Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Dole sai na yi haka? Kuma dole kai zaka yi?”
“Aikin Soja ba kamar sauran aiki bane Ammy, dole na bi dokoki da ka’idodin manya kamar yadda na kasa da ni ma za su bi ni, zan iya tafi na yi yanzu?”
Permission kawai ya roka daga gurin Ammy sai ta kara masa da tukuici.
“I will escort you”
Duk yadda ya so ta zauna yaje yayi abun da ya kamata da akansa be samu haka ba, sai da Ammy ta raka danta da kanta har gurin da ya kamata shi kadai ya shiga sai da ya karya dokar ya shiga tare da ita. After ya dawo abokan aikinsa suka yi ta shigowa suna masa ya jiki, ciki har da manyansu and da yawansu sun san Engr AA Turaki wato mahaifinsa ba dan yana aikin sojan ba sai dan connection da kuma kudi mai sa asan mutum dan dole. Wasu kuma suka shigowa ne saboda Captain jindadin aikin da suke da shi da kuma kokarinsa. Momy bata bari sun fita a office din ba sai da Captain ya wanke bakinsa ya yi breakfast sannan suka fito wasu sojojin na take masa baya har gurin da aka faka manyan motocin gidansu, Daya ta Momy, daya wanda Ammy da Engr suka shigo sai kuma dayar da bodyguards din mahaifinsa suke ciki, dayar kuma ta Momy Ikilima ce. Captain ya kalli Mahaifiyarsa ba tare da fargabar komai ya ce.
“Kamin mu wuce Ammy ina son muje mu duba Hurriya asibiti….”
Ammy zata yi magana Engr yayi saurin girgiza mata kai alamar kar ta hana, sai kuma ya tari numfashin mahaifiyarsa ya amsa masa.
“Okay zamu fara zuwa mu dubata tukuna sai mu tafi gida ko Family House?”
“Family House”
“Okay My Son”
Direban ya bude masa mota ya shiga baya, tare da iyayensa Ammy da Engr, wani Knight ya shiga Front seat, Hajiya Nafisa wato Momy da Momy Ikilima ma a dole suka bi Captain da iyayensa dake kokarin cika masa kudirinsa. A harabar Federal Medical Center wato FMC suka faka, security dake gaban motar Engr ya bude motar da sauri Captain ya fito tare da iyayensa, Bodyguards na take musu baya. Ko kadan Momy bata so zuwa duba Hurriya a asibiti ba, ba dan Captain ya so haka ba kuma iyayensa suka biye masa ba zata taba zuwa dubata ba, domin ta fi jin tsanar Hurriya a yanzu fiye da koyaushe, sanadinta suka fara samun da Captain gashi kuma yanzu ta ja musu abun kunya, sai dai babu yadda ta iya saboda ďan ďan’uwanta ya so haka. A dokar asibitin lokacin da suka zo ba lokacin ganin marar lafiya ba ne, amman ba a hana su shiga ba domin ko na goye ya san kura.
“Ina ne?”
Captain ya tambayi Momy ba dan ita ma ta sani ba, sai da ta sauke ajiyar zuciya ta kalli yayanta sannan ta daga wayarta ta kira Namra.
“Gamu mun shigo asibitin, wane daki ne?”
Ta fada musu har da number dakin, a nan suka juya zuwa wani ward din da ba wannan ba, ko’ina suka wulga sai ya kallesu kana ganinsu ka san ba kananan mutane ba ne. A lokacin da suka isa dakin da Hurriya take sai Captain ya kalli iyayensa ya ce.
“Wata kila ba zata so ta gan mu tare da ku ba, zan fi jindadi idan na shiga ni kadai, na san idan na ce ku zauna a mota na shigo ni kadai ba za su yarda ba shiyasa ban yi magana ba”
A nan kam Momy kasa hadeye maganar ta yi cikin bacin rai ta ce.
“Mu iyayenka mu zamu jiraka har sai ka shiga duba wata banzar yarinya tukuna mu tafi? Sai kace kai ka haife mu?”
“Idan hakan zai faranta ransa me ye a ciki? Shiga ka yi abun da zaka yi son zamu jiraka a mota”
Daddy ya fada sannan ya kalli bodyguard dinsa daya.
“Ka tsaya a nan idan ya fito ku same mu a mota”
“Okay Sir”
Daddy ya juya tare da Ammy domin komawa gurin motarsu, Momy ma dole ta bi bayansu iyayen yaro sun goyi bayansa ita a su ta ki bi, a nan ta samu damar karanta musu kabli da ba’adi na Hurriya, tana ta kusheta. Sai da suka wuce sannan Captain ya murda kofar dakin ya tura ya shiga, tana zaune saman gadon ta lankwashe kafafuwanta tana fuskarta hadu da kofar dakin.
“Kai kuma kai ne wa?”
Gwaggo ta tambaya tana kallonsa. Sai a lokacin ya tuna be yi sallama ba. Dan haka ya jadada sallamarsa sannan ya karasa cikin dakin yana gabatar da kansa.
“Sunana Jamal amman an fi sanina da Captain ni dan Momy dan yayanta…”
“Toh ko me ya sa ka zo?”
Ya kalli Hurriya da babu gilashi a idonta hawaye na zubo mata ya ce.
“Na zo na duba Hurriya ne? Namra ta fada mana tana nan”
“Namra ta tafi gida tun dazu, kuma dan Allah ba ma bukatar kowa, daga dangin Nafisa har na Kaltume, wannan kiyayyar ta yi yawa, ba bar uwa ba a bar ya ba, babu kalar azabar da ba a nunawa yarinyar nan ba yanzu abun ya wuce nan har sai a hada da kazafi? Kazafin ma na zina? Ita da gidan ubanta amman bata da walwala? Bata da jindadi? Akan me? Yanzu gashi nan kun yi sanadi idanuwan nata sun rufe gaba daya, bata iya gani ko da gilashin, buri ya cika tun safe da ta farka bata cewa komai ba, an kashe yarinya tana ji tana gani”
Gwaggo ta karashe fadan da kuka, Captain ya sauke idonsa kasa hawaye suka zubo masa.
“Ina kyautata zaton ni ne mutum na farko da ban yarda Hurriya ta aikata wannan abun ba, ban zo nan domin cin mutumcinta ba, ita ma ta sani kawai dai na kasa natsuwa ne har sai na zo na dubata, ban san matsayinki a gurinta ba, amman dan Allah ina rokon Alfarmar ki bar ni na ga Hurriya”
“Gata nan ka ganta, amman ba zan je ko’ina ba, kai ma ba zaka dauki hotonta ka yadawa duniya ka bata mata suna ba, kuma ko waye da hannu a lamarin kada Allah ya bar shi da salama, daga yaron har kowa”
“Ameen”
Ta saka yatsansa ya cire hawayen sannan ya karasa gaban gadon Hurriya saitin inda take zaune ya tsaya yana kallon fuskarta. Hawaye take malalarwar irin malalar da gulbi yake idan ya kawo, babu yankewa kuma babu fasa zuba, yanayin yadda take kallon saitin da yake tsaye ya isa ya kara tabbatar masa da bata iya tantance fari da ja a yanzu, sai bakin da ya rufe ganin idanuwanta.
“Hurriya…”
Bata amsa ba, motsa ba bata bar masa wata alama da zai gane tana jin muryarsa, ibadarta kawai take ta kuka. Cikin kuka Gwaggo ta ce
“Bata cewa komai, kuma bata gani”
Captain ya hadeye yawu mai matukar ďaci fa maƙaƙi a maƙoshi.
“Likita ne ya ce bata gani ko kuma ke kika ga alamar bata ganin?”
“Na ga alama, sa safe da ta tashi zata shiga bandaki ga gilashi a idonta amman lalabe take, na fada Likitan da ya shigo suka duba idon suka ce ua samu matsala, shiyasa suka canja mana daki ai, yanzu ba maganar sumanta ake ba, maganar idonta ake Likita biyu ya duba idon zamanmu a nan sun ce sai an yi aiki wai jijiyar dake hada idonta da kwakwalwarta ta samu matsala”
Captain ya daga kansa sama kamar zai fashe da kuka.
“Ya Rahma….”
Ya ambacin mafi rahamar masu tausayi, sannan ya sauke kai ya kalleta pointing finger dinsa ya kai saitin idonta kamar zai tsokale ido amman bata matsa ba, a nan ya tabbatar da bata gani da gaske.
“Jiya kin zo min a suma, kin fada min baki aikata ba, kuma na yarda da ke. Yau kuma ina tsaye a gabanki ne domin na fada miki wani abu, kowaye ya aikata miki wannan abun Hurriya, ba zai sake samun farinciki ba a rayuwarsa, sai ya kunyata fiye da yadda ya so ya kunyata ki, sai na sa duniya ta tsine masa irin tsinuwar da zai ce ina ma be aikata ba”
Ya kama hannunta ya rike a gaban Gwaggo.
“Na miki wannan alkawarin Hurriya, kamar yadda na yi miki alkawarin dawo miki da dan’uwanki, shi ma wannan ki rubuta ki aje nauyin yana kai na….”