Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
Hannu biyu Hajiya Kaltume ta dora saman kai ta fashe da kuka tana taya aminiyarta alhini.
“Kai wayyo Allah wannan Iyami wannan Iyami Allah ya isar mana gareki, kin aure min miji kin fitine ni yanzu kuma sanadin nan mun fada cikin bala’i, ni Wallahi ma rasa ya zan yi da matar nan da yaranta, kin ga cikinta ya shiga wata na tara kenan wani zata haifowa Alhaji, yayanta da suke gidan ma be hada kowa da su ba, birthday nan da Hurriya ta yi sarkar zinari ta miliyoyan kudi yayi mata kyauta, ni da nake matarsa be taba siya min ba, sarkar da Nafisa take ta kuri da ita yau Alhaji ya siya irinta ya mallakawa Hurriya, ga birthday Hamad tafe waya san iya abun da zai masa shi ma, kuma saboda ita yanzu ya budewa kofa kofar birthday, abun da da ya hana”
Hajiya Fatee ta daki kirji.
“Sarka Hajiya? Lallai Iyami ba zata gama da duniya lafiya ba, ta mallake shi yanzu ta bar gida ta bar muku ya ku yi kishi da ita”
“Hmm abun nan ya ishe ni, ai saboda na san kina cikin taki matsalar ne ya saka ban kawo miki kukana ba, amman ciwon matar nan yana nan a kirjina, a yanzu bana da burin da ya wuce na ga Alhaji ya fita lamarin yaran nan, kuma dukiyar da ya bata ta lalace”
“Ba ke ba, ai ko ni ba zan iya yafewa Iyami ba Hajiya, sanadinta yara kanana sana’in yayana suka daure mu a daji babu kalar wulakancin da ba su min ba, yanzu kuma ga wani abun bakinciki ya sake biyo baya, ban san ya zan yi ba”
Ta karashe zancen tare da fashewa da kuka.
“Toh ni dai ina ganin abun da ya kamata kawai mu saka a nemo mana malamin nan ko Allah zai saka mu dace”
Hajiya Fatee ta mata wani kallo galala.
“Waya zai koma a wannan dajin? Ko gawata ba za a kai ba”
“Aa ina fa? Ni ma ai ba zan yarda ba, ba komawa zamu yi ba nemansa zamu yi idan ya so shi sai ya zo ya same mu”
“Ta ina? Duka wayoyin mu suka karbe fa, ba ni da number ba, kuma da aka yi welcome din Sim din har yanzu be kira ni ba, waya sani ma ko shi ya turo a dauke mu? Mutanen nan kauye nan fa ba su da kyau”
“Kai bana tunani haka, kin ga ni fa na ga kyau aikinsa domin shi kadai ne yayi min aiki kuma aikin yayi yadda nake so har Iyami ta bar gidan nan, shekara nawa ina kashe kudi a banza ban dace ba sai a gunsa, sa zaki yi a nema mana shi waya nuna miki gurin Malamin”
“Wata kawata ce Salame”
“Toh ita zaki saka ta je ta dauko mana shi, sai mu saka gurin haduwa da shi ba dole sai ya san gidan mu ba, mu gabatar masa da bukatanmu mu basa kudin aiki, daga nan ma sai na tambaye shi ina aka kwana zancen aikin Iyami, ke kuma sai ki saka yayi miki na wannan mugun abun da yake cikinki”
Kallon rashin fahimta Hajiya Fatee ta yi mata
“Ya danne miki shi mana, ba zai taba tashi ba har ki mutu, ko baki san ana haka ba? Na Iyami ma so nake a danne shi kar ta haifa ma Alhaji mugun abu, dan na san duk wayonta be wuce Alhaji ya mutu ta ci gado ba”
Hajiya Fatee ta kalleta wata rahma na saukar mata a ruhi, jin kamar ta samu mafitar masifar da take ciki.
“Kuma kina ganin hakan zai yi?”
“Me zai hana? Ki dai ki zuba masa kudi kawai, ni ma kudin zan zuba masa, kuma a hannun Alhaji zan karbe su, kudin sarkar zinarin da ya siyawa Hurriya da kudin da ya bawa Iyami duk sai na fanshesu a hannunsa, yanzu ne za su gane sun yi kuskuren taba mace kamar ni, kuma Wallahi sai na malleke Alhaji ko ta halin yaya, sai ya dawo a tafi hannuna Iyami da ƴaƴanta sai sun ɗanɗana kuɗarsu, Iyami sai ta gane kuskuren da ta aikata na aurar min miji, sai ta yi nadamar hada shimfida da Alhaji, matsayin da ta taka a baya na tana Matar Alhaji ina Matar Alhaji sai na saka ta yi nadamar haka… Ba ita ba har Nafisa sai na sake mata sabon karatu na goge mata hadda. Dukansu sai sun dawo a tafin hannuna”
Ya daki tafin hannunta tana kashe ido alamar yanzu ta shiryawa rashin imani, da kuma fada da Iyami da Momy.
________________
Hmmmmmm Allah yasa kuna hango abubuwan da nake hangowa
Tafiyar fa duk duka yanzu aka fara…. Ku daura ɗamara ku zage damtse domin domin alkalinmin da zafinsa ya zo
Kar a manta idan an karanta ayi sharing
☆❁ ❁☆
ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy
https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy
1️⃣4️⃣
Namra ta dago ta dubi kofar shigowa falon tana amsa sallama, sai ta mike tsaye da sauri tana kallon Captain da mamaki, zuwansa a yanzu ya bata mamaki tsabanin baya da bata mamakin zuwansa domin ya saba zuwa gidan a duk lokacin aiki ya kawo shi ko ziya, tana mamakin zuwansa ne kasa da wata uku da faruwar abun da ya fusata shi, wato fasa masa tayun mota da Hamad yayi suke zaton Hajiya Kaltume ce ta saka aka aikata haka. Ba kasafai yake sake zuwa gurin da aka bata masa rai ba, idan ma zai sake komawa a gurin sai ya dauki lokaci mai tsawo har an manta da shi yake sake zuwa, wannan ya saka duk wani makusancinsa da yake son alaka da shi ta daure ko da iyayensa yake kokarin kiyaye duk wani abu da zai batawa dan gatan Ammy kuma ďa daya tilo ga Alhaji Aliyu Turaki. Wata kila haduwar jinin da Allah ya saka tsakanin Momy da ďan Yayanta ya wuce yayi mata haka. Fuska ba yabo ba fallasa ya shigo falon hannayensa duka biyu suna bayansa.
“Sannu da zuwa Ya… Captain”
Tunawa da ta yi baya son ace masa Yaya ya saka ta kasa karasa sai ta kiranshi da sunan da kowa yake kiransa.
“Yauwa hutawa kike?”
“Eh bari na kira Momy tana ciki”
Tana juyawa ya dakatar da ita.
“No Wait… Ina yarinyar nan take Namra?”
Ta juyo tana wara alamar bata fahimce wadda yake tambaya ba.
“Wata fara haka mai dan tsayi marar jiki, mai saka glasses”
“Oh Hurriya, tana bangaren Hajiya a kirata”
Ya daga mata kai, sai ta aje remote din hannunta ta nufi kofar fitar ta fice da sauri, da mamaki da tunanin dalilin kiran Hurriya ta isa bangaren Hajiya Kaltume, sai ta ci karo da Hurriya tana rike da tiyo tana watsawa motar Yasir ruwa, Hamad kuma na ta kada kumfa.
“Hurriya”
“Uhmm”
Ta juyo ta kalleta.
“Wai ki zo ana kiranki Captain…”
“Waye Captain…?”
“Ina wani wadda na ganku tsaye a bakin kofar Momy har na dauko miki glashinki da ya fashe? Kin tuna”
Hurriya ta yi shiru ta dan bata fuska, kuma ta kasa amsawa Namra da ta tuna ko ba ta tuna ba.
“Wanda ya mareki?”
Hamad ya tambaya, Hurriya ta daga masa kai Namra ta zaro ido domin bata saka ran marinta yayi ba, ta san dai akwai abun da yake faruwa.
“Au daman marinki yayi? Ikon Allah me kika masa?”
“Wucewa na zo yi ban gani ba muka yi karo shi ne ya mare ni har gilashina ya fashe”
“Ni kuma na fasa masa tayun mota duk biyu da wuka”
Namra ta rufe baki with mamaki. Hurriya ma masa kallon rashin jindadi fadar da yayi a yanzu.
“Daman kai ka fasa tayun nan? An kusan yaki a gidan nan fa saboda an fasa tayun Captain, Allah ya tsare ka Momy bata sani ba, da sai ka zama abun tausayi”
“Ni ina ruwana”
Ya fada yana turo baki.
“Captain akwai zafin zuciya ko shi zai iya maka hukunci babu ruwansa da alakarka a gidan nan, to yanzu dai shi ya ce a kiraki”
Hurriya ta ake tiyon kasa ta nufi fanfon ta kashe sannan ta bi bayan Namra, Hamad kuma ya cire hannayensa daga cikin kumfan da yake kadawa ya bi bayan Hurriya. Ita dai bata san ta masa laifi a yanzu ba balle ta yi zaton mari ne ko cin mutumci, sai idan kuma cewa za’ayi ta haifar masa da ciwon kirji saboda kanta ya bugi kirjinsa. Namra ce ta fara shiga sannan Hurriya sai kuma Hamad dake bayanta. Yana tsaye a gurin da Namra ta barshi sai dai wannan karon gefen kujerar da Namra ta tashi yake kallo ma’ana kofar falon ta koma gefensa na dama sabanin dazun da ya bata baya.