VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

“Ban gane ta canja ba? Jiya na shimfida shi fa, kuma jiya da yau girkina ne, ai ta jira har sai girkinta ya zagayo tukuna ta canja”

“Ni na saka ta canja kuma na karya zaki iya dauke abincinki”

Kamar an watsa mata ruwa sanyi a jiki haka ta ji duk wata kusurwa da logo dake jikinta ya saki, lakkar jikinta ta yi kasa.

“Gaba daya na daina gane maka a yanzu Appan Hurriyya ka canja min”

Ta matsa inda yake tsaye ta risina kasan guiwowiyinta ta hade hannayenta kamar mai rokon gafara.

“Wannan shi ne karo na biyar da zan sake rokonka idan wani laifi na yi maka ka fada min na nemi yafiyarka, ka dubi girman Allah ka yafe min, ka daina hukunta ni da wasu dabi’u da halayya da ban sanka da su ba, kuma baka saba yi min ba”

“Baki min laifin komai ba Iyami, Wallahi ban rike ki da wani abu ba a zuciyata ba”

Ta daga kai ya kalleshi.

“Toh me yasa kake min haka? Akan wani dalili zaka saka Hajiya ta canja zanen gado kuma ta kawo maka abun karyawa bayan ni ce da girki?”

“Saboda zata karbi girki a yau”

Kamar an tsinke wutar cikin jikinta haka ta ji, sai ta mike tsaye tana kallonsa ta kasa sake furta komai.

Hannayensa ya cire aljihu zuba ya nufi kusa da inda ta aje masa tray ya zauna gefen gadonsa sannan yayi mata alama da ta zo ta zauna.
Ta kalli gurin da ya nuna mata amman ta kasa cira kafata ta isa gurin.

“Zo ki zauna Iyami”

Sai a lokacin ta ji kuzari ta cira kafarta ta taka har ta isa gurin ta zauna jiki a sanyeye tana kallonsa. Ajiyar zuciya ya sauke kusan sai uku sannan ya kai hannunsa ya bude bedside drawer ya dauko wata yar karamar jaka ya bude ya dauko wasu takardu ya mika mata.

“Wannan takardun gidana ne da yake a Samaru, na saka lawyer na ya canja komai daga sunana zuwa naki, na kafa shaida da lawyer na kuma ta bangarenki na yi magana da Bappa shi ma ne shaida domin a gabansa aka yi komai, sai dai na bukaci kar ya fada miki saboda ina son ya zama ni zan fara sanar da ke, saboda haka yanzu gidana dake Samaru mallakinki ne halak malak…”

Ta mika hannu biyu ta karba cikin yanayin mamaki da faduwar gaba, ta kasa godiya haka kuma ta kasa jin farinciki ko kishiyarsa. Wata karamar Envelop ya dauko a cikin jakar ya mika mata.

“Wannan Cheque ne na Naira miliyan Ashiri, ina son ki yi amfani da kudin ta hanyar da ya dace ki yi kasuwanci ki rike kanka dan Allah”

Ta karba idonta na cika da hawaye.

“Wannan duk na minene?”

Yayi shiru ya kasa ce mata komai, sai ya sake saka hannunsa ya dauko wani envelop din ya mika mata.

“Ki yi hakuri Iyami, ina jin rashin natsuwa da faduwar gaba da tashin hankali a duk lokacin da girkinki ya zagayo, idan na tuna kina a cikin gidana karkashin kulawata sai na ji kamar zan mutu, na yi ta daurewa ina ganin kamar abun nan zai wuce amman ban ga alamar haka ba, a kullum sai kara yin gaba abun yake, akan hakan na yanke hukuncin yin abun da zai zame mana mafita gudun kar na cutar da ke, domin idan muka daure a haka ban san a gaba yadda zama zai kasance ba”

Kasa mika hannu ta yi ta karba kuma ta kasa ta kasa cewa komai, ta kasa dauke idonta daga barin kallonsa, hawaye kuma suka ce mata ga rabarsu. Ganin haka ya saka ya aje mata takardar a saman takardun da ya mika mata.

“Bana son ki bar min komai duk wani abun da na siya miki tun daga kayan daki har tufafi da duk wani abun more rayuwa, mallakinki ne zan saka a kawo miki har gida, amman dan Allah ki bar min Yayana a hannuna ban yarda ki tafi da ko daya ba, cikin dake jikinki ma idan kin haihu zan dawo da abu na a gidana”

Sai a lokacin ta samu kuzarin bude bakin da yayi mata nauyi ta yi magana.

“Babu uwar da zata so wasu yayan kamar nata, kuma babu yayan da za su jidadin wata uwar kamar ta su, musamman a gida irinka”

“Kin fi kowa sanin yadda nake son ƴaƴana, da uwa ko babu uwa za su jidaɗin zama a gidan mahaifinsu, zan kula da su”

Ta haɗe wani abun da ya tsaya mata ta miƙe tsaye da tunani kala kala, ta bude takardar ta duba me ke ciki saki ne ko akasin haka? Idan sakin ne saki nawa ne? Ko kuma dai ta faɗi a ƙasa ta yi masa kuka ta roƙi ya maida ita bayan ya faɗa mata baya jin natsuwa da kwanciyar hankalin a zamansa da ita yanzu?

“Allah yasa hakan shi ne alheri, kuma ya baka ikon kula da su Hurriya da Hamad”

Ita kanta sautin murya mai kama da tata take jin tana fita a bakinta, domin bata da tabbacin tana da kuzarin furta masa wani abu a yanzu. Tana jan ƙofar ɗakin nasa ta ji ƙafafuwanta sun yi nauyi, mararta ta murɗa wani irin tashin hankalin da bata taɓa samun kanta a ciki ba ya baibayeta. Da gaske Appan Hurriya sakinta yayi? Anya zata iya tafiya ta bar ƴaƴanta? Ko dai wasa yake mata wata ƙila kuma wunin yau gaba ɗaya be faru ba. Tana tafiya jini na mata zuba amman bata sani ba zafin zaton sakin da bata tabbatar ba ya manta da ita zafin mararta dake murɗawa, ya hana hankalinta kusanto jikinta ya juya tunaninta a gurin abun da bata taɓa mafarkin faruwarsa ba.

Arzikinta ɗaya, ko wane part an yi masa corridor da zai sada ɓangaren da ɓangaren Alhaji Haruna ba sai ta gaban gidan ba. Kuma zaka iya fita ko shiga ba tareda sanin kowa ba, har sai idan mutum ya isa part ɗin. Kamar wadda ta sha giya haka ta isa ɓangarenta ta zarce bedroom ɗinta ta zauna a kan gadonta.

“Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un”

Ta furta daker tana kokarin dawowa hayyacinta.

“Haka ake ji? Haka saki yake? Ko dan ina da kurciya ne? Ko kuma saboda ban saka tsammanin zuwan sakin ba ne gaba daya a zaman rayuwata? Ko kuma saboda ina tsoron barin ƴaƴana ne? Allah ka sassauta min, ka saka min natsuwa da kwanciyar hankali, ka hallata aure ka hallata saki, Allah ka yaye min wannan damuwar da zata rufe ni, Ubangiji ka tsaya min”

Rahamar Allah ga bayinsa, da kuma dace ya ƴan amin a kusa, tana gama addu’ar ta ji natsuwa ta sauko mata, numfashin da take jin kamar zai danne mata kirji ya daga mata, mararta ta sake murdawa har sai da ta lumshe ido ta kai hannunta ta taba cikin dake jikinta na wata shida.

Kamar wadda aka yi ma allurar kuzari haka ta tashi ta aje takardun hannunta ta shiga bandaki ta gyara kanta ta fito ta gyara dakin inda ta ɓata ta cire Bedsheet din ta bar gadon a haka, ta dauki ruwa da tsumma ta bi tana goge jinin da bata san ya zuba ba sai a lokacin. Kamar mai shirin yin sata haka ta shiga ɓangaren ta goge jinin sannan ta juyo gabanta na tsananta faɗuwa ta fito daga ɓangaren. Ganin jinin yaƙi tsaya mata ya saka ta sake tsabtace jikinta ta saka pant da pad ta tare sannan ta kwanta saman gadon tana sauraren zuciyarta da ke bugawa da karfi, mararta kuma na cigaba da murdawa.

“Me na yi ma Appan Hurriya?”

Shi ne abun da take ta tambayar kanta, tambayar da bata da amsarta, mulmulawa ta yi saman gadon tana karewa katon dakinta kallo kamin ta tashi zaune ta fashe da kuka mai karfi, a rayuwarta bata taba fuskarta wani abu na tashin hankali irin yau ba. Cikin kuka da bakinciki ta dauko akwatunanta ta fara zuba kayanta ba tare da ta tsaya shiryasu ba, wani abun ma sai dai ta gwamatsa shi cikin wani talkaminta da atamfa ta saka su a kwati daya, sai da ta gama ta rufe ta kaisu gurin kofa ta aje ta dawo cikin dakin ta zauna kasa ta rasa me ya rage mata ta yi, kuma ta kasa fita daga dakin.

Misalin Karfe biyu da mintuna Bus dake dauko yaran makaranta ta shigo gidan, a harabar da aka tanada domin aje motoci direban ya faka motar. Sai da manyan suka fara fita sannan Hurriya ta fito, Hamad kan cikin manyan yayyunsu ya kutsa ya fita, daman shi yana daga cikin sarakunan kiriniya da rashin kunya na gidan, babu kalar dukan da basa masa ko hantara amman kowa yace masa kule zai ce chasss, Amma ta yi fada har ta gaji, Appa ma har baya son a kai masa kararsa domin ko ya masa fada ba zai hana gobe ya sake ba, Hamad irin yaran nan ne da ko kallonsu ka yi a karkace sai sun rama.
Hurriya na shiga part dinsu ta jefar da jakarta a kan kujera ta nufi bedroom din mahaifiyarta, a hankali ta tura kofar dakin ta shiga tsaye ta yi bakin kofar tana kallon kanenta Hamad dake ta fadawa Amma abun da ta yi masa a makaranta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected