Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
A gidan suka wuni har dare, abincin da Hamad ya kasa ci a gidan Ubansa sai gashi ya ci a gidan kakarsa kasancewar Amma ce ta dafa masa da kanta, kuma ta saka shi gaba ya zauna ta cinye abincin tass ya dora da lemu, tukuna hira ta biyo baya, sai da dare yayi misalin tara da rabi sannan Yasir ya zo daukarsu daman ya fada musu a lokacin da direba zai kawo su cewar shi zai dauko su. Nasiha sosai Amma ta yi musu sannan ta aika Hamad ya shigo da Yasir ya zauna saman kujerar karamin falon suka gaisa.
“Yasir ga kanenka nan, na san kana kokari amman Dan Allah a kara, a rika ja musu kunne idan suka yi ba daidai ba, kuma a rika duba su dan Allah”
“Amma dan Allah ki daina wannan maganar, ko minene Allah ya kawar da shi ya kawo maslaha ki dawo gidan kamar yadda aka saba”
“Toh Ameen, duk da haka dai a kula da su musamman Hamad”
“In Shaa Allah”
“Allah ya taimaka ko a kawo maka abinci”
“Aa idan na koma gida zan ci, yau Rukayya bata gidan”
“Tana ciki karatu take yi kasan idan suka samu littafan nan na hausa basa son tashi, yanzu haka bata ma san ka shigo, bari a kirata ku gaisa”
“No kyaleta Amma, a gaisheta dai, bamu mu tafi kar dare ya kara yi”
Yana rufe baki wayarsa ta bude nata ta fara kuka, hannu ya saka aljihu ya ciro wayar ya duba ganin mai kira ya saka ya amsa da sauri.
“Hello Appa”
“Yasir Hurriya bata dawo ba?”
“Gasu na zo dauko su”
“Sai yanzu? Kasan bana son ana kaiwa dare a waje ko? Me yasa direba be je dauko su tun wuri ba?”
“Affuwan Appa, laifina ne ni nace zan dauko su kuma yanzu haka ina gidan”
“To ku dawo yanzu nan, karka sake yaran nan su ce zasu kwana a nan”
“In Shaa Allah, yanzu zamu taso”
“Sai kun iso…..ka gaishe da Mamansu”
Ya fada daga karshe bayan yaja dogon numfashi, da mamaki Yasir ya amsa masa da toh sannan ya sauke wayar.
“Appa ne, ya ce na gaishe ki”
Wani irin faduwa gaban Amma yayi, mutumen da ya sake ta ya kwaso kayanta ya yace a kawo mata kuma shi zai ce a gaisheta.
“Ina amsawa”
Mikewa yayi tsaye yayi mata sallama Hamad da Hurriya suka bi bayansa, Amma kasa raka su ta yi har suka fice daga gidan. Daga gidan Gwaggo Yasir be tsaya ko’ina ba sai gidansu ya faka a bangaren Hajiya Kaltume, Hamad ya riga fitowa motar sannan Hurriya, Yasir kuma ya tsaya gyara parking din.
“Me yasa baki fadawa Amma na fasa miki gilashi ba?”
A jere suke suna tafiya Hamad ya tambayeta domin abun da ya tsaya masa a rai kenan tun a lokacin da ta boyewa Amma cewar sun yi fada.
“Idan ta ji zata ji ba dadi ba, baka ji tana cewa mu zauna lafiya ba? Idan kana yin fada ran Amma zai bace”
“Ni dai bana son Hajiya bana son Momy bana son kowa a gidan nan”
Yana fada yana wani cin magani kamar wani babban saurayi, Hurriya ta tsaya kallonsa da mamakin furunci, shi kam tuni ya juya ya fasa shiga bangaren Hajiya Kaltume ma ya nufi na su bangaren duk kuwa da ya san Amma bata gidan. Hurriya ta cigaba da tafiya har ta isa bakin kofar falom ta muda kofar ta shiga da sallama farin gilashin dake kara mata kyau yana fuskarta.
“Wa’alaikassalam”
Fadeel ya amsa mata yana zaune daga gefen kujera yana gwada kiran Hajiya Fatee.
“Ni yanzu hankalina ya tashi sosai, ace har karfe goma Hajiya bata dawo ba? Ga wayarta baya shiga, daman tun da Ruma ta dawo makaranta take ta damu na da ina Hajiya”
Cewar Maama tana gwada kiran Hajiya Kaltume.
“Amman fa ce mana ta yi gurin Hajiya Fatee zata je”
Fadeel ya ce
“Bata gidan, domin daga can na fito masu aikin suka ce min tare suka fita da Hajiya, shiyasa na zo nan ko tana nan domin wayarta har yanzu bata shiga”
Yasir ne ya shigo falon yana motsa keys din dake hannunsa.
“Hurriya ke da Hamad Appa yace na kira ku, Ina Hajiya?”
Ya karashe zancen yana kallon Maama da hankalinta ya tashi sosai kamin ya karasa ya mikawa Fadeel hannu su gaisa.
“Ita muke ta nema?”
“Ban gane ita kuke nema ba?”
Tambayar Fadeel dake fadar haka yake da mamaki.
“Dazu na shiga na gaishe da Hajiya aka ce sun fita tare da Hajiyarka, yanzu kuma na dawo masu aikin suka ce min bata nan, na gwada kiran wayarta kuma ba a samu shiyasa na zo nan ko zan sameta sai kuma na tarar nan din ma kanenka neman Hajiyarka suke”
“Wai tun fitar da ta yi da safe bata dawo ba? I thought ta dawo ba fa, yanzu ma Appa ne ya ce a kirata”
Maama da tuni ido ya raina fata ta fara kuka ta ce.
“Wallahi bata dawo ba har yanzu, ni hankalina ya tashi”
“Subhanallahi, to ina ta ce zata je?”
Maama da Salma suka amsa masa, duk abun da ake Hurriya da ido kawai take binsu, Fadeel kuma yana jefa mata kallo time to time, farar fatarsa sai daukar masa hankali take kasancewarsa baki, ba shi kadai ba har Yasir da duka yan matan Hajiya Kaltume babu fari ko daya, sai wanda ya dara wani baki, domin an yi gadon bakar fata ta uwa ta uba, kamar yadda shi ma yake baki sai dai nasa bakin mai kyau ne irin mai shaike da ya dace da fatarsa ya karawa hancinsa fa fararen hakoransa da idanuwa kyau. Hurriya ta mike tsaye ta nufi kofa domin amsa kiran mahaifinta Fadeel ya bita da ido yana kallonta kasa kasa har ta fice, ba wannan ne karon farko da ya fara ganinta ba, amman a yau ta tafi da shi, domin ta kure iyakar ganinsa ta cika idonsa.
*** *** ***
Wasa-wasa aka nemi Hajiya Kaltume aka rasa babu amo babu labari, duk inda ake saka ran za’a gane an bincika bata nan, haka ma Aminiyarta Hajiya Fatee ita ta bangaren danta Fadeel babu inda be bincika ba amman be same ta ba, gashi be san direban da ya daukesu ba balle ya neme su, wayoyinsu kuma idan an kira ba mai shiga, shi kansa Appa sai hankalinsa ya tashi balle kuma yayanta da bachi ma ya gagaresu, Hurriya ma da ba yarta ba sai da nata hankalin ya tashi domin bata son ta ji wani abu marar kyau ya same mutum.
Tun ana maganar kwana daya, biyu har aka yi sati, sai da Hajiya Kaltume da Kawarta Hajiya Fatee suka yi kwana goma cif sannan aka kira wayar Appa ana neman ya fada miliyan dari, domin sun tambayi Hajiya kuma ta fada musu waye mijinta, ta bangaren Hajiya Fatee ma haka suka nema gurin ďanta. A lokacin Appa ya zo musu da labarin yana mamaki su ma mamakin suka yi, ba su mamakin jin cewar tana hannun kidnappers ba daman sun saka tsammanin haka domin sun bincika ko’ina ba a same ta ba, kuma su kai report gurin police an saka addu’a amman duk shiru, kudin da suka bukata ne abun mamaki.
“Miliyan dari kuma? To a ina suka samu number ka Appa?”
Yasir ya tambaya cike da mamaki da kuma tashin hankali a lokaci daya.
“A gurinta suka samu, na yi magana da ita na ji murayarta?”
“How taya suka kama su? Wannan abun sai idan da na gida aka hada kai”
“Ban sani ba, amman dai mai maganar yace sun kama su a wani kauye dake kusa da gidan zalla nan kwatarkwashi”
“Ikon Allah, amman dai tana lafiya ko Appa”
Ruma ta tambaya tana kuka.
“Ba mu sani ba dai, ba mu gama magana ba suka yanke wayar kuma na kira bata shiga”
“Kamata yayi a sanar da police tun wuri”
“Zan kira yanzu na sanar musu”
Appa ya juya ya fice, cikin wani karin tashin hankali sa be gama warkewar daga na Amma ba an kara masa wani.
HURRIYA POV.
Hurriya na zaune falon Momy plate din shimkafa a gabanta tana cin abincinta na dare, Namra zaune saman kujera tana duba dogayen rigunan dake zube gefenta kan kujera. Momy ta shigo daga bangaren Appa. Namra ta mike tsaye da sauri tana nuna mata rigar da ta zaba.