ya aiko da shi ban aikata ba Appa”

Ta karasa cikin kuka… Gwaggo ta saka kalma shahada.

“La’ilaha Illaha Muhammad Rasulullah”

Sai gaba daya falon ya amsa suka karasa a tare.

“Sallalahu Alaihi Wassalam…”

Appa ma ya sauke kansa kasa ya fashe da kuka, babu wanda be yi hawaye ba a falon kuma babu wanda be tausaya mata ba ciki har da Momy. Yasir ya sa hannu ya karba yana hawaye da murmushi a fuskarsa, yar’uwarsa ta tsarkake kanta a gaban kowa hakan ya kwantar masa da hankali yanzu kam ya yarda hundred percent bata aikata ba.. Appa ya dago hawaye na zubowa daga idonsa ya mika mata kamar ance masa tana ganinsa.

“Zo nan gareni yata, fada min wa kika tarewa farinciki ya aikata miki haka?”

Hurriya ta fara takawa ta inda take jiyo sautin muryarsa tana kuka tana lalaben hanya, Yasir ya rika hannunta ya karasa ta ita gurin Appa, hannayensa ta fara kamawa sannan ta zube kasa a gabansa ta kwantar da kanta a kafarsa.

“Allah ya tsinewa wanda ya aikata miki wannan abun Hurriya, ba zai gama lafiya ba, bakinciki da ya saka mana da neman bata miki da sunan gidan nan Allah ya ninka masa shi…”

Kowa ya amsa da Ameen ban da Khairy da Namra dake ta kuka kai ka rantse da Allah su aka aikatawa haka ba Hurriya ba.

“Ba zan bar maganar nan ba, sai na yi shari’a da yaron nan, ya ci mutuncina ya ci mutuncin ƴata ba zan kyale shi ba”

“Ni ma na yi wannan tunanin Appa, na kudirta a raina idan har ta tabbata Hurriya bata aikata abun nan ba, ba zan kyale maganar nan ba”

Yasir na aje aya Hajiya Binta ta ce.

“Da kun kyauta daman be kamata a kyale ba”

Momy ta tashi ta fice ba tare da tace komai ba, Ruma ta bi bayanta. Gwaggo ma ta mike tsaye fuska a daure ta ce.

“Zan tafi gida, kuma zan tafi tare da Hurriya saboda a can zata samu kulawa”

Appa be ce komai ba bayan shafa kan Hurriya da yake, har Gwaggo ta iso gurin ta kama hannunta suka fice. Sai da suka kusa isa gate sannan Yasir ya cin musu da mota ya bukaci su shigo ciki ya sauke su gida, Gwaggo kamar bata shiga ba saboda yana dan Hajiya Kaltume sai kuma ya daure ta shiga saboda saukaka Hurriya wahalar fita titi zuwa neman abun hawa. Back seat suka shiga ita da Hurriya har suka isa Yasir be yi wata magana ba, balle kuma Gwaggo da ta matsu su sauka a motarsa. Har cikin gidan ya faka ya fito ya budewa Gwaggo ta fito ita kuma ta riko Hurriya ta fito suka shiga cikin gidan. Yasir ya bisu da kallo gaba daya Hurriya ta zama abun tausayi a yanzu.

“Kina ganin jarabawa Hurriya”

Ya furta sannan ya sauke ajiyar zuciya ya bude motarsa ya shiga. Rukayya na ganin Hurriya ta shigo falon tana lalabe sai ta fashe da kuka ta saki kofin kurar da zata bawa Amma ta nufi Hurriya ta rumgume ta suna kuka. Gwaggo ta girgiza mata kai domin bata son Amma ta sani, sai dai abin da bata sani ba Rukkaya ta fada ma Amma komai bayan tafiyarta.
Jin kukan Hurriya sai ya saka Amma ma ta fashe da kuka, kukan da ta shekara hudu bata yi irinsa ba, kukan da tun da ciwon ya kamata bata taba kuka anji muryarta ba sai yau. Hurriya na jin sautin kukan Amma ta saki Rukkayya ta fara lalaben gurin da Amma take, Amma ta rika fuskarta ta saka hannunta ta bude cikin idonta tana kuka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected