Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Okay zan je”
Hurriya ta yi murmushi tana amsa mata da kai sannan ta daga ta nufi dakinta. After ta maida kofar ta rufe ta cire hijab dinta ta zauna bakin gadonta ta dauko Qur’anen ta bude tana karatu, bata daga ba sai da aka kira sallah Isha’i sannan ta aje ta dauki hijab din ta saka ta gabatar da Sallah Isha’i. Tana sallamewa Namra ta turo kofar dakin ta shigo tana murmushi.
“Na je mun gaisa, amman ya tambaya wai ko ni na hana mi dawowa”
Hurriya ta yi murmushi tana karanta addu’o’in sallame sallah. Namra ta zauna bakin gadon Hurriya.
“Yana da ban dariya, he’s nice na yi mamaki yadda ya gane ki”
Hurriya ta shafa addu’ar da take ta mike tsaye tana kallon Namra irin duban nan na tuhuma (Zargi)
“Yaya Namra…. ”
“What? Nonono please daga haduwa da mutum? Don’t please”
Ta tashi da sauri ta fice tana dariya, Namra ma dariyar ta yi ta hau saman gadonta ta kwanta, zuciyarta cike da farinciki alkwarin da Husna ta yi mata domin ta san zata cika. Washe gari da yamma Husna ta dawo mata da martanin cewar ta fadawa Ummarta kuma ta cika kudin and the most beautiful thing is ta tafi ta kaiwa Gwaggo kudin har suna saka mata albarka suna godewa Umma. Hurriya ta rumgume ta da sauri tana murna.
“Na gode sosai Husna”
“Ba komai tarenmu y wuce haka, and Umma ma na ji tana magana akan makarantarki domin ta nuna damuwarta sosai akai gaskiya”
“Ni ma abun yana damuna, ina son na yi ma Yayana magana shi zai iya magana da Appa ko Allah zai saka ya tuna da ni ya saka ni”
“Hurriya da neman magana waya ce miki Appa ya manta da ke?”
Ta yi dariya.
“Haka dai nake gani”
“kin ga bari na tashi ke ma haka kike da kin zo gidanmu baki wani dadewa sai ki fara cewa zaki tafi”
“Laaaa ai to ni kin san yadda gidanmu yake ba ni da freedom ne, amman ke ba a miki tsananin da ake min, dan Allah ki zauna Husna na jidadin zuwanki”
“Ba zan zauna ba, muje ki rakani”
“Idan naje zan sake dadewa”
“Naki wayon zan tafi idan ba zaki rakani ba”
Hurriya ta tashi da sauri ta dauki Hijab dinta ta saka, sannan ta bi bayan kawarta da tuni ta fice daga dakin, a tare suka daga kai suna kallon Ruma dake isar da sakon Hajiya Kaltume ga Hurriya.
“Ni kuma? Me na yi to Hajiya take nema na?”
“Sako aka kawo miki”
Gaban Hurriya ya fadi ita da Husna suka kalli juna kamin su kalli Ruma da tuni ta wuce abunta ta barsu a stairs din tsaye.
“Kin yi da wani za’a kawo miki sako?”
“Aa Wallahi ni wa nake da shi da zai kawo min sako? Kuma idan za a kawo sako da sanina ai ba za a kai bangaren Hajiya ba sai dai nan da nake zaune ko?”
“Haka ne kuma, to sakon miye”
“Ban sani ba”
“Allah yasa ba wani sherin aka kulla miki ba”
“Amin, bari na tafi kar na dade na yi laifi”
Husna ta dafata.
“Na rakaki?”
“Aa dan Allah ki tafi, idan Hajiya ta lura da yawan zuwan da kike zata iya bata alakarmu, ni kuma bana son haka”
“Shi ke nan”
Tare suka sauko Masu aikin Momy suka gaishe da bakuwar Hurriya duk da kasancewar ta yarinya ta amsa cikin Ladabi domin bata hadu da su lokacin da ta shigo falon ba, sai yanzu da zata fita.
A karamin gate suka rabu Husna ta nufi babban gate din fita gidan, Hurriya kuma ta nufi bangaren Hajiya Kaltume gabanta na faduwa domin ta san ita kullum mai laifi ce a gurin Hajiya. Cikin tsoro da fargaba ta shiga falon kana kallon idanuwanta dake cikin gilashi zaka san babu kwanciyar hankali a tare da ita. Nesa da Hajiya Kaltume ta tsaya ta risina
“Hajiya ga ni”
“Sako ne aka aiko miki, wannan dan iskan yaron da mahaifinki ya rabaki da shi wato baki ji ba ko?”
Ta girgiza kai da sauri.
“Wallahi na kyale shi Hajiya, daman ni ban san shi ba sai a bikin Yaya Khairi”
“Amman mai gadin daya karbo sakon ai cewa yayi yace ga sakon da yace zai aiko miki nan”
“Ban yi da shi zai aiko min da sako ba, Wallahi Allah Hajiya”
Khairi ya yamutsa fuska tana jan tsaki.
“Karya kike munafuka, baki hadu da shi a Mall ba, jiya ai sai da kika saka yayi ta min masifa sai da na kai miki waya kuka gaisa, amman yanzu kin wani narke kina rantsuwa kamar gaske, sannu kitse”
“Ni ba wani abu zan ce miki ba, zo ki dauki kayanki kamin Mahaifinki ma ya gani ace na hadaku”
“Ko dai yayi mistake ne, Wallahi ban yi da shi za a kawo min komai ba, Hajiya ki yarda da ni”
Khairi ta taba hannu.
“Yau ina Yaya yake ya zo ya ga abun da salihar nan take aikatawa ana ganin kamar sai mu kadai ne zamu aikata, gashi nan kin aikata fiye da na mu ma”
Hawaye ya fara saukowa Hurriya jikinta ya hau rawa, domin bata san yadda zata wanke kanta ba idan maganar ta kai ga Yayanta ko Appanta da take tsoro yanzu kamar mutuwa.
“Yaya Namra ma tana tsaye a gurin a kira ta a tambayeta”
Hajiya ta tabe baki.
“Ita da Yasir ai ko rai kika kashe ba zasu fada ba, saboda kin iya kirsa da munafurci da kalailayar mai rai kin bi kin lafe a jikinsu uwa macijiya, ni ba wani abun zan fada ba dauki kayanki ki tafi”
“Aa ni ba nawa ba ne”
“Daukar shi ne rufin asirinki Malam domin Wallahi idan baki dauka ba, Yaya na shigowa zan nuna masa su”
Hurriya ta mike tsaye ta iso gurin ta saka hannu ta dauki kwaton kwalin da aka yi ma kwalliya aka rubuta. From Adam to Hurriya in stylish way. Kuka be kamata ba sai da ta fita daga bangaren na Hajiya Kaltume sai ta zauna a balcony ta fara kuka marar sauti saboda ta san daukar ma zai zame mata laifi ne. Ta yi minti talatin a gurin sannan ta tashi ta nufi bangaren Momy, a bude ta samu kofar falon, a lokacin da ta shiga babu kowa a cikin falon, sai ta maida kofar ta rufe, ta nufi stairs tana jin kamar ace Adam din yana kusa da ita ya yakuta masa fuska ta yaga tufafinsa ta watsa masa ruwa da yawu a jiki da fuska, tana tunanin haka ne iya karshen wulakanci. Maida kofar dakinta ta yi ta rufe ta zauna bakin kofar ta fashe da kuka kuka sosai mai sauti, domin gaba daya ta rasa ma ya zata yi, ta kira Yayanta ta fada masa kamin Hajiya ko Khairi su fada masa ko kuma ta samu Appa da kanta ta yi masa bayani, ko kuma dai ta zauna a gurin har sai an nemeta. Sai da ta ci kukanta ta koshi sannan ta ďa ga daga ta tura kwalin karkashin gadonta bata ma tsaya duba meye a cikinta. Ta shiga bathroom ta wanke fuskarsa ta fito ta kwanta saman gadonta, ana daf da kiran sallah Magariba Momy da Khairi suka dawo gidan, ita dai tana dakinta bata leko ba, abun duniya ya isheta, saurare kawai take ta ji an aiko cewar Appa ko Yayanta yana kiranta.
Immediately after gama Sallah Magariba tana zaune saman carpet din da ta yi sallah, Namra ta turo kofar dakin ta shigo cikin yanayin damuwa.
“Hurriya wa kika bari ya shiga dakin Momy da nawa?”
Hurriya ta dago ta dubeta ta cikin gilashinta.
“Babu wanda ya shiga”
“Tuna dai ko wani shiga?”
“Babu wanda ya shiga Yaya Namra me ya faru?”
Kamin Namra ta amsa mata Momy ta shigo dakin a kufule fuska kamar bakin hadari, ta nufi wardrobe dinta ta fara watsa tufafi tana zubarwa a kasa, kamin ta juyo ta yi gurin gadonta ta daga Bedsheet din, sai kuma ta juyo ta kalli Namra.
“Ke sauka ki kira min masu aikin nan”
Namra da rashin jindadin abun da Momy take yi ya bayyana a fuskarta ta ce.
“Momy dan Allah mu bi abun nan a hankali”
“Zaki sauka ki kira su ko sai na bata miki rai?”
Namra ta juya da sauri, domin ta fi kowa sanin yadda Momy take idan ranta ya bace. Hurriya dai na zaune a gurin da ta yi Sallah faduwar gabanta a yanzu ya fi na kallum, duk wani sake sake da take a ranta na dalilin shigowar Momy a dakin da kuma tambayar da Namra take mata be kawo mata cewar zarginta ake da abun da bata taba aikatawa ba ko a mafarki, har sai da masu aikin har uku suka shigo dakin.