Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
Fadeel ya sauke ajiyar zuciya, tabbas idan har duniya ta san halin da mahaifiyarsa take ciki zai ji kunya ba karami ba, daga lokacin da na gane gaskiyar abun da take boye masa har zuwa lokacin da ta bayyana masa gaskiyar komai da komai be sake walwala ba, ba sake kwantawa bachi ya dauke shi ba, be sake kallon wani abu yayi dariya ba gaba daya farinciki ya kaurace masa.
“Zan tafi na bar muku abun kunya Fadeel, dan Allah ka yafe min kuma ka kula da yar’uwarta, ka fahimtar da ita ban kai aikata aka min cikin nan ba sai dan kaddara ta biyo ta nan”
“Karki damu Hajiya, Zainab zata dauko kuma zaki samu sauki ki tashi da yardar Allah, ko ma miya faru mu dai muna son rayuwarki”
“Mutuwata tafi rayuwata Fadeel bana fatan rayuwa idan ma na haihu lafiya, idan kuma ban haihu ba, kun huta karku fadawa kowa abun da uwarku ta yi, Afrah ki yafe min dan Alla..”
“Na yafe miki Hajiya Wallahi ni ban rike da komai ba”
“Allah ya muku albarka… Tashi ka tafi gurin aikinka, ga matarka nan ai ta isa tana kula da ni”
“Toh Hajiya”
Ya mike tsaye ya fice daga dakin. Kusan tun da gaskiyar cikin ta bayyana shi da yar’uwarsa suka ji cewar ba kari ba ne, cikin shege ne Hajiya Fatee ta yi Zainab ta bar gidan ta koma gidan kanen mahaifinsu kuma ta kasa komawa gidan mijinta saboda uwarta ta yi abun kunya, sai kulawar Hajiya Fatee ta dawo karkashin Matar Fadeel wato Afrah wanda ya maida ita gidansa bayan fasa auren Khairy da yayi daman ba shi da burin auren kawai yana biyayya ga cilastawar mahaifiyarsa ne. Matar da take zagi take cewa ta mallake mata ďa matar da saboda ita wannan mummunan kaddara ta same ta yau ita ce take kula da komai nata take mata komai kamar yarta, kusan a gidan ta tare ita da yaranta saboda kula da uwar mijinta.
A ranar da Hajiya Fatee ta yi ma danta da matarsa wasiya kuma ta roki gafararsu a ranar ta yi musu bankwana, a ranar ita da danta ba su kwana duniya ba, cikin dare nakudar data shekara ashirin da wani abu rabon da ta yi kalarta ta taso mata, idan Fadeel yayi yunkurin kiran wani ko kaita asibiti sai ta hana tana fadin ya barta ta mutu cikin gidanta domin ta san cikin nan ba zai barta ba, daga karshe da ya ga wahalar ta yi yawa sai ya dauko mota kamin ya saka ta ciki ta ce ga garinku ita da danta. Rufin asirin da take rokon Allah yayi mata na mutuwa cikin gida ta samu wannan an karba mata, kamin safe fuskar Fadeel da Afrah ta kumbura sosai saboda kuka. Haka Afrah ta rinka rusa kuka kamar uwarta ce ta mutu tana matukar jin tausayin mijinta da ya rasa uwa da kuma tausayin Hajiya Fateen. Sai yafiyar Allah take roka mata, wani kukan ba tashi a gidan ba sai da yarta Zainab ta zo ta fara nadamar tafiyar da ta yi ta bar mahaifiyarta cikin fushin abun da ta aikata musu ashe ma ba mai dade bace a duniya, a yanzu kam sun zama ba su da kowa daman uban ya dade ta rasuwa yanzu kuma uwa ta bi bayansa. Har aka yi amsar gaisuwa aka kare Hajiya Kaltume bata zo gidan ba, sai da aka kara kwana sannan Yasir ya zo gaisuwa gurin Fadeel Maama kuma ta shiga ciki ta yi ma matan. Yasir ya fada masa halin da Hajiya Kaltume take ciki na rashin lafiya da ba zata ita zuwa gaisuwa ba, sai Fadeel ya tausayawa mata duk da kasancewar Yasir din be fito fili wikiwiki ya fada masa hauka take ba. Sai dai hakan be hana shi tausaya masa ba, domin daga ta shi Hajiyar har Hajiya Kaltume bin bokaye da rashin yarda da kaddara be haifar musu da ďan mai ido ba.
*** *** ***
Lokacin da Captain ya kira Appa ya fada masa sun kusa shigowa garin Gusau, sai Appa ya fadawa Amma ita kuma ta kira mutanen gidansu ta fada musu sai duk suka taru a gidan na Appa a bangaren Amma. Shi kan shi Appa sai ya dawo gida da wuri, kamin su iso, Amma ta kasa zama ta kasa tsayuwa sai safe da marwa take ta kagara ta ga ďanta shi din ne ko waninsa. Suna Haka Hajiya Binta ta iso daman tun da Appa ya fada mata take ta mamaki kuma take daukin ganin jikan nata.
Duk yadda Appa ya so ta natsu sai ta kasa saboda abun da yake gabanta ma son ganin Yarta da Ďanta. Daga Hurriya har Mama Rukayya babu wanda ya san da daurin auren Alhaji Haruna da Iyami da aka sake daurawa bayan dawowarta saudi balle tarewar Amma a gidan Appa sai da suka dira a gidan.
Motarsu na tsayawa Amma ta fito da sauri tana sanye da Hijab. Hindu, Gwaggo da Inna Uwani suna bayanta Appa tare da Alhaji Musa da Malam Zakiyyu kanensa da Hajiya Binta duk suna tare da shi, Yasir ma da a lokacin ya iso gidan ya fito motarsa da sauri yana kallon Hamad da Hurriya da suka fito motar. Amma ta durkushe a kasa tana rufe baki tana kuka, tabbas danta ne amman kamaninsa sun sauya yanzu girma ne yake kamashi ya zama ba kamar lokacin da aka dauke shi ba, banbancin wacan ranar da Ruma ta fito mota tana fada mata Hamad ya mutu da wannan shi ne wannan yana a raye ne, amman kukan kusan daya ne, Appa ma hawaye yake kusan kowa kuka yake har shi kan shi Hamad ne.
Amma ta dubi Hurriya dake kallonta garau tana gani babu gilashi ga kuma Hamad sai ta juya baya tana kuka tana godiya a gurin Allah. Hamad ya nufi inda take da gudunsa yana kuka kamar za a cire masa rai irin kukan da ya fi kama da rashi. Ya rumgume Amma yana kiran sunanta jikinsa na rawa muryarsa na rawa Amma ma ta rumgumeta danta tana kuka sosai. Hurriya ma kuka take Hajiya Binta, Rukayya Yasir kusan kowa sai da yayi hawaye a gurin saboda tausayi. Amma ta taba fuskarsa ta taba kunnesa ta lalaba jikinta ta shafa bayansa kamar wanda ta rude.
“Hamad… Hamad… Hamad.. Hamad… Allahu Akbar.. Hamad.. Da gaske ne ashe Hurriya gaskiya ta fada maka mutu ba…”
Hamad ya dago ya rumgume Appa yana kuka.
“Na yi marmarinku Appa na yi kewarku, rayuwar da babu iyaye babu dadi no matter what mutum zai samu a duniyar nan”
“Mun yi bakinciki rashinka Hamad ashe kana raye, Alhamdulillahi”
Appa ya share hawayensa sannan ya kalli yarsa yana murmushi.
“Hurriya an samu lafiya Alhamdulillahi”
Hurriya ta nufi mahaifinta ta rumgumeshi tana kuka.
“Kukan ya isa haka ku shiga ciki mana”
Hajiya Binta ta fada, sai da Hamad ya rumgume kowa a gurin sannan ya daga kansa yana kallon gidan ta ko’ina.
“Ashe zan dawo na yi rayuwa a nan”
Ya fada yana tuna ranar da Amma ta shirya kayanta zata bar gidan, tana boye musu sakin da Appa yayi mata, shi kuma a lokacin ya gama fahimtar komai saboda ya fi Hurriya wayo da fahimtar abubuwa. Yasir kallonsa yake yana jin tausayin mahaifiyarsa ita kawai yake tunawa halin da take ciki yanzu da kuma wanda zata shiga a nan gaba.
A falon Amma suka zauna gaba dayansu, Hurriya na ganin yadda aka kawata falon aka saka furniture da komai ta fahimci Mahaifiyarta ta dawo sai farinciki ya lullube ta daman abun da take da burin gani tuntuni kenan dawowar mahaifiyarta a gidan.
Sai da suka yi sallah suka dan huta sannan suka sake haduwa a bangaren Appa har Momy da yaranta Hamad ya ba su labarin yadda aka daukeshi zuwa lokacin da suka buga masa karfe a kai suka fita da shi daga dakin be sake sanin inda yake ba sai da ya farka ya ganshi a wata kasar tare da wasu mutanen da ba yarensa ba kabilarsa ba.
“A haka na yi ta rayuwa a cikinsu, sun suna min kauna sosai sun dauke ni kamar ďansu ba su tana muna min banbanci ba, saboda mahaifiyar Salim mace ce mai son mutane, musamman ni, tana yawan cewa tana ganina kamar ďanta Salim ne, tun daga lokacin da Captain ya fada min cewar ba ni da kowa a duniyar nan, sai na rike su a matsayin yan’uwa da iyaye amman babu daren da bana kewarku…”