VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

“A gwada Malam zan biya ko nawa ne karka ji haufi”

Malam ya san washe baki. “To Mallada ai mu haka muke so”

Hajiya Fatee ta ce.

“Toh ni Malam ya za’ayi na gane idan cikin ya dannu?”

“Idan na yi aiki, zaki ji motsi sosai a cikinki idan motsin be daina ba har safe, to cikin ne dannu ba wata kila sai mun sake yi, idan kuma kin ji motsin kadan to aiki yayi kuma zaki daina duk wasu dabi’u da kike na masu ciki, cikin kwana biyu”

“Alhamdulillah, ni da zaka cire cikin ma ni ka dauki cikin na bar maka, ko ina da aure me zan yi da mugun iri? Balle kuma an kwana biyu har na kai ga jikoki”

“Komai zai wuce Hajiya karki samu damuwa”

A ranar da farinciki Hajiya Kaltume ta dawo gida, saboda ta samu fadawa bokanta abun da take so kuma ya tabbatar mata da zai iya. Wani karin abun farincikin ma sai da babbar yarta Mace mai bin Yasir wato Umm Kaltoon da ake ma inkiya da Maamata saboda sunan Hajiya Kaltume mata albishir da mai cewar mai son ta zai zo ya gaishe da Hajiya da Appanta sai Hajiya ta rasa ina zata saka kanta dan dadi, daga ita har Hajiya Fatee sun kwana da farinciki a daren kowa da bukatarsa da kuma burinsa, Hajiya Fatee bata da burin da ya wuce a danne cikin nan kuma a raba Fadeel da matarsa Afrah saboda ta tsokane mata ido.

 

Washe gari…

A tare da Hamad Hurriya ta fito bangaren Momy da far’arta tana hira da Hamad, kai ka rantse ba sa fada da juna labari take ba shi na wata class mate dinta da ya sani sai dariya yake. Sai da suka fara zuwa gurin Appa suka karbi na na su lemun da Chocolate Hurriya ta masa godiya, sannan suka nufi box din dake kai su makaranta suka shiga. A makarantar ma sai suka wuni kamar ba su ba, daman tare suke breakfast amman kowa da abincinsa dabam, a ranar duk abun da Hamad ya siya sai ya iskota har cikin ajinsu ya bata, kasancewar ajin maza dabam na mata dabam. Misalin karfe daya da rabi suka tashi suka tafi Masallaci suka yi sallah sannan suka tsaya jiran direbansu dake zuwa karfe biyu daukarsu gaba dayansu yan gidan. Biyu da mintuna ya iso suka shiga box Hurriya tana can baya Hamad kuma yana a inda ya saba zama, wato front seat babu mai zama a gurin sai shi kuma baya zama da kowa sai shi kadai. Kilometers kadan ne tsakaninsu da Family house dinsu wata bakar motar ta shiga gabansu ta tara musu har sai da direbansu ya tsaya gashi gurin babu mota ni motoci ma ba kasafai fa, shi ma direban yana biyo hanyar ne saboda ta fi saurin kawo su gida.

“Malam baka gani ne?”

Ya fada cikin tsawa ganin yadda yake masa ganganci kamar ba akan titi suke ba. Bude motar aka yi wasu maza hudu suka fito fuskarsu a rufe biyu daga cikinsu na rike da bindiga suka bude ma direban da tuni ya fara salati ya fito Hamad ma ya bude ya fito jikinsa na rawa suka sa ya zagayo gurin direban sannan suka bude gambun bus din.

“Kowa ya fito”

Kowa ya fito cikinsu na rawa suna ihu.

“Ku yi shiru ko na halbe mutum yanzu”

Dayan ya fada sannan biyun da ba sa rike da makami suka iso gurin dayan ya rika Hurriya dayan kuma ya rika Ruma suka fara jansu zuwa motar. Hamad ya fashe da kuka sosai yayi saurin riko Hijabin Hurriya da ita ma kukan take, kamin ta kai bakinta ta gantsawa wanda ya rike mugun cizo a hannu, aiko ba shiri ya sake ta sai ta ranta ana kare, abun ka da marar jiki kamin dayan ya rikota ta yi nisa, sai yayi wuf ya cafke Hamad dake kokarin guduwa, suka dauke shi tare da Ruma sai motarsu. Suka shiga da sauri suka fisgi motar sannan Salma da Khairi suka fara ihu tare da Namra suna kuka, Hurriya kam tun da ta sa gaba bata dawo ba sai da direban ya wasu mutane da suka tsaya bayan bata garin sun gudu suka bi sawunta, sai suka same ta tsakanin wani gida da kwararo ta duke a gurin ta runtse idon ta saka hannayensa ta danne kunnuwanta.

“Hurriya”

Ta razana ta bude ido jikinta da zuciyarta na rawa, gilashinta ya fadi gurin gudun da dake, shiga kwararon ma da ganinta dishe-dishe ta shiga lalabe ya taimka mata, shi ne silar tsayarwa a gurin ma, domin da tana ganin hanya da kyau ba zata kusa ba guduwa zata yi. Jin muryar direbansu ne ya saka ta fashe da kuka, tana lalabensa shi ya rikota yana matsar kwalla suka fito gurin. Kin yarda ta yi su koma gurin saboda tsoro sai da direban ya janyo motar ya kawo gurin sannan ta yarda zata shiga.

“Ina Hamad?”

Ta tambaya yana taimaka mata ta hau bus din har lokacin kowa kuka yake, ita kuwa bata ji kukan dan’uwanta ba kuma bata ji muryarsa ba.

“Sun tafi da shi”

A take ta saki hannun direban ta yi shiruuuuu kamin ta fara haki.

“Wayyo Allah na Hamad”

Ta dora hannu akai ta fadi a gurin ta fashe da kuka mai karfi.

 

 

 

______________________

Masu karatu shin suwaye wadannan mutanen da suka dauki Hamad?
Me suke so? Za su dawo da shi ko kuma yaya?
Anya Hajiya Kaltume da Hajiya Fatee za su nasara akan kudurinsu?
Wai ni kam me Afrah ta yi ma Hajiya Fatee ne ta tsane ta har take neman raba aurenta da danta? Anya ana samun uwar mijin dake neman raba auren danta ta hanyar asiri?
Anya asirin da Hajiya Kaltume ta saka aka yi ma Iyami akan karta sake aure zai yi kuwa? Amma zata dawo gidan mijinta Appa ko kuma wani auren zata yi ko kuma dai ba zata auru ba kamar yadda Hajiya Kaltume take fata?
Waye wannan Captain din?
Waye Wannan Fadeel din?
Anya Momy zata daina halinta na kyamar Iyami da yayanta kuwa?
Akwai tsabtataciyar Soyayya a cikin littafin mai taba zuciya ta zauna a ruhi, ku dai kun san ba mu fara komai ba. Kuma da yardar Allah ba zan ba ku kunya ba.

Duk amsoshin wannan tambayar tana nan ƙumshe a cikin littafi na biyu da zamu fara ranar Litanin mai zuwa In Sha Allah. Sai dai shi Book two din ba free ba ne na kudi akan 500 only.

If you want subscribe biya 500 to

2451879008
Zenith Bank
Hadiza Abubakar

Sai ku turo shaidar biyan ta wannan number 08036126660

Ƴan Nijar kuma za su turo katin Zain ko Orange na 500 ta wannan number 08036126660.

Za ku iya bibiyar Litfafin nan a Arewabooks ga wadanda basa ra’ayin karantawa a Whatsapp. A username dina @khadeejacandy ko kuma ku yi searching book din Hurriya.

Sai mun hada ku a Paid Group Real Masoya masu Patronizing dina a ko da yaushe.
Ku huta lafiya, Allah ya bawa masu niyar siya kudin biya.
https://www.arewabooks.com/chapter?id=653656a358cd413f0dc70b74

Kamin direban ya isa gida duk wanda ke cikin motar ya dauka Hurriya shudewa zata yi, saboda kukan da take yana yin sama da nufashinta kamar nunfashin zai fice daga jikinta gaba daya. Namra ce take rike da ita tana kuka tana bata hakuri.

“Yi Hakuri Hurriya In Sha Allah zai dawo lafiya Allah zai tsare su”

Hurriya bata iya furta komai, gashin idon nata ya rufe gaba daya saboda kukan hawayen ya hanata ganin dishe-dishe ma da take gani idan babu gilashi a idonta. Direban na fakawa Salma da Khairi suka fita suna kuka suka nufi bangaren Hajiya Kaltume suna kuka, Namra kuma ta tsaya ta riko Hurriya suka fito.

“Bana ganin komai Yaya Namra idon ya rufe gaba daya… Karki bar ni nan dan Allah tsoro nake ji… Kira min Yaya Yasir ko ki kaini gurin Amma ko ki kira min Appa na dan Allah”

Tana maganar muryarta na rawa saboda numfashim da ya sarke ta. Ta san a gurin dayan su ne kadai zata yi kukanta ta more kuma ta fada musu abun da ya faruwa. Kowane ďa ko ƴa idan abun farinciki ko kishiyarsa ya same shi guduwa yake gurin uwarsa, sai dai ita a yau bata da wannan gatan, ba dan mahaifiyarta bata raye ba sai dan bata tare da ubanta, bata taba sanin zafin rashin Amma a gidan ba sai yau, ko wane ďa yana bukatar uwa a kusa da shi balle kuma ita da take da lalaurar ido. Dukawa ta yi a gurin ta dora duka hannayenta biyu a kai ta kwalla ihu da kukam muryarta tana kuka har sai da duk wanda ke harabar gidan hankalinsa ya dawo kanta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected